El Rufai Ya Sake Kwanto Rigima, Ya Yi Kaca Kaca da Ɓangaren Gwamnatin Najeriya

El Rufai Ya Sake Kwanto Rigima, Ya Yi Kaca Kaca da Ɓangaren Gwamnatin Najeriya

  • Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce adalci a ɓangaren shari'a ya yi ƙaranci saboda yadda rashin gaskiya ya yi wa alƙalai katutu
  • El-Rufai ya soki ɓangaren shari'a wanda ke zaman kansa a tsarin gwamnatin Najeriya, yana mai cewa ya koma sai da kuɗi ko mulki
  • Ya buƙaci alƙalai da lauyoyi su zauna su yi wa kansu karatun ta natsu, su tuna muhimmancin yi wa kowa adalci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya kwancewa ɓangaren shari'a a Najeriya zani a kasuwa kan cin hanci da rashawa.

Malam Nasir El-Rufai ya soki alkalai da lauyoyi a Najeriya, yana mai cewa galibinsu sun yi nisa a harkokin rashawa da rashin gaskiya.

Malam Nasiru El-Rufai.
El-Rufai ya yi kaca kaca da bangaren shari'a a Najeriya Hoto: Nasir El-Rufai
Asali: Twitter

Tsohon gwamnan ya yi wannan furuci ne ranar Litinin da yake jawabi a makon ƙungiyar lauyoyi ta Najeriya (NBA) reshen Bwari a Abuja, Premium Times ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

El-Rufai ya yi kaca-kaca da bangaren shari'a

El-Rufai ya ce yanzu mutane sun daina yarda da shari’a a Najeriya saboda jinkirin yanke hukunci da kuma zaluntar mai gaskiya ta hanyar take masa haƙƙinsa.

Malam Nasir El-Rufai ya bayyana cewa shari’a a Najeriya ta koma iya kuɗinka da ikonka, iya gaskiyarka a gaban kotu, idan ba ka da kudi to ba za a maka adalci ba.

Har ila yau, ya soki amfani da umarnin wucin gadi a cikin shari’ar siyasa, yana zargin wasu lauyoyi da amfani da kotu domin cimma burinsu na siyasa.

Ya bukaci alkali da lauyoyi da su duba muhimmancin aikinsu, tare da tabbatar da ana yin adalci, ba tare da tasirin bangaren zartarwa ba.

Wane irin lalacewa ɓangaren shari'a ya yi?

"A gefe guda, bangaren shari’a, wanda ya kamata ya zama ginshikin adalci da doka, ya zama abin zargi.
"Kalubale irin su jinkirin yanke hukunci, gaza bin hanyoyin da aka shimfida, da kuma wasu lokutan cin hanci a kotuna, sun sa jama'a sun daina yarda da shari'a.

"Ƙaruwar shiga kotuna daban-daban domin samun hukuncin da ake so, amfani da umarnin wucin gadi don cimma burin siyasa da sauransu, ya sa ake ganin kotuna sun bar tubalin adalci.

- Nasir Ahmad El-Rufai.

Nasir El-Rufai.
El-Rufai ya bukaci alkalai da lauyoyi su tuna muhimmancin ayyukansu ga rayuwar jama'a Hoto: Nasir El-Rufai
Asali: Facebook

El-Rufai ya faɗi masu yin nasara a kotuna

Taohon gwamnan ya ƙara da cewa yadda kotuna suka koma iya kudi ko ikon ka iya gaskiyarka, ya sa sun daina amsa taken da ake cewa shari'a gatan talaka a Najeriya.

“A Najeriya, akwai gibi mai girma tsakanin doka da adalci. Ba wai kawai ana neman adalci ba ne, hatta dokar da ake aiki da ita ana maida ita kamar yadda bangaren zartarwa ke so.
"Don haka akwai bukatar ku, a matsayin ku na ma’abota doka, ba abin da ake bukata daga wurinku sai adalci," in ji shi.

El-Rufai bai tsoron sauya-shekar gwamnoni

A wani labarin, kun ji cewa Nasir El-Rufai ya bayyana cewa haɗakar da suke shirin yi a ƙasar ba ta bukatar goyon bayan gwamnoni kafin ta samu nasara.

Ya ce ko da gwamnoni ko ba gwamnoni, haɗakar ƴan adawa za ta ba da mamaki kuma za ta ceto ƙasar nan daga halin ƙaƙaƙani kayi.

Da aka tambaye shi ko akwai yiyuwar a tsayar da ‘yan takara kamar Atiku Abubakar ko Peter Obi, El-Rufai ya ce yanzu ba lokacin hakan ba ne.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262