"Tinubu na Tsaka mai Wuya," PDP Ta Canza Lissafi kan Haɗakar Atiku, Obi da El Rufai a 2027

"Tinubu na Tsaka mai Wuya," PDP Ta Canza Lissafi kan Haɗakar Atiku, Obi da El Rufai a 2027

  • Duk ta ce ba za ta shiga haɗaka ba, PDP ta hango yadda Atiku Abubakar, Peter Obi da Nasir El-Rufai za su lashe zaɓen 2027 cikin sauƙi
  • Mataimakin shugaban matasan PDP, Timothy Osadolor ya ce matukar waɗannan jiga-jigai uku suka cire son rai, za su kawo sauyi a 2027
  • Ya ce idan aka haɗa kuri'un da Atiku da Obi suka samu a zaɓen 2023, za a gane ƙarfin tasirin da haɗakar za ta iya idan ba su sanya son rai ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Duk da nesanta kanta daga shiga haɗakar ƴan adawa, jam'iyyar PDP ta bayyana cewa kawancen, Atiku Abubakar, Peter Obi da Nasir El-Rufai na da haɗari.

PDP ta ce haɗewar tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku da fitattun ƴan siyasa kamar Peter Obi da El-Rufai na iya karya lago tare da kayar da Bola Tinubu a zaɓen 2027.

Peter Obi, Atiku da El-Rufai.
PDP ta ce haɗakar Atiku, Obi da El-Rufai za ta iya kayar da APC a 2027 Hoto: Peter Obi, Atiku Abubakar, Nasir El-Rufai
Asali: UGC

Babbar jam'iyyar adawa ta yi hasashen cewa irin wannan hadaka na iya sa a gama zabe tun da karfe 1:00 na rana a ranar zabe, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mataimakin shugaban matasan PDP na ƙasa, Hon. Timothy Osadolor, shi ne ya bayyana hakan a Abuja a ranar Litinin.

Sai dai ya ce nasarar hadakar ta dogara ne kan kyaun niyya, hadin kai da kuma iya amfani da fushin jama’a duba da halin ƙuncin rayuwa da suke ciki, rahoton This Day.

Atiku, Obi da El-Rufai za su kayar da Tinubu

Ya jaddada cewa jimillar kuri’un Atiku da Obi da suka haura miliyan 13 a zaben 2023 idan aka kwatanta da na Tinubu miliyan takwas, ya ƙara nuna tasirin da haɗakar za ta iya yi.

“Idan aka gama tattaunawa kuma aka kai matakin da ya dace, girman kai bai shiga tsakanin wadannan manyan mutane ba; Atiku, Obi, da El-Rufai, to tabbas za su iya zama tawagar nasara.

"Idan Atiku da Obi suka yi dagaske wajen goyon bayan wannan hadaka kamar yadda ake gani yanzu, sannan El-Rufai ma ya taka rawarsa yadda ya kamata, ban ga dalilin da zai sa ‘yan Najeriya su ki wannan hadakar ba.”
“A karshe, wannan zaɓe mai zuwa zai zama tsakanin ‘yan Najeriya ne da Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyarsa watau APC.”

- Hon. Timothy Osadolor.

Atiku da Obi.
PDP ta yi hasashen faɗuwar Tinubu idan jagororin ƴan adawa suka haɗa kansu Hoto: Atiku Abubakar
Asali: UGC

Najeriya na fama da talauci da rashin aikin yi

Timothy, mamba a kwamitin gudanarwa na PDP (NWC) ya ce yunwa, rashin tsaro, damuwa da takaici da ke karuwa a Najeriya na daga cikin muhimman abubuwan da za su iya jan hankalin masu kada kuri’a su goyi bayan hadakar.

Ya kuma kara da cewa yawancin ‘yan Najeriya na fatan ganin bayan APC, inda ya kawo misalin yadda aka sauke tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan daga mulki a zaben 2015.

Atiku ya yi wa Obi tayin takara a 2027

A wani labarin, kun ji cewa ana raɗe-raɗin Atiku Abubakar ya yi wa Peter Obi tayin zama ɗan takarar mataimakin shugaban kasa a 2027.

An ruwaito cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kuma yi alkawarin cewa wa'adi ɗaya zai yi a mulki kuma a shirye yake ya rattaɓa hannu kan yarjejeniya.

Majiyoyi sun nuna cewa Obi ya amince da tayin kuma a shirye suke su duka biyun, su sanya hannu a yarjejeniya idan ya zama dole.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262