Latest
DSS ta kama Sani Galadi a Sokoto yana kokarin tafiya aikin Hajji. Ana zargin Galadi da garkuwa da mutane a Zamfara, kuma yanzu haka yana hannun DSS domin bincike.
‘Yan bindiga da ake zargin Lakurawa ne sun kai hari a coci a kauyen Zagani, Kebbi, inda suka sace mata da dama. Gwamnati ta tabbatar da sace mutum 10.
Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya ce mafi yawan alkalai sun zama masu karɓar na goro, sun daina yi wa jama'a adalci a shari'sr Najeriya.
Gwamna Francis Nwifuru ya ƙara albashi ga sababbin likitoci zuwa N500,000, ya kuma kaddamar da shirin samar da magunguna a farashi mai rahusa a jihar Ebonyi.
Rt. Hon. Alhassan Doguwa ya ce ba sa jin tsoron kowa ya shiga APC, yana mai jaddada cewa Kano da Najeriya duk tafiyar Ganduje ce a siyasa kuma dole a bi shi.
Tsagin NNPP ya nemi gafarar shugaban kasa Bola Tinubu, Abdullahi Ganduje da dukkan 'yan APC kan kalaman da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi kan sauya sheka.
Atiku Abubakar ya yi wa Peter Obi tayin zama mataimakinsa a zaben 2027 a shirin hadakar 'yan adawa domin kayar da APC da Bola Tinubu. Za su iya komawa ADC.
Kano ta haramta haska fina-finai 22 na Kannywood saboda sabawa da al’adu, lamarin da ke haifar da ce-ce-ku-ce. Fina finan da aka hana haskawa sun hada da Labarina.
Mataimakiyar kakakin Majalisar Dokokin jihar Edo, Misis Maria Oligbi-Edeko ta ajiye kujerarta, ta ce ta yi murabus ne saboda a yi wa kowa adalci.
Masu zafi
Samu kari