'Yan Bindiga Sun Hallaka Basarake a Wani Harin Ta'addanci a Benue
- Ƴan bindiga ɗauke da makamai sun sanya mutanen ƙaramar hukumar Agatu a jihar Benue cikin jimami bayan wani hari da suka kai
- Miyagun ƴan bindigan sun hallaka Hakimin Odugbeho bayan sun buɗe masa wuta lokacin da yake aiki a gonarsa
- Shugaban ƙaramar hukumar Agatu da rundunar ƴan sandan jihar Benue sun yi magana kan lamarin mara daɗin ji
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Benue - Ƴan bindiga sun hallaka wani basarake a harin da suka kai a jihar Benue.
Ƴan bindigan sun hallaka Hakimin Odugbeho da ke cikin ƙaramar hukumar Agatu ta jihar Benue, Cif Anthony Adejoh.

Asali: Facebook
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa ƴan bindigan sun hallaka basaraken ne tare da wani mai suna Jerry John a ranar Laraba, 7 ga watan Mayun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan bindiga sun kashe basarake a Benue
Miyagun ƴan bindigan sun hallaka su ne a Otobi-Akpa da ke cikin ƙaramar hukumar Otukpo, bayan sun farmake su.
Mutanen biyu suna cikin aikin gona ne a Otobi lokacin da maharan suka mamaye su sannan suka buɗe musu wuta.
Daga baya, mutanen da suka ji ƙarar harbe-harbe sun garzaya zuwa wurin, inda suka tarar da gawarwakinsu kwance a ƙasa.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, shugaban ƙaramar hukumar Agatu, Marvis Ejeh, ya ce Cif Adejoh ya rasa ransa ne a gonarsa da ke Akpa-Otobi sakamakon harin da wasu ƴan bindiga suka kai misalin ƙarfe 10:00 na safe.
Ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai son zaman lafiya, mai kishin al’umma kuma jagora wanda mutane da dama za su yi kewarsa matuƙa.
"Eh da gaske ne an kashe Hakimin Odugbeho, Cif Tony Adejo. Wasu makiyaya ɗauke da makamai ne suka kashe shi yayin da yake aikin noma a gonarsa da ke Otobi a ƙaramar hukumar Otukpo ta jihar."
“Duk da wannan mummunan labari, al’ummar Odugbeho suna zaune cikin kwanciyar hankali, mutanenmu sun haƙura domin ba za mu ɗauki doka a hannunmu ba.”
“Babu wanda zai dauki doka a hannunsa, babu buƙatar ramuwar gayya domin lamarin bai faru a garinmu ba. Agatu na cikin zaman lafiya."
- Marvis Ejeh
Wane bayani ƴan sanda suka yi?
Legit Hausa ta tuntuɓi kakakin ƴan sandan jihar Benue, CSP Catherine Anene, domin samun ƙarin bayani kan lamarin.
Kakakin ƴan sandan ta bayyana cewa ba ta samu rahoto kan harin ba.
"Ban samu rahoto kan faruwar lamarin ba."
- CSP Catherine Anene
Duk da haka ta ce za ta tuntuɓi DPO na Agatu kan lamarin. Sai dai har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton ba a sake ji daga gare ta ba.
Ƴan bindiga sun kashe sufeton ƴan sanda
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan binɗiga ɗauke da makamai sun hallaka wani jami'in ɗan sanda a jihar Benue.
Ƴan bindigan sun hallaka ɗan sandan ne mai matsayin sufeto lokacin da yake dawowa daga ƙauyensu bayan ya je jinya.
Rundunar ƴan sandan jihar Benue ta tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a ranar Laraba, 7 ga watan Mayun 2025.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng