Yahaya Bello: EFCC Ta Gabatar da Shaida a Shari'ar Tsohon Gwamnan Kogi
- Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta gabatar da shaida a karar da ta shigar kan tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello
- Mai ba da shaidar da EFCC ta gabatar a kotu ya yi bayani filla-filla kan yadda ya rika sauya kudaden da ke da alaka da Yahaya Bello
- Ya bayyana cewa ya rika sauya tsabar kudi na Naira zuwa dalar Amurka inda yake mika su ga wani na kusa da tsohon gwamnan
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ci gaba da sauraron karar da hukumar EFCC ta shigar kan tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello.
Kotun ta ji yadda aka yi zargin sauya dimbin kudaden da ke da alaka da Yahaya Bello zuwa dalar Amurka tare da mika su ga wani na kusa da shi.

Source: Twitter
Jaridar TheCable ta kawo rahoton cewa mai ba da shaida na EFCC ne ya yi bayanin hakan a ranar Alhamis, 23 ga watan Afirilun 2026.
Shaidar EFCC ya yi bayani a kotu
Wani dan canji mai suna Jamilu Abdullahi, ya je kotu a matsayin shaida na 12 na masu shigar da kara a shari’ar.
Shari'ar ta mayar da hankali kan zargin almundahanar kudi har Naira biliyan 80.2 da hukumar yaki da yi wa tattalin arziki zagon kasa (EFCC) ta shigar kan Yahaya Bello.
Yayin da yake bayar da shaida karkashin jagorancin lauyan EFCC, Kemi Pinheiro, Jamilu Abdullahi ya shaida wa kotu cewa an biya tsabar kudade sau da dama a cikin asusun kamfanin E-Traders International Limited a kwanaki daban-daban.
Ya ce Abba Adaudu ne ya yi ajiyar kudaden, wanda shi ne mutumin da suka yi mu’amala da shi kai tsaye a lokacin gudanar da hada-hadar, rahoton jaridar Premium Times ya tabbatar da hakan.
An sauya kudade zuwa Dalar Amurka
Jamilu Abdullahi ya ce ko da yake sunansa ya bayyana ta fuskoki daban-daban a wasu bayanan hada-hadar, ba shi ne ke da alhakin yin ajiyar kudaden ba.
“Sunayen da aka nuna an yi amfani da su ne a matsayin bayanin hada-hadar, amma ba ni ne na yi ajiyar kudaden a reshen Lokoja ba."
- Jamilu Abdullahi
Mai ba da shaidar ya kara da cewa bayan karbar kudaden, ya sauya Naira zuwa Dalar Amurka tare da mika tsabar kudaden ga Adaudu.
A cewarsa, hada-hadar ta gudana ne a kwanaki daban-daban, ciki har da Oktoban 2021 da Maris din 2022.
An rika zuwa ana karbar kudade
Jamilu Abdullahi ya kuma shaida wa kotun cewa kamfaninsa, Kunfayakun Global Limited, ya karbi Naira miliyan 100 da Naira miliyan 400 a watan Disambar 2021 daga kamfanin Keyless Nature Limited, wanda ya ce yana da alaka da Adaudu.
Mai ba da shaidar ya ce an bayar da kudaden ne don sayen dala, kuma daga baya aka sauya su aka kai su.

Source: Facebook
Dan canjin ya kara bayar da shaidar cewa a watan Fabrairun 2022, ya karbi Naira miliyan 600 a lokuta daban-daban, da kuma karin naira miliyan 325 ta hannun RTGS zuwa asusun da ke da alaka da hada-hadar, duk domin manufa guda.
Mai ba da shaidar ya ce an mika dalar ne ko dai a ofishinsa ko kuma a ofishin Adaudu da ke Area 8, Abuja.
“Abin da zan iya tunawa shi ne yawanci yana zuwa ofishina ne don karbar dala."
- Jamilu Abdullahi
Kotu ta ba Yahaya Bello iznin tafiya
A wani labarin kuma, kun ji cewa wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta ba tsohon gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, izinin tafiya zuwa kasar Saudiyya.

Kara karanta wannan
Hormuz: Ana zargin dakarun Iran sun buɗe wa jirgin ruwan da ya yi kunnen ƙashi wuta
Kotun ta ba shi wannan damar domin shiga Saudiyya saboda gudanar da Umrah ta shekarar 2026 da muke ciki.
Alkalin da ke jagorantar shari'ar ya bayar da umarnin sakin fasfon kasa da kasa na Yahaya Bello na wucin gadi, wanda ke hannun kotu, domin ya samu damar zuwa gudanar da ibadar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


