Ningi: Babban Kuskuren da zai Hana Wasu Sanatoci da 'Yan Majalisu Koma wa Kujerunsu a 2027
- Sanata Abdul Ningi ya ce akwai babban kalubalen da zai taka rawa wajen hana wasu daga cikin 'yan majalisu da sanatoci koma wa kujerunsu
- Ya bayyana cewa rashin aiwatar da kasafin 2024 da 2025 ya jawo matsala ga ‘yan majalisa saboda ba a iya ganin manyan ayyuka a yankunan da su ke wakilta
- Abdul Ningi ya bayyana haka ne yayin da wasu daga cikin sanatocin da yan majalisu ke kokarin sake neman jama'a su zaben su bayan an kada gangar siyasa
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Sanatan da ke wakiltar mazabar Bauchi ta Tsakiya, Abdul Ningi, ya bayyana cewa rashin aiwatar da kasafin kudin shekarun 2024 da 2025 ya yi tasiri matuka kan aikin ‘yan majalisar tarayya a yankunansu.

Kara karanta wannan
Hormuz: Matakin Amurka da Iran ya ta'azzara farashin fetur a duniya, ganga ta haura $100
Sanatan ya ce wannan matsala na iya hana da dama daga cikin sanatoci da ‘yan majalisar wakilai komawa majalisa a zaben shekarar 2027.

Source: Facebook
Da yake magana a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels TV a ranar Alhamis, 23 ga watan Afrilu na shekarar 2026, ya ce wannan zai zama illa ga wakilan da ke son a sake zabensu.
Ningi: Yan majalisa za su gamu da matsala
Jaridar Punch ta wallafa cewa Ningi ya ce rashin aiwatar da kasafin ya zo masu da mamaki ganin cewa manyan ayyukan da ake yi ba za su taɓa al'ummar yankuna kai tsaye ba.
Ningi ya ce:
“Ba mu samu aiwatar da kasafin 2025 ba; abin ya ba mu mamaki, domin a gwamnatin da ta gabata mun samu nasara sosai wajen aiwatar da kasafi."
Sanatan ya bayyana cewa rashin aiwatar da wadannan kasafi ya janyo matsala ga ‘yan majalisa, domin yawancinsu ba su da abin da za su nuna wa al’ummomin da suke wakilta yayin da ake tunkarar zabe.
A cewarsa:
“Ba za mu iya komawa mazabunmu ba domin ba mu iya kawo ayyukan da muka dauki alƙawari ba sakamakon rashin sakin kudi, kuma hakan na nufin sake zabarmu na cikin hadari.”
Ya kara da cewa jama’a na sa ran ganin ayyuka a mazabunsu, amma halin da ake ciki ya sa hakan ya zama kalubale ga ‘yan majalisar.
"Gwamnati ta karkata ga manyan ayyuka": Ningi
Ningi ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na mai da hankali wajen kashe kudi kan manyan ayyuka na musamman, maimakon ayyukan mazabu.
Ya ce wannan salon ba ya amfanar kai tsaye ga al’ummomin yankuna, inda ake bukatar kananan ayyuka da ke shafar rayuwar yau da kullum.

Source: Twitter
A cewarsa:
“Wannan ba ya magana kai-tsaye kan ayyukan mazabu. Haka kuma mun gano cikin takaici cewa wannan gwamnati ta karkatar da kudi da yawa zuwa ga gwamnoni fiye da kowace gwamnati da ta gabata, a wasu lokuta har sau uku.”
Sanata Abdul Ningi ya kara da cewa, a irin wannan yanayi, ‘yan majalisar ba za su iya jingina wani aiki ga gwamnatin jiha ba, haka kuma ba za su iya nuna wani abin da suka samu daga Gwamnatin tarayya ba.
Ya yi gargadi cewa wannan matsala na iya haifar da sauyi mai yawa a majalisa bayan zaben 2027, domin da dama daga cikin ‘yan majalisar ba za su samu damar dawowa ba saboda rashin abin da za su nuna wa masu zabe.
2027: Ningi ya mika kudiri majalisa
A baya, mun wallafa cewa Majalisar dattawa ta bukaci gwamnati ta duba yiwuwar dakatar da harkokin siyasa a jihohi takwas na Arewacin Najeriya yayin da ake shirin fara tunkarar 2027.
A zaman majalisar, Sanata Abdul Ningi ya ce rashin tsaro ya zama barazana ga kasa baki daya, ba wai yankunan kaɗai ba, amma akwai kokarin a fara daukan mataki a kan siyasar yankin.
Haka kuma Majalisar tarayyar ta nemi a gaggauta ceto mutane 416 da ake ‘yan ta’addan Boko Haram suka sace a Borno bayan wa'adin da aka bayar na biyan bukatu kafin a sake su ya kusa cika.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

