An Tono Shirin da Amurka Ta Yi wa Spain da Kasashen da Suka Ki Taya Ta Yakar Iran
- Wasu rahotanni sun nuna cewa an samu wani sako da ya nuna cewa Amurka ta fara barazanar dakatar da Spain daga kungiyar NATO
- Hakan na zuwa ne saboda yadda Spain da wasu kasashen Turai suka ki ba Amurka hadin kai a yakin da ta hada kai da Isra'ila ta yi da Iran
- Masana a kasar Amurka sun yi karin bayani game da sakon imel da aka gani daga ma'aikatar yakin Amurka da ke yi wa Spain barazana
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Wani sakon imel daga Ma’aikatar yakin Amurka (Pentagon) ya bayyana wasu matakai da Amurka za ta iya dauka domin hukunta kasashen kawancen NATO kan yakin Iran.
Za ta dauki mataki ne a kan kasashen da take ganin ba su ba ta cikakken goyon baya ba a yakin da ta yi da Iran, ciki har da yiwuwar dakatar da Spain daga cikin kawancen.

Source: Facebook
Shirin Amurka ga kasashen NATO
Rahoton Times of Israel ya nuna cewa wani jami’in Amurka ya bayyana cewa Gwamnatin shugaba Donald Trump za ta dauki mataki kan wasu kasashen NATO game da yakin Iran.
A cewar jami’in, imel din da aka gani ya kunshi korafe-korafe da ke nuna rashin jin dadin Amurka kan yadda wasu kawayenta suka nuna halin ko-in-kula kan yakin da ta gwabza da Iran.
Korafin ya kunshi rashin damuwa ko kin amincewa da ba ta damar amfani da sararin samaniya, sansanonin soja, da hanyoyin zirga-zirgar jiragen sama domin kai hari Tehran.
Imel din ya bayyana cewa damar da Amurka ta nema ita ce mafi karancin abin da ake tsammani daga mambobin NATO. Haka kuma, jami’in ya ce ana tattauna matakin da za a dauka a Pentagon.

Source: Getty Images
Daya daga cikin abubuwan da da imel din ya gabatar cikin matakan da za a dauka shi ne dakatar da kasashen da ake kallon suna da taurin kai daga mukamai masu muhimmanci ko daraja a cikin NATO.
Karin bayani daga Pentagon
Reuters ta rahoto cewa jami’in ya ce imel din bai ba da shawarar ficewar Amurka daga NATO ba, haka kuma bai hada da shirin rufe sansanonin sojan Amurka a Turai ba.
Da aka nemi karin bayani kan imel din, mai magana da yawun Pentagon, Kingsley Wilson, ya ce kamar yadda Trump ya fada, duk da irin kokarin da Amurka ta yi wa kawayenta na NATO, ba su tsaya mata ba a lokacin da take bukata.
An kama sojan Amurka
A wani labarin, mun kawo muku cewa Gwamnatin Amurka ta kama wani jami'in sojanta bisa zargin fitar da bayanan sirri game da kai hari Venezuela.
Ana zargin sojan ya je gidan caca a daidai lokacin da ake shirin kai hari kasar, inda ya yi hasashen cewa za a cafke shugaban Venezuela.
Hasashen sojan ya tabbata bayan farmakin Amurka da aka kai tare da shi kuma makudan kudin da ya samu ne suka ja hankalin jama'a zuwa gare shi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

