Kotu Ta Yanke Hukunci a Shari'ar Sanata Natasha da Yahaya Bello, Ta Umarci Biyan N1bn
- Kotu ta zartar da hukunci a karar da tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya shigar kan Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan
- Babbar kotun da ke zamanta a Lokoja ta samu Sanata Natasha da laifin bata sunan tsohon gwamnan na jihar Kogi
- Bayan samunta da laifi, kotun ta umarci sanatar mai wakiltar Kogi ta Tsakiya ta biya diyya ga Yahaya Bello wanda ya shigar da karar
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kogi - Wata babbar kotu da ke Lokoja ta zartar da hukunci a shari'ar Sanata Natasha Akpoti Uduaghan da Yahaya Bello.
Kotu ci tarar Sanata Natasha N1bn a matsayin diyya a karar zargin bata suna da tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello, ya shigar.

Source: Instagram
Jaridar Vanguard ta ce wannan umarni yana ƙunshe ne a cikin takardar hukuncin kotun mai dauke da kwanan wata 23 ga watan Afrilun 2026 a Lokoja.

Kara karanta wannan
Za a gurfanar da sojoji 36 da ake zargi da yunkurin yi wa Tinubu juyin mulki gaban kotu
Wane hukunci kotu ta yanke?
Kotun ta bayyana cewa, bisa la'akari da hujjoji masu gamsarwa, an yanke hukuncin ne don goyon bayan mai shigar da ƙara.
Mai shari’a A. S. Ibrahim, yayin da yake yanke hukunci a cikin ƙarar mai lamba “HCL/16/2023”, ya bayyana cewa bayan kammala shari’ar, an warware batutuwa biyu da aka gabatar don tantancewa don goyon bayan mai ƙara.
Hukuncin kotun na cewa:
“Tattaunawar da wadda ake ƙara ta yi a ranar 4/11/2022 a shirin ‘The Morning Show’ na gidan talabijin na Arise TV, ɓatanci ne ga mutunci da martabar mai shigar da ƙara."
“A wannan tattaunawa ta ranar 4/11/2022, wadda ake ƙara ta siffanta mai shigar da ƙara a matsayin mai kisan kai, azzalumi, mai aikata munanan ayyuka, da kuma annoba ga mutanen jihar Kogi, ba tare da wata ƙwaƙƙwarar hujja ba.”
Sanata Natasha Akpoti za ta biya diyya
Haka kuma kotun ta ba da “umarnin dindindin na hana wadda ake ƙara, wakilanta, ko abokan siyasarta, ci gaba da fitar da kalaman ɓatanci ko kalmomi ga mai shigar d ƙara a gidajen talabijin ko na rediyo.
“An ba da umarnin biyan N1bn kacal a matsayin diyya ga wadda ake ƙara domin amfanin mai ƙara."
- A cewar kotun
Tsohon gwamna Yahaya Bello ne ya shigar da ƙarar Sanata Akpoti-Uduaghan saboda zargin ɓata masa suna, jaridar Premium Times ta kawo labarin.

Source: Twitter
Lauyan wadda ake ƙara, Johnson J. Usman (SAN), ya ƙalubalanci ikon kotun na sauraron ƙarar.
Bayan da Babbar Kotun ta yanke hukuncin cewa tana da ikon sauraron ƙarar, Sanata Akpoti-Uduaghan ta ɗaukaka ƙara kan wannan hukunci.
Sai dai, Kotun daukaka kara, a cikin ƙara mai lamba “CA/ABJ/CV/626/2024”, ta yi watsi da ɗaukaka ƙarar saboda rashin inganci, sannan ta tabbatar da cewa babbar kotun Jihar Kogi tana da ikon sauraron ƙarar.
Shaida ya yi magana a shari'ar Yahaya Bello
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani shaida na hukumar EFCC ya yi jawabi a gaban kotu a shari'ar da ake yi da tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello.
Kotun wadda ke zamanta a Abuja ta ji yadda aka yi zargin sauya dimbin kudaden da ke da alaka da Yahaya Bello zuwa dalar Amurka tare da mika su ga wani na kusa da shi.
Mai ba da shaidar, Jamilu Abdullahi, ya shaida wa kotu cewa an biya tsabar kudade sau da dama a cikin asusun kamfanin E-Traders International Limited a kwanaki daban-daban.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
