INEC: Mahmud Yakubu Ya Nemi Afuwa kan Zaben Tinubu a 2023? An Samu Bayanai
- Wani shafi a dandalin Facebook da kuma wani gidan yanar gizo sun yada labarin karya cewa shugaban INEC ya nemi afuwar magudin zabe
- An binciki labarin kuma an gano cewa shafin yanar gizon da ya yada labarin na amfani da dabarar jawo hankalin jama'a ba tare da hujja ba
- Bincike bai gano wata kafa mai tushe da ta tabbatar da ikirarin ba, kuma babu bayanan da suka nuna lokacin da Mahmood ya furta haka
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Wani shafin Facebook mai suna Express ya wallafa sanarwa da ke ikirarin shugaban hukumar INEC ya nemi afuwar yan Najeriya.
A sanarwar an ce Mahmood Yakubu wanda shi ne shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ya nemi afuwa kan zargin canza sakamakon zaɓen 2023.

Asali: Twitter
Gaskiyar zancen neman afuwar Mahmud Yakubu?
Shafin Dubawa da ke bincike kan haka ya ce labarin ba shi da cikakkun bayanai da za su tabbatar da gaskiyar ikirarin wanda ya wallafa a X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Binciken ya kuma ce babu wata kafar labarai mai tushe da ta wallafa irin wannan bayani da ake yaɗawa.
Yawancin masu zaɓe a Najeriya ba su gamsu da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na 2023 ba, wanda ya haifar da nasarar Bola Tinubu.
Labarin ya ce Mahmood ya ce ya canza sakamakon ne saboda rayuwarsa da ta ‘yan uwansa na cikin haɗari.
A cewar rahoton, Mahmood ya bayyana cewa wannan mummunan abu yana daga cikin mafi wahala da ya taɓa fuskanta a rayuwarsa.
Yadda wannan ikirari ya bazu da kuma illarsa ga amincin tsarin zaɓe a Najeriya ya sa aka yi bincike na musamman.

Asali: UGC
Menene gaskiyar neman afuwar Mahmud Yakubu?
Binciken ya duba gidan yanar gizon kuma an karanta labarin, bayan haka, an lura cewa labarin ba shi da cikakken bayani kuma babu wurin da aka bayyana ko inda da kuma yaushe Mahmood ya furta hakan.
An danna tambarin gidan yanar gizon don duba shafinsa na gaba daya, amma duk kokarin ya tafi zuwa wasu shafukan kasuwanci.
Wannan yana daga cikin alamomin dabarar jawo hankali, kuma an riga ta binciki irin wadannan shafuka a baya.
An gano cewa shafin Facebook da ya wallafa ikirarin an kirkire shi ne a ranar 9 ga Yuni, 2019.
An tuntubi mai magana da yawun Mahmood Yakubu wato Rotimi Oyekanmi, don samun karin bayani, amma har zuwa lokacin rubuta wannan rahoto, ba a samu amsa daga gare shi ba.
Lokacin da Mahmud Yakubu zai bar INEC
Kun ji cewa shugaban INEC na ƙasa, Farfesa Mahmood Yakubu, zai kammala aikinsa a ƙarshen 2025 bayan cikar wa'adinsa na biyu.
Hukumar da fadar shugaban ƙasa sun karyata jita-jitar da ke yawo cewa an kore shi daga mukaminsa, sun bukaci jama'a su yi watsi da labarin.
An ce za a nada wanda zai gaje shi ta hanyar bin tsarin doka wanda ya haɗa da naɗin shugaban ƙasa, binciken DSS da tantancewar majalisa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng