Gwamna Zulum Ya Fadi Manyan Dabaru 2 da ke ba Ƴan Ta'adda Damar Kai wa Sojoji Hari

Gwamna Zulum Ya Fadi Manyan Dabaru 2 da ke ba Ƴan Ta'adda Damar Kai wa Sojoji Hari

  • Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya ce ‘yan ta’adda na amfani jirage marasa matuka wajen kai wa sojojin Najeriya hari
  • Babagana Zulum ya bayyana cewa lallai akwai bukatar a sabunta kayan tsaro da ƙarfafa haɗin gwiwar jama’a da gwamnati don a yaƙe su
  • Ya bayyana haka ne a wani taron tsaro da aka gudanar a Kogi na neman tara N500bn domin inganta tsaro da kayan aikin jami'an Najeriya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kogi – Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya bayyana wani sabon ƙalubale da ke kara dagula yaƙin da ake yi da matsalar rashin tsaro a Najeriya, inda ya ce yanzu ’yan bindiga da ’yan tada ƙayar baya.

Gwamnan, wanda jiharsa ke daga cikin jihohin da matsalar ƴan ta'adda ta yi ƙamari ya ce miyagun mutanen na amfani da sababbin fasahohi wajen bibiyar dakarun sojoji.

Kara karanta wannan

Tofa: Iran ta kai sabon hari da zai iya rusa shirin tattaunawar sulhu da Amurka

Gwamna Zulum ce ƴan ta'adda suna kara amfani da sababbin dabaru
Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno Hoto: The Governor of Borno state
Source: Twitter

Nigerian Tribune ta wallafa cewa Zulum ya yi wannan bayani ne a ranar Talata, 21 ga watan Afrilu, 2026 yayin kaddamar da taron koli kan tsaro da kuma taron tara kuɗi na jihar Kogi da aka gudanar a cibiyar taro ta rundunar sojin sama (NAF) a Abuja.

Ƴan ta'adda na kai wa sojoji hari

A cewarsa, ’yan ta’addan da ke yankin Arewa maso Gabas sun fara amfani da jiragen sama marasa matuki da kuma fasahar basirar na’ura ta AI domin gano wuraren da kayan aikin sojoji da kuma jami’an tsaro suke.

Ya ce:

"Yanzu ƴan bindiga da ƴan ta'adda na amfani da jirage marasa matuka da fasahar AI a filin daga wajen gano wuraren da ma'aijiyar makamai ta ke."

Gwamnan ya jaddada cewa wajibi ne gwamnati ta rika sabunta kayan aikin tsaro, tattara bayanan sirri, horaswa da kuma ƙwarewar jami’an tsaro lokaci zuwa lokaci domin tunkarar sabbin dabarun ’yan ta’adda.

Kara karanta wannan

Yadda sojoji da tsohon minista suka raba miliyoyin Naira don kifar da gwamnatin Tinubu

Kiran Gwamna Zulum kan ƴan ta'adda

Haka kuma, ya yi kira da a ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin jama’a da gwamnati domin dakile matsalar rashin tsaro da ke ƙara ta’azzara a sassan ƙasar.

Zulum ya bayyana jihar Kogi a matsayin wata muhimmiyar hanya da ke haɗa Arewa da Kudu, inda ya bukaci gwamnan jihar, Usman Ododo, da ya ƙara ƙarfafa tsarin tsaron jihar domin tabbatar da zaman lafiya da bunƙasar tattalin arziki.

Gwamnan Kogi ya ce ba zai saura wa ƴan ta'adda ba
Gwamnan jihar Kogi, Ahmed Ododo Horo: Alhaji Ahmed Ododo
Source: Facebook

A nasa bangaren, Gwamna Ododo ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta shiga sulhu da masu aikata laifi ba, yana mai jaddada aniyar tinkarar su kai tsaye.

Taron tsaro na jihar Kogi, wanda tsohon gwamnan Zamfara, Sanata Abdulaziz Yari, ke jagorantar kwamitin tara kuɗi, na da burin tara Naira biliyan 500 domin inganta tsarin tsaro, faɗaɗa ayyuka da kuma sake ƙarfafa hukumomin tsaro da kayan aiki.

Ƴan ta'adda sun yi barazana

A baya, mun wallafa cewa ƙungiyar Boko Haram ta bayar da wa’adin sa’o’i 72 tare da barazana kan mutane 416 da ta yi garkuwa da su a wani daji da ba za a sake ganinsu ba.

Kara karanta wannan

Kotu ta ɗauki mataki kan buƙatar belin El Rufai, Malam zai zauna a hannun ICPC

'Yan ta'addan sun yi barazanar rarraba su zuwa wurare daban-daban idan ba a biya bukatunta da ta zayyana wa gwamnati ba, daga ciki har da yanka masu fansar biliyoyin Naira.

Ƙungiyar ƴan ta'addan Boko Haram ta yi wa gwamnati taƙama, inda ta ƙalubalance ta a aiko dakaru sun zo su kwaci mutanen idan ana ganin akwai ƙarfin da za a yi hakan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng