Tinubu Ya Manta da Bambancin Siyasa, Ya Yabi Gwamnan Jam'iyyar Adawa

Tinubu Ya Manta da Bambancin Siyasa, Ya Yabi Gwamnan Jam'iyyar Adawa

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya isa jihar Anambra domin ƙaddamar da wasu ayyuka da Gwamna Chukwuma Soludo ya aiwatar
  • Mai girma Bola Tinubu ya yabawa Gwamna Soludo kan ayyukan ci gaba da gwamnatinsa ta ke gudanarwa a fadin jihar Anambra
  • Shugaban ƙasan wanda ya isa jihar da tsakar rana, ya samu tarba mai kyau daga wajen Gwamna Soludo da sauran manyan jami'an gwamnati

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Anambra - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yabawa Gwamna Chukwuma Soludo na jihar Anambra.

Shugaba Tinubu ya yabi Gwamna Soludo ne bisa shugabancinsa na hangen nesa da kuma samar da ababen more rayuwa da yake yi a jihar.

Tinubu ya yabi Gwamna Soludo
Tinubu ya kwararo yabo ga Gwamna Soludo Hoto: Prof. Chukwuma Soludo, Ibrahima Kaulaha Mohammed
Asali: Facebook

Tinubu, wanda ya isa Anambra a ranar Alhamis domin ƙaddamar da muhimman ayyuka da gwamnatin Soludo ta aiwatar, ya bayyana gamsuwarsa da nasarorin da gwamnan ya cimmawa, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaba Bola Tinubu ya isa jihar Anambra

Jaridar The Punch ta ce Shugaba Bola Tinubu ya sauka ne a filin jirgin sama na Chinua Achebe da ke Umueri, jihar Anambra, da misalin ƙarfe 12:17 na rana domin ziyarar aiki.

A cikin tawagar shugaban ƙasan akwai mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, da wasu manyan jami’an gwamnatinsa.

Waɗanda suka tarbe shi a filin jirgin sun haɗa da gwamnan jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo, mataimakinsa, Onyekachukwu Ibezim, mambobin majalisar dokokin jihar da sauran manyan baƙi.

Ayyukan da shugaban ƙasa zai ƙaddamar sun haɗa da cibiyar Emeka Anyaoku a Jami’ar Nnamdi Azikiwe, sabon Gidan Gwamnati, Solution Fun City, da titin Aroma zuwa Gidan Gwamnati mai layi takwas a garin Awka.

Me Tinubu ya ce kan Gwamna Soludo

Yayin da yake jawabi a wajen taron, Tinubu ya bayyana Soludo a matsayin aboki kuma jagora mai hangen nesa.

"Na ji daɗin kasancewa a nan. Ina yabawa abokina, Gwamna Chukwuma Soludo, wanda ke da hangen nesa kuma shugaba mai ƙwarewa, saboda ayyukan da yake aiwatarwa a jihar Anambra."

- Shugaba Bola Tinubu

Tinubu ya je jihar Anambra
Tinubu ya kaddamar da ayyuka a Anambra Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

An hana sanya kayan siyasa wajen tarbar Tinubu

Tun da farko, mai ba ba Gwamna Soludo shawara kan harkokin siyasa, Dr. Alex Obiogbolu, ya fitar da sanarwa yana bai wa mahalarta taron a dandalin Dr. Alex Ekwueme shawarar ka da su sanya kayan siyasa.

"Ana sanar da cewa duk wanda zai halarci taron tarbar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu yau a dandalin Dr. Alex Ekwueme, ya zo sanye da kaya na yau da kullum. Don Allah, ka da kowa ya sanya kayan APGA ko kayan ƙungiyoyin magoya baya.”

- Dr. Alex Obiogbolu

Mutanen Buhari suna goyon bayan Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu daga cikin manyan magoya bayan tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, sun yi wani zama a Abuja.

Magoya bayan na Buhari waɗanda suka yi jam'iyyar CPC tare, sun nuna goyon bayansu ga shugaban ƙass Bola Ahmed Tinubu.

Manyan ƙusoshin na tsohuwar jam'iyyar CPC sun kuma musanta jita-jitar da ke cewa suna shirin ficewa daga APC.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng