'Yana cikin Hatsari': Iyalan Sarki da Aka Sace Sun Fara Neman Taimakon Kuɗin Fansa
- Iyalin Sarkin da aka yi garkuwa da shi a Yabga sun nemi taimako domin tara kudin fansa da masu garkuwa da shi ke bukata
- Sun ce sun riga sun tara N25m ta hanyar sayar da kadarori, amma masu garkuwa da shi sun ki karba sai an biya N50m
- Dangin sun bukaci taimako daga mutane, kungiyoyi da 'yan siyasa, suna kuma rokon addu'o'i da karin kokarin jami’an tsaro
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Lokoja, Kogi - Bayan sace basarake a jihar Kogi, iyalansa sun koka kan halin da yake ciki a hannun yan bindiga.
Iyalan Dada James Ogunyanda, Obalohun na Okoloke a karamar hukumar Yagba ta Yamma a Kogi sun roki taimakon jama’a da kungiyoyi.

Asali: Facebook
An ƙaryata neman N12m kuɗin fansar Sarki
Masarautar ta ce an sace Sarkin ne daga fadarsa da misalin karfe 2:00 na safe ranar Alhamis da ta gabata inda aka kai shi wani wuri, cewar The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wata majiyar fada ta shaida cewa ba gaskiya ba ne cewa an rage kudin fansa zuwa N12m kamar yadda wasu ke yaɗawa bayan sace Sarkin.
Majiyar ta ce:
“A ranar Lahadi 18 ga watan Mayun 2025 mu a matsayin iyali, mun tara N25m.
"Amma wadanda suka yi garkuwa da shi na nan kan matsayinsu na N50m, da fari N100m suka nema.”
An soki gwamnati da sakaci wajen Sace Sarki
Iyalan sun bayyana takaici kan yadda gwamnati da 'yan siyasa musamman 'yan majalisa daga Kogi ta Yamma suka ki taimaka inda suka ce wasu ma sun toshe layinsu.
Sun bayyana cewa sun sayar da wasu kadarori domin tara N25m domin neman sako musu dan uwa.
“Muna cikin damuwa sosai domin lafiyar sarkinmu na kara tabarbarewa.
“Muna rokon duk wanda ke da zuciya mai tausayi da kungiyoyi su cika mana N50m.”
“Rayuwar sarkinmu na cikin hadari; muna bukatar taimako daga kowane bangare: ‘yan jarida, ma’aikata, malamai, ‘yan kasuwa."

Asali: Original
Rokon iyalin Sarki ga 'yan siyasan Kogi
Sun yi kira musamman ga Sanata Dino Melaye, Sanata Sunday Karimi, Leke Abejide, James Faleke, Natasha Akpoti-Oduaghan da sauransu su taimaka.
Iyalin sun kuma roki malamai da limamai su ci gaba da yin addu’a, tare da bukatar karin kokari daga jami’an tsaro domin ceto sarkin, cewar Punch.
“Gaba dayan iyalin suna cikin damuwa da halin da sarkinmu ke ciki tun bayan sace shi kwanaki biyar da suka wuce.
“Muna kaunar sarkinmu sosai, muna rokon Allah ya bai wa jami’an tsaro nasara wajen kubutar da shi da sauran wadanda aka sace."
- Cewar majiyar
'Yan bindiga sun yi ta'asa jihar Kogi
Kun ji cewa wasu yan bindiga sun kuma kai hari a jihar Kogi inda suka kashe matasa uku da ake zargin ‘yan sa-kai ne a Ofoloke.
Majiyoyi sun ce matasan ‘yan sa-kan an dauke su ne don kare ma’aikatan sadarwa da suka je gyara na’urar sadarwa a daji.
Wani matashi, Demola Samuel, ya ce al’umma na cikin fargaba da damuwa, dole ne a dauki matakan tsaro.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng