Hadakar 2027: Atiku Ya Yi wa Peter Obi Tayin Zama Mataimaki bisa Sharuda

Hadakar 2027: Atiku Ya Yi wa Peter Obi Tayin Zama Mataimaki bisa Sharuda

  • Rahotanni sun nuna cewa Atiku Abubakar ya miƙa wa Peter Obi tayin takarar mataimakin shugaban ƙasa a ƙarƙashin tikitin wa'adin shekara huɗu
  • An bayyana cewa Peter Obi ya amince da tayin amma yana ci gaba da tuntubar magoya bayansa kafin a sanar da haka a hukumance
  • Saboda rikice-rikicen da ke cikin PDP da LP, ana duba yiwuwar amfani da jam’iyyar ADC a matsayin sabuwar mafita ga 'yan adawa a Najeriya a 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, na ci gaba da kokarin kafa kawancen jam’iyyun adawa domin kayar da shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.

Wasu rahotanni sun nuna cewa bangaren Atiku Abubakar ya miƙa tayin mataimakin shugaban ƙasa ga Peter Obi.

Atiku
Atiku ya yi wa Obi tayin mataimaki a 2027. Hoto: Atiku Abubakar|Mr Peter Obi
Asali: Facebook

Majiyoyi masu tushe sun tabbatar wa jaridar The Punch cewa Atiku ya gabatar da wannan tayin ne ga Obi a wani taro da suka yi a Birtaniya tun farkon shekarar 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku ya yi wa Obi tayin mataimaki a 2027

Majiyoyin da ke kusa da bangarorin biyu sun bayyana cewa Atiku ya amince zai yi wa’adi guda na shekaru huɗu, sannan ya mika mulki ga Obi idan sun yi nasara a 2027.

A cewarsu, Obi ya yarda da shirin, kuma a shirye suke su sanya hannu a yarjejeniya idan ya zama dole. Sai dai, Obi na kokarin samun goyon bayan masoyansa kafin a fito da sanarwar.

Wani jigo a jam’iyyar PDP ya ce sun fahimci cewa haɗin kai tsakanin Atiku, Obi da wasu ‘yan adawa ne kawai zai iya karɓar mulki daga APC.

A cewar jigo a PDP, tuni wasu daga cikin 'yan bangaren Peter Obi suka shiga jam’iyyar ADC don shirin duba mafita.

Kwanan nan aka ji jam'iyyar adawa ta ADC ta na zancen kifar da Bola Tinubu a 2027.

Rade radin komawar Atiku da Obi ADC

Duk da rikicin da ke cikin jam’iyyun PDP da LP, wasu daga cikin jagororin kawancen suna tuntubar jam’iyyar ADC domin mayar da ita dandalin takara.

Shugaban jam’iyyar ADC, Ralph Nwosu, ya tabbatar da cewa akwai tattaunawa da shugabannin siyasa da ma wasu daga cikin gwamnati, ciki har da masu ruwa da tsaki a APC.

Nwosu ya ce nan da ƙarshen mako za su fitar da sanarwar da za ta fayyace matakin da aka kai wajen kafa jam’iyya mai ƙarfin gwiwa wacce za ta ceto Najeriya daga halin da take ciki.

Bayanin makusanta Obi kan hadaka

Duk da irin rahotannin da ke yawo, wasu daga cikin magoya bayan Obi sun ce ba su samu sahihin bayani daga Obi kan wannan yarjejeniya ba.

Shugaban ƙungiyar ‘Obedient Movement’, Yunusa Tanko ya ce Obi bai sanar da shi wani shiri irin haka ba.

Haka zalika, Peter Ahmeh na CUPP ya ce har yanzu ana nazarin rikicin da ke cikin jam’iyyar LP kafin a yanke hukunci.

Peter Obi
Bangaren Obi sun ce ba su samu bayani kan hadakar 2027 ba. Hoto: Mr Peter Obi
Asali: Facebook

Zaben 2019 da na 2023

A zaben shekarar 2019, Peter Obi ya kasance ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na Atiku Abubakar a karkashin jam’iyyar PDP.

Wannan kawance ya samu karɓuwa daga magoya baya saboda an yi hakan kallin gamin haɗin gwiwa mai ƙarfi tsakanin bangarorin Arewa da Kudu maso Gabas.

Sai dai bayan zaben 2019 da Atiku ya sha kashi, alaƙar siyasa tsakanin Atiku da Obi ta fara sauyawa.

A shekarar 2023, Peter Obi ya yanke shawarar fita daga jam’iyyar PDP saboda wasu matsaloli ciki har da rashin jituwa da shugabannin jam’iyyar.

Obi ya kafa jam’iyyar Labour Party (LP) domin ya nemi takarar shugaban ƙasa a zaben 2023. Wannan mataki ya nuna rabuwa sosai tsakanin Atiku da Obi, inda kowannensu ya bi hanyarsa daban.

A wannan lokacin, Obi ya samu goyon baya sosai a kudu maso gabas, yayin da Atiku ya cigaba da jagorantar PDP.

Legit ta tattauna da dan PDP a Gombe

Wani dan PDP a Gombe, Bilyaminu Yahaya ya ce hadaka tsakanin Atiku da Obi ne mafita ga 'yan adawa a Najeriya.

Matashin ya ce:

"Ya kamata su cire son rai su daidaita tsakaninsu. Muna da tabbas za mu kayar da Bola Tinubu idan sun hadu."

ADC ta ce za ta kori APC da Tinubu a 2027

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar ADC ta ce tana shirin tabbatar da cewa APC da Bola Tinubu ba su samu nasara a 2027 ba.

Shugaban jam’iyyar ADC na kasa, Ralph Nwosu ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai a Abuja a makon da ya wuce.

Legit ta rahoto cewa Ralph Nwosu ya ce za su tara miliyoyin kuri'u idan suka yi hadaka domin korar APC daga mulkin Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng