PDP Ta Kara Birkicewa bayan 'Yan Majalisar Wakilai 3 Sun Koma Jam'iyyar APC
- Jam'iyyar PDP mai adawa a jihar Katsina ta rasa wasu daga cikin mambobinta da ke majalisar wakilan Najeriya
- Ƴan majalisar wakilan guda uku sun sanar da ficewarsu daga jam'iyyar a zauren majalisa a ranar Alhamis, 8 ga watan Mayun 2025
- Tsofaffin 'yan PDP da suka koma APC sun bayyana cewa sun fice daga jam'iyyar ne saboda rikicin cikin gida da take fama da shi
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Jam'iyyar PDP ta rasa mambobi uku na majalisar wakilai daga jihar Katsina.
Ƴan majalisar wakilan waɗanda suka fito daga jihar Katsina sun fice daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Asali: Twitter
Jaridar TheCable ta ce shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, ne ya karanta takardun ficewarsu a zaman majalisar da aka yi a ranar Alhamis, 8 ga watan Mayun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ficewar ƴan majalisar ta sanya adadin mambobin majalisar wakilai da suka sauya sheƙa ya kai 27 tun bayan da aka ƙaddamar da ita a watan Yunin 2023, cewar rahoton jaridar The Nation.
Meyasa ƴan majalisar suka bar PDP zuwa APC?
Dukkan ƴan majalisar guda uku sun danganta ficewarsu da rikicin cikin gida da ke addabar jam’iyyar PDP.
Abdullahi Balarabe Dabai, wanda ke wakiltar mazaɓar tarayya ta Bakori/Danja, ya ce ya fice ne domin ya nemi wata jam'iyyar siyasa mafi kwanciyar hankali saboda rikicin da ya daɗe a PDP.
Ɗan majalisar ya koka cewa jam’iyyar PDP na fama da rikici tun daga shekarar 2022, kuma duk kokarin da aka yi domin magance rikicin ya ci tura, lamarin da ya shafi mambobin jam’iyyar.
Abubakar Albaba Aliyu, wanda ke wakiltar mazaɓar tarayya ta Batsari/Safana/Dan-Musa, ya ce ya bar PDP ne saboda rashin haɗin kan da take fama da shi.
Yusuf Majigiri, wanda ke wakiltar mazaɓar tarayya ta Mashi/Dutsi, ya bayyana matsanancin rikicin cikin gida mara ƙarewa na PDP a matsayin dalilinsa na ficewa daga jam'iyyar.
Ya ce ba shi da wani zaɓi face ya nemi wata jam'iyya domin ci gaba da siyasarsa da kuma tabbatar da ingantaccen wakilci ga jama’ar da yake wakilta.
Ya kuma ce ya gamsu da salon shugabanci na gaskiya da gwamnan Katsina ke yi, tare da tafiyar da gwamnati cikin haɗin kai da gaskiya.
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, shugaban jam’iyyar APC na jihar, Muhammad Ali da wasu manyan ƴan siyasa a jihar sun halarci zaman majalisar domin shaida ficewar ƴan majalisar daga PDP.

Asali: Facebook
Mutum muke bi ba jam'iyya ba
Wani mazaunin Bakori mai suna Kamal Musa ya shaidawa Legit Hausa cewa sauya sheƙar da Abdullahi Balarabe Dabai ya yi zuwa APC, ba zai hana son da suke yi masa ba.
"Mu mutum muke bi ba jam'iyya ba. Mun gamsu da irin wakilcin da yake yi mana a majalisar wakilai."
"Ficewarsa zuwa APC bai zo mana da mamaki ba domin jam'iyyar PDP ta gama hargitsewa a Najeriya."
- Kamal Musa
Shugaban majalisa ya magantu kan komawa APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban majalisar dokokin jihar Edo, Blessing Agbebaku, ya yi ƙarin haske kan dalilinsa na ficewa daga PDP zuwa APC.
Rt. Hon. Blessing Agbebaku ya bayyana cewa ya koma APC ne domin ya ci gaba da amfana da muƙaminsa na shugaban majalisar dokokin jihar.
Ya bayyana cewa mutanen mazaɓarsa sun goyi bayan matakin da ya ɗauka na yin bankwana da jam'iyyar PDP.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng