"Ba Abin da Tinubu Ya Kawo sai Wahala," CUPP Ta ba Yan Najeriya Shawara game da Zaɓen 2027
- Ƙungiyar CUPP ta caccaki gwamnatin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu bisa jefa ƴan Najeriya cikin ƙangin wahala da ƙaƙanikayi
- CUPP ta bayyana cewa duba da halin da aka aka shiga a zangon mulkin Tinubu na farko, shugaban ƙasar ba zai iya share hawayen jama'a ba
- Ta bukaci ƴan Najeriya su yi wa kansu karatun ta natsu, su kawar da jam'iyyar APC a zaɓen 2027 saboda zargin ta kawo karin matsaloli
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Gamayyar jam’iyyun siyasa a Najeriya (CUPP), ta caccaki gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan matakan tattalin arziki da ta dauka da suka jefa 'yan kasa cikin matsanancin hali.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun kungiyar, Kwamared Mark Adebayo ya fitar, CUPP ta bayyana gwamnatin APC a karkashin Tinubu da, “mara imani, mai girman kai da rashin kishin kasa”.

Asali: Facebook
Kungiyar ta ce babu wani sabon abu da Shugaba Tinubu zai iya kawo wa kasar a halin yanzu, illa kara tabarbarewar tattalin arziki da matsalar tsaro, Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wane hali Najerita ta shiga a mulkin Tinubu?
A cewar CUPP:
“Najeriya na tafiya ne kamar ba ta da shugaba, kamar jirgin ruwa da ya rasa matuki, sakamakon salon mulkin Tinubu wanda ke nuna rashin tausayi da kishin kasa da al’umma.”
Kungiyar ta kara da cewa mai girma shugaban ƙasa ba shi da lokacin jama'a kuma ga dukkan alamu ba shi ne mafita ga wahalhalun da al'umma ke ciki ba.
CUPP ta ba yan Najeriya shawara kan 2027
Bisa haka ne CUPP ta yi kira ga ƴan Najeriya su tashi tsaye, su kawo ƙarshen mulkin APC a babban zaɓen 2027.
Ta kara da cewa matsalar tsaro a Najeriya ta kai wani mataki mai muni da daruruwan mutane ke rasa rayukansu a kowanne mako a jihohi kamar Filato, Benue, da Borno, yayin da gwamnati ke nuna halin ko-in-kula.
Kungiyar CUPP ta zargi Shugaba Tinubu da fifita lafiyarsa ta kashin kansa fiye da walwalar ‘yan Najeriya da ya rantse da Allah zai kare.

Asali: Facebook
An zargi gwamnatin Tinubu da rashin tsari
Ta kuma ce gwamnatin Tinubu ba ta da tsari, inda har yanzu babu jakadu na Najeriya a kasashen duniya.
Haka kuma CUPP ta bayyana cewa hukumomin gwamnati kamar Hukumar Haraji ta FIRS da Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta Kasa (NPA) da wasu da dama ba su da kwamitin gudanarwa tun bayan nadinsu.
A cewarta, rashin majalisun gudanarwa a wadannan hukumomi na nufin duk wasu kudi ko kwangilar da ake bayarwa ba bisa ka’ida ba ne.
A karshe, CUPP ta ce gwamnati ta kasa shirya wani babban taron tsaro domin samo mafita ga matsalolin da ke addabar kasar, lamarin da ta bayyana a matsayin gazawa.
Aliyu Kabir, wani mazaunin Katsina a Najeriya ya shaida wa Legit Hausa cewa ai babu bukatar faɗawa jama'a wanda za su zaɓa a 2027.
A cewarsa, kowa ya san halin da ake ciki na wahala, don haka ya ragewa mutane su zaɓi wanda ya dace ko su koma gidan jiya.
"Bana tunanin ɗan Najeriya na bukatar a faɗa masa wanda zai zaɓa a 2027, wannan wahala da yunwa kaɗai sun koya wa kowa darasi, Allah Ya zaɓa mana shugabanni na gari," in ji shi.
Tinubu ba zai iya gyara Najeriya ba - Jigon APC
A wani labarin, kun ji cewa wani jigo a APC, Eze Chukwuemeka Eze, ya yi ikirarin cewa Bola Tinubu ba zai iya warware matsalolin Najeriya ba.
Mista Eze ya ce wannan ne ya sa mutane daga sassa daban-daban na ƙasar nan suka fara rokon tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya fito takara a 2027.
A cewarsa, Amaechi mutum ne mai nagarta wanda ke da duk wano abin da ake bukata wajen tsamo Najeriya daga ramin da ta faɗa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng