Kotu Ta Yanke Hukunci kan Karar da NNPP ta Nemi Tsige Gwamna da Mataimakinsa

Kotu Ta Yanke Hukunci kan Karar da NNPP ta Nemi Tsige Gwamna da Mataimakinsa

  • Jam'iyyar NNPP da ɗan takararta na gwamna a Ondo, Hon. Gbenga Edema sun yi rashin nasara a karar da suka kalubalanci Gwamna
  • Kotun ɗaukaka ƙara mai zama a Akure ta kori karar da NNPP da Edema suka nemi tsige Mai girma Lucky Aiyedatiwa da mataimakinsa
  • A cewar masu ƙara, an tafka wasu kura-kurai a zaben fitar da gwanin da APC ta yi wanda Gwamna Aiyedatiwa ya samu nasara

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ondo - Kotun daukaka kara da ke zama a Akure, babban birnin jihar Ondo, ta yi watsi da karar da ta kalubalanci sahihancin takarar Gwamna Lucky Aiyedatiwa a zaben da ya gabata.

Karar dai ta ƙalubalanci sahihancin zaben fidda gwanin da APC ta yi wanda ya samar da Gwamna Aiyedatiwa a matsayin ɗan takara a zaɓen gwamnan Ondo.

Gwamna Aiyedatiwa.
Kotun daukaka ƙara ta kori karar da aka nemi tsige gwamnan Ondo Hoto: Hon. Lucky Aiyedatiwa
Asali: Facebook

Tribune Nigeria ta tattaro cewa ɗan takarar gwamna a inuwar NNPP, Hon. Gbenga Edema ne ya shigar da ƙarar, yana mai neman a tsige gwamnan da mataimakinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ondo: Kotu ta kori ƙarar ɗan takarar NNPP

To ammma kotun ta yi watsi da karar ne bayan wanda ya shigar da karar ya gaza bin umarnin farko da kotun ta bayar.

Alkalin kotun ɗaukaka kara mai shari’a, Toyin Bolaji Adegoke, wacce ta jagoranci zaman, ta ce cire sunan NNPP a matsayin daya daga cikin masu karar ya rage karfin karar.

Don haka ne ta yanke hukuncin cewa karar ta zama mara amfani kuma ta sallameta nan take.

Kwamitin alkalai uku da suka saurari karar sun amince da wannan hukunci, inda suka ce karar ba ta da tushe balle makama.

Kotu ta ci tarar wanda ya shigar da ƙara

Bugu da ƙari, kotun ta ci tarar Edema tare umartar ya biya kowane ɗaya daga cikin waɗanda yake ƙara Naira miliyan daya (₦1,000,000).

Tun farko dai Edema, ta bakin lauyansa Mr. Abayomi Ojo, ya nemi kotu ta tilasta wa hukumar INEC ta soke sunayen Aiyedatiwa da mataimakinsa, Dr. Olayide Adelami, a matsayin ‘yan takarar APC.

Edema da NNPP ne masu kara a shari'ar yayin da Aiyedatiwa, Adelami, INEC da jam’iyyar APC ke cikin jerin wadanda ake kara.

Ya bukaci kotu ta fassara masa ma'anar yadda sashe na 15, sakin layi na uku a kundin tsarin mulki na 1999 (wanda aka gyara) ke aiki kan batun tsayar da ‘yan takara.

Tutar NNPP.
NNPP ta yi rashin nasara a kotun daukaka ƙara Hoto: NNPP
Asali: UGC

Wane hukunci kotun ɗaukaka ƙara ta yi?

Kotun dai ta tabbatar da cewa Gwamna Aiyedatiwa da mataimakinsa su ne sahihan ƴan takarar da APC ta tsayar a zaben gwamnan Ondo da aka yi ranar 16 ga watan Nuwamba, 2024.

Sakamakon haka kotun ta kori ƙarar gaba ɗaya bisa rashin cancanta, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

NNPP ta dakatar da ɗan takararta a Ondo

A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar NNPP ta dakatar da ɗan takararta na gwamna a zaɓen Ondo na 2024, Hon. Gbenga Edema da mataimakinsa.

Shugaban NNPP na Ondo, Peter Olagookun, da wasu jiga-jigan jam’iyyar 12 ne suka sanya hannu kan takardar dakatarwa da tsofaffin ƴan takarar.

NNPP ta ɗauki wannan mataki ne kan wasu zarge-zarge da ta bayyana da masu girma, ciki har da ƙarar da ya kai kotu ba tare da izinin jam'iyya ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262