Ta Faru Ta Kare: Jam'iyyar APGA Ta Amince Tinubu Ya Yi Tazarce a 2027

Ta Faru Ta Kare: Jam'iyyar APGA Ta Amince Tinubu Ya Yi Tazarce a 2027

  • Gwamnan Anambra ya ce APGA ta amince da Shugaba Bola Tinubu a matsayin ɗan takararta a zaben shugaban kasa na 2027
  • Charles Soludo ya tunatar da Tinubu cewa APGA ta goyi bayan shugaban ƙasa mai ci a 2011, don haka za ta goyi bayansa a 2027
  • Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da Tinubu ya je Anambra domin ƙaddamar da ayyukan da aka kammala a jihar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Anambra - Gwamna Charles Soludo na jihar Anambra ya bayyana cewa jam'iyyarsa ta APGA ta amince da Shugaba Bola Tinubu a matsayin ɗan takararta a zaɓen.

Gwamna Charles Soludo ya ƙara jaddada cewa APGA da jam'iyyar APC za su yi aiki tare, saboda dukkan jam'iyyun sun ginu ne akan manufofin ci-gaban al'umma.

Gwamnan Anambra ya ce APGA za ta goyi bayan Tinubu a zaben 2027
Gwamnan jihar Anambra, Charles Soludo tare da Shugaba Bola Tinubu a fadar shugaban kasa, Abuja. Hoto: @CCSoludo
Asali: Twitter

APGA ta amince Tinubu ya yi tazarce a 2027

Gwamnan jihar na Anambra ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a filin Alex Ekwueme da ke birnin Awka, lokacin da Tinubu ya ziyarci jihar, inji rahoton Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake magana a gaban shugaban kasar, Gwamna Charles Soludo ya jaddada cewa jam'iyyun da suke da burin samar wa al'umma ci gaba za su yi aiki tare.

Ana ganin wannan matsaya da gwamnan tare da jam'iyyar APGA suka dauka, za ta kara taimakawa Tinubu a lokacin da zai nemi tazarce a zaɓen 2027.

'Dalilin APGA na goyon bayan Tinubu' - Soludo

Soludo ya tunatar da Tinubu cewa APGA tana da manufar tallafawa shugaban ƙasa da jam'iyya mai mulki a matakin tarayya, yana mai jaddada cewa wannan manufar na nan daram.

A cewar gwamnan:

“A shekarar 2011 kafin na shiga APGA a 2013, APGA ta ɗauki matsaya a hukumance na tallafawa da kuma yin aiki tare da jam’iyya mai mulki da gwamnati a matakin kasa.

“Hakika, a waccan shekarar, APGA ta amince da shugaban ƙasa mai ci a lokacin a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa kuma ina so in sanar da kai cewa manufar APGA ba ta canza ba.”

Soludo ya ce lokaci ya yi da dukkanin jam'iyyun da aka kafa su da sunan 'All Progressive' su haɗa kai don inganta Najeriya tare da kawo ci gaba da haɗin kai mai dorewa.

Shugaba Bola Tinubu ya kaddamar da muhimman ayyuka a Anambra
Shugaba Bola Tinubu, yayin da yake kaddamar da ayyuka a jihar Anambra. Hoto: @CCSoludo
Asali: Twitter

Tinubu ya kaddamar da ayyuka a Anambra

Idan ba a manta ba, a safiyar Alhamis dinnan ne muka ruwaito cewa shugaban kasa Bola Tinubu zai ziyarci jihar Anambra domin kaddamar da muhimman ayyuka.

Rundunar 'yan sandan jihar ta ce ta kammala dukkanin wasu shirye-shirye da sauran hukumomin tsaro domin ganin ziyarar shugaban ta gudana cikin nasara.

A sanarwar da ya fitar a shafinsa na X, hadimin shugaban kasa ta fuskar kafofin sada zumunta, Olusegun Dada, ya ce:

"Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da Cibiyar Nazarin Harkokin Ƙasashen Duniya da Diflomasiyya ta Emeka Anyaoku a jami'ar Nnamdi Azikiwe, Awka.  
"A halin yanzu kuma yana ƙaddamar da birnin Solution Funcity, wanda ya ƙunshi Anambra Country Club, gidan nishaɗi na iyali, filin wasan ruwa, da filin shakatawa."

Tinubu ya yabawa gwamnan Anambra

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya isa jihar Anambra domin ƙaddamar da ayyukan ci gaban da Gwamna Chukwuma Soludo ya aiwatar.

Yayin kaddamar da ayyukan, Tinubu ya yabawa Soludo kan ayyukan ci gaban da gwamnatinsa ke gudanarwa a faɗin jihar Anambra.

Shugaban ƙasar, wanda ya isa jihar da tsakar rana, ya samu tarba mai kyau daga Gwamna Soludo da sauran manyan jami'an gwamnati.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.