USAID: Ana Zargin Attajirin Duniya, Elon Musk Ya 'Kashe' Kananan Yaran Talakawa
- Babban mai ba da tallafi na duniya, Bill Gates ya zargi Elon Musk da kashe yaran talakawa ta hanyar dakatar da hukumar USAID
- Bill Gates ya bayyana cewa dakatar da USAID da Elon Musk ya yi ya sake haifar da yaduwar cututtuka kamar HIV da kyanda
- A hannu daya, Gates ya ce zai rufe gidauniyarsa a 2045, amma kafin nan, ya ce zai kashe kusan dukkanin dukiyarsa a harkar tallafi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Amurka - Hamshakin mai ayyukan jin kai, Bill Gates, ya ƙara ruruta rigimar da ke tsakaninsa da Elon Musk, inda ya zarge shi da 'kashe yaran talakawa a duniya.'
Bill Gates ya ce ta hanyar dakatar da ayyukan USAID, attajirin duniya, Elon Musk ya yi sanadiyyar mutuwar yaran da suka fito daga gidajen talakawa.

Asali: Twitter
Bill Gates ya soki Elon kan dakatar da USAID
A zantawarsa da jaridar Financial Times, Bill Gates ya ce Elon Musk ya yi aiki da jahilci wajen dakatar da ayyukan agaji da USAID ke yi a kasashen duniya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amma, Bill Gates ya ce yana shirin ƙara yawan agajin da ya ke bayarwa a duniya a cikin shekaru 20 masu zuwa, sannan zai rufe Gidauniyar Gates gaba ɗaya a 2045.
A watan Fabrairu, sashen Inganta Ayyukan Gwamnati (DOGE) wanda Musk jagoranta, ya dakatar da ayyukan hukumar USAID, babbar hukumar da Amurka ke kai agaji ga kasashen duniya.
Wanda ya kafa kamfanin Microsoft, kuma tsohon mafi arziki a duniya, Bill Gates ya ce dakatar da ayyukan USAID ya sa abinci da magunguna sun lalace a rumbunan ajiya.
Bill Gates ya zargi Elon Musk da 'kashe' yara
Hakazalika, Bill Gates ya ce dakatar da ayyukan USAID da Elon Musk ya yi ya haifar da sake bullar cututtuka kamar kyanda, HIV, da shan inna.
"Akwai abin takaici yadda mafi arziki a duniya yake kashe yaran da suka fi talauci a duniya" a cewar Bill Gates.
Bill Gates Gates ya ce Elon Musk ya soke tallafin asibiti a Lardin Gaza, Mozambique, wanda ke hana mata yada cutar HIV ga jariransu, da kuskuren tunanin cewa Amurka na samar da kwaroron roba ga Hamas a Gaza da Gabas ta Tsakiya.
"Zan so a ce ya shiga wadannan kasashe, ya hadu da yaran da suka kamu da cutar HIV yanzu saboda yanke kuɗin tallafin da ya yi."
- Bill Gates.

Asali: Getty Images
Bill Gates zai rufe ayyukan gidauniyarsa a 2045
Attajirin, mai shekaru 69, a ranar Alhamis ya sanar da shirye-shiryen kashe kusan dukiyar sa a cikin shekaru 20 masu zuwa.
Bill Gates ya kuma ce gidauniyarsa za ta kashe sama da dala biliyan 200 kan ayyukan agajin lafiya a kasashen duniya.
Hakazalika, ya ce gidauniyar za ta yi amfani da kudin wajen ci gaba da ilimin 'ya'yan talaka, kudin da suka haura dala biliyan 100 da ya kashe a cikin shekaru 25 da suka gabata.
Ya kara jaddada cewa za a rufe Gidauniyar Gates gaba dayanta a 2045, wanda hakan ke nufin cewa ya rage shekaru 10 daga asalin shekarar da ya so rufe gidauniyar.
USAID: Miliyoyin da Amurka ta ba Najeriya a 2024
A wani labarin, mun ruwaito cewa, a shekarar 2024, Najeriya ta kasance ta bakwai a jerin ƙasashen da suka fi karɓar tallafin Amurka, inda ta samu $763m daga USAID.
Hukumar USAID ta raba tallafin ga fannoni biyar masu mahimmanci: Lafiya, tsaro, tattalin arziƙi da mulki, abinci, da ilimi, wanda kowanne ya samu miliyoyin daloli.
A shekarar 2024, Ukraine ce ta karɓi mafi yawan tallafi da dala biliyan 6.1, sai Isra'ila, Afghanistan, Jordan, Ethiopia, Yemen, Sudan, Kudancin Sudan da Congo suka biyo baya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng