Yakin Duniya na 3? Isra'ila na Shirin Kai Sabon Hari Iran, Irin Wanda Ta Kai wa Hamas

Yakin Duniya na 3? Isra'ila na Shirin Kai Sabon Hari Iran, Irin Wanda Ta Kai wa Hamas

  • Gwamnatin kasar Isra'ila ta yi barazanar kai hare-haren kan Iran kamar yadda ta yi wa Hamas bayan harin Houthi a filin jirgin sama
  • Isra'ila ta kuma gargadi Iran da ta daina tallafa wa Houthi, tana mai cewa za ta yi wa Tehran abin da suka yi wa Beirut, Gaza, da Damascus
  • An ce Isra'ila ta kai hare-hare kan Houthi a Sana'a, yayin da ta dage cewa ba ta bukatar wani taimako daga Amurka don kare kanta

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Isra'ila - A ranar Alhamis, 8 ga Mayu, Ministan tsaron Isra'ila, Israel Katz ya yi barazanar cewa za su yi wa Iran irin abin suka yi wa Hamas a Gaza.

Isara'ila ta yi barazanar kai sabon hari Iran kwanaki kaɗan bayan harin da 'yan tawayen Houthi masu goyon bayan Iran suka kai filin jirgin sama na Ben Gurion.

Isra'ila ta yi barazanar kai hari kan Iran kamar yadda ta yi wa Hamas
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu | Jagoran Iran, Ayatollah Ali Khamenei. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Isra'ila ta yi barazanar kai hari kan Iran

Kafar labaran Isra'ila, ta ruwaito Israel Katz yana cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ina gargadin shugabannin Iran da ke ba da kuɗi da makamai don daukar nauyin ƙungiyar ta'addanci ta Houthi, da su sani cewa, gadar zaren ta tsinke kuma za su rufta a ramin muguntar da suke hakawa.
"Duk abin da ya faru, ku kuka da kanku. Za mu yi maku irin abin da muka yi wa Hezbollah a Beirut, Hamas a Gaza, zuwa abin da muka yi wa shugaban Siriya, Bashar al-Assad da aka hambarar a yanzu a Damascus."

Tare da Hezbollah da Hamas, 'yan tawayen Houthi na Yemen na daga cikin rundunonin da Iran ke takama da su a wajen adawa da Isra'ila da kawayenta, Amurka.

Hezbollah ta kai hare-hare a watan Oktobar 2023 domin nuna goyon baya ga Hamas, bayan harin da ta kai Kudancin Isra'ila, wanda ba a taɓa ganin irinsa ba.

Isra'ila ta mayar da martani kan Houthi

An ji cewa kafin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a watan Nuwamba, sojojin Isra'ila sun kusan murƙushe Hezbollah, yayin da aka ragargaza shugabancin Hamas a harin 7 ga Oktoba.

'Yan Houthi sun kai hari kan babban filin jirgin sama na Isra'ila kusa da Tel Aviv a ranar Lahadi, a wani ɓangare na yaƙin da suke yi da Isra'ila, in ji 'yan tawayen, domin nuna goyon baya ga Falasɗinawa a Gaza.

Sai dai kuma Iran ta musanta cewa tana goyon bayan Houthi a wannan harin da suka kai, inji rahoton Leadership.

Amma, Isra'ila ta mayar da martani ga Houthi da hare-hare a filin jirgin sama na birnin Sana'a, inda 'yan tawayen ke riƙe da shi, da kuma kan cibiyoyin wutar lantarki na birnin.

Isra'ila ta ce ba ta bukatar taimakon Amurka wajen kare kasarta
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu. Hoto: Getty Images
Asali: AFP

Iran ta ce ba ta neman taimakon Amurka

Jami'ai sun kuma nuna damuwa a ɓoye game da tattaunawar nukiliya ta Amurka da Tehran da ke kawo cikas ga yiwuwar matakin soja na Isra'ila kan Jamhuriyar Musulunci.

Sai dai, ministan tsaro, Katz, a hirarsa da 'yan jarida a ranar Alhamis, ya nuna cewa Isra'ila ba ta buƙatar dogaro da Amurka ko goyon baya ko tallafinta a wannan yaki.

"Dole ne Isra'ila ta iya kare kanta da kanta daga kowace barazana ko maƙiyi. Hakan ya kasance gaskiya a baya kuma zai kasance a nan gaba," inji ministan.

India ta kai hare-hare kan Pakistan

A wani labarin, mun ruwaito cewa, a ranar Laraba, 7 ga Mayu, 2025, kasar Indiya ta harba makamai masu linzami a kan Pakistan da wani yanki na Kashmir.

Indiya ta bayyana cewa ta kai harin ne kan wurare tara da ake zargin 'yan ta'adda ne, waɗanda take zargi da kai hari kan 'yan yawon buɗe ido a Kashmir.

Sai dai, Pakistan ta mayar da martani, inda ta ce harin na Indiya ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula 26, kuma ta yi ikirarin harbo jiragen yaƙin Indiya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.