CPC: Mutanen Buhari Sun Yi Zama a Abuja, Sun Yi Matsaya kan Bola Tinubu a 2027
- Magoya bayan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari daga tsohuwar jam’iyyar CPC sun bayyana cikakken goyon bayansu ga Bola Ahmed Tinubu
- Sun bayyana haka ne bayan rade-radin cewa wasu daga cikinsu na shirin ficewa daga jam’iyyar APC saboda nuna rashin jin daɗi da mulkin shugaban kasar
- Taron da ya gudana a Abuja ya samu halartar jiga-jigai irinsu Aminu Masari, Buba Marwa, Dikko Radda da Tanko Almakura da sauran fitattun ‘yan siyasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - A wani mataki da ke nuni da haɗin kai a cikin jam’iyyar APC mai mulki, wasu daga cikin manyan magoya bayan Muhammadu Buhari sun yi taro a Abuja.
Yayin taron, magoya bayan na Buhari a tsohuwar jam’iyyar CPC sun bayyana cikakken goyon bayansu ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Asali: Facebook
Vanguard ta rahoto cewa jiga-jigan tsohuwar CPC sun musanta jita-jitar cewa suna fushi da Tinubu ko kuma suna shirin ficewa daga jam’iyyar APC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sun ce duk da cewa kowa na da ‘yancin bin ra’ayinsa na siyasa, ba daidai ba ne wasu su yi hakan suna fakewa da suna ko tarihin CPC don cimma burinsu.
Magoya bayan Buhari da suka halarci taron
Taron na Alhamis ya samu halartar fitattun mutane da dama daga 'yan siyasar Najeriya, ciki har da gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, da wakilin gwamnan Neja, Umar Bago.
Sauran sun haɗa da tsohon gwamnan Nasarawa, Sanata Tanko Almakura; tsohon gwamnan Katsina, Rt. Hon. Aminu Bello Masari.
Tribune ta rahoto cewa shugaban hukumar NDLEA, Janar Buba Marwa (Mai ritaya) na cikin wadanda suka halarci taron.

Asali: Facebook
Haka kuma, akwai tsohon daraktan hukumar VoN, Osita Okechukwu; tsohon mai ba shugaban kasa shawara, Okoi Obono Obla; da tsohon sakataren jam’iyyar APC na ƙasa, Waziri Bulama.
Sauran mahalarta sun haɗa da Farouk Adamu, wakilin shugaban majalisar wakilai Tajudeen Abbas, da ministan harkokin wajen Najeriya.
Mutanen Buhari sun ce suna tare da Tinubu
Da yake mayar da martani kan tambaya ko za su mara wa Tinubu baya a 2027, Farouk Adamu ya ce suna nan daram da shugaban kasa Tinubu, kamar yadda suka kasance tare da Buhari.
Farouk Adamu ya ce:
“Mu na tare da Tinubu kamar yadda shugabarmu Buhari ya ke. Muna fatan zai ci gaba da zama jagoranmu har zuwa 2027,”
Magoya bayan Buhari sun jaddada cewa ba za su raba kawunansu da jam’iyyar APC ba, suna masu cewa hadin kai da ci gaba da goyon bayan Tinubu zai inganta mulki a Najeriya.
Taron ya zama wata dama ta warware jita-jita da kuma ƙarfafa sahihiyar alakar da ke tsakanin tsofaffin magoya bayan Buhari da shugaban kasa Tinubu.
Yadda wasu masoya Buhari ke kallon gwamnatin Tinubu
Bayan kammala wa’adin mulkin Muhammadu Buhari a 2023, wasu daga cikin magoya bayansa, musamman daga tsohuwar jam’iyyar CPC, sun fara nuna alamun rashin jin daɗi da sabuwar gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.
Wannan rashin jin daɗi ya samo asali ne daga yadda wasu daga cikinsu suka ji cewa ba a ba su guraben mukamai ko tasiri da suka cancanta a gwamnatin Tinubu, duk da gudummawar da suka bayar wajen kafa APC da nasarar jam’iyyar a 2015.
Wasu daga cikin su sun fara fitar da maganganu da ke nuna cewa suna jin an yi watsi da su, kuma ana zargin cewa wasu daga cikinsu na shirin barin jam’iyyar.
Sai dai, domin hana rikicewa da raunana jam’iyyar, jiga-jigan CPC sun gudanar da taro a Abuja inda suka musanta jita-jitar.
Sun tabbatar da goyon bayansu ga Tinubu, suna cewa hadin kai ya fi komai muhimmanci.
Taron ya zama wata dama ta bayyana matsayarsu na goyon bayan Tinubu har zuwa 2027.
Duk da haka, zanga-zangar sirri da tursasawar siyasa da ke tsakanin sababbin kusoshi da tsofaffin magoya bayan Buhari na nuni da cewa akwai rikicewar cikin gida da gwamnatin Tinubu ke buƙatar magancewa cikin hikima.
'Aikin Buhari ne': An kare Tinubu kan tallafin mai
A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Kawu Sumaila da ya fice daga NNPP zuwa APC ya ba shugaba Bola Tinubu kariya.
Sanata Kawu Sumaila ya ce ba shugaba Bola Tinubu ba ne ya cire tallafin man fetur, kawai shi ya sanar da cire tallafin ne.
Kawu Sumaila ya ce tun a lokacin shugaba Muhammadu Buhari ba a sanya kudin tallafin mai a 2023 bayan watan Yuni ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng