'Kano Ta Ganduje ce,' Hon. Alhassan Doguwa Ya Tsokano Masu Shiga Jam'iyyar APC

'Kano Ta Ganduje ce,' Hon. Alhassan Doguwa Ya Tsokano Masu Shiga Jam'iyyar APC

  • Rt. Hon. Alhassan Ado Doguwa ya bayyana cewa shi da sauran manya a APC ba sa tsoron kowa ya shiga jam’iyya mai mulki a kasa
  • Dan majalisar, mai wakiltar Tudunwada/Doguwa na wannan batu ne awanni kadan bayan haduwarsu da Rabi'u Musa Kwankwaso
  • Ya kara da cewa duk wanda ke son ya shiga APC, sai ya yi biyayya da Shugaban jam'iyya, Dr. Abdullahi Umar Ganduje

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar KanoDan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Tudun Wada/Doguwa ta Kano, Rt. Hon. Alhassan Ado Doguwa, ya ce ba sa jin tsoron kowa dangane da shirin shigarsu APC. Rt. Hon. Doguwa, wanda shi ne shugaban kungiyar 'yan majalisun Arewa, ya ce babu wanda zai iya razana su da maganar sababbin masu shigowa jam’iyya mai mulki.

Doguwa
Dan Majalisar Kano ya ce Ganduje ne jagoran da za a bi a APC Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso/Alhassan Ado Doguwa TV
Asali: Facebook

Ya bayyana hakan ne a cikin wani bidiyo da Basiru Yusuf Shuwaki ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya shata iyaka da wasu yan siyasa da bai ambaci sunayensu ba.

Doguwa ya caccaki masu niyyar komawa APC

Duk da bai ambaci sunan kowa ba, amma kalaman Hon Alhassan Ado Doguwa na zuwa ne jim kaɗan bayan ya hadu da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a fadar Sarkin Zazzau.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin jawabinsa, Rt. Hon. Ado Doguwa ya ce:

"Kano ta Ganduje ce. Ni da ma da ake cewa za su dawo, cewa na yi a bar kowa ma ya shigo."
"Kowa ma ya shigo, amma kowa ya sani cewa bakin rijiya ba wajen wasan yaro ba ne. Idan ma za ka je kana wani wasa a wajen Nasarawa, ko ka je wasa a Shanono ko Bagwai, ko Rogo ko Karaye."
Alhassan
Alhassan Ado Doguwa ya ce babu wanda ke ba su tsoro Hoto: Alhassan Ado Doguwa TV
Asali: UGC

Doguwa ya nanata cewa mazabar Tudun Wada da Doguwa ba wuri ba ne da wasu za su zo su riƙa gwaji da jam’iyyar APC.

"Najeriya ma ta Ganduje ce" - Hadimin Doguwa

A wata ganawa da Legit a Kano, Auwal Ali Sufi Utai, mai magana da yawun Rt. Hon. Doguwa, ya ce babu gardama a batun shugabanci a APC.

Ya ce:

"Najeriyar ma ta Ganduje ce domin shi ne shugaban jam’iyya, kuma duk wanda zai shiga jam’iyyar APC a yau, ba sai gobe ba, Ganduje shugabansa ne."

Utai ya ƙara da cewa duk wanda ke sha’awar shiga APC, ya kamata ya tafi mazabarsa, ya yanki fam, ya yi rajista, sannan ya nuna biyayya ga Ganduje.

Matsalar da Ado ke fuskanta da Kanawa

Rt. Hon. Alhassan Ado Doguwa, dan siyasa ne mai tasiri a jam’iyyar APC kuma dan majalisar tarayya daga Kano, wanda yake fuskantar kalubale daga wasu Kanawa a jihar.

Wannan rikici ya samo asali ne daga sabanin siyasa, musamman ma game da yadda ake rarraba mukamai da damar siyasa tsakanin 'yan jihar.

Ado Doguwa daga karamar hukumar Doguwa ne kuma dan jam'iyyar APC, inda wasu 'yan jihar ke masa kallon wanda bai cancanci shugabanci ba.

Matsalar ta kara tsananta ne saboda karuwar tasirin Ado Doguwa a cikin jam’iyyar APC da kuma kusancinsa da gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje.

Wasu daga cikin Kanawa suna ji cewa an dora mulki a hannun wasu ‘yan kalilan ne kawai, lamarin da ya rage masu dama da wakilci a siyasar jihar.

Doguwa da magoya bayansa sun dage cewa duk wanda zai shiga APC dole ne ya bi umarnin Ganduje, wanda hakan ya sa wasu kungiyoyi suka fara ficewa ko samun matsala a cikin jam’iyya.

Wannan rikici na nuna yadda siyasa ta kabilanci da bin kungiyar a makance ke taka rawa a Kano, kuma zai iya kara tsananta kafin zaben gaba.

Doguwa ya yi martani ga Kwankwaso

A wani labarin, kun ji cewa dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Tudun Wada/Doguwa a Kano, Rt. Hon. Alhassan Ado Doguwa, ya yi kaca-kaca da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

Rt. Hon. Doguwa ya ce kalaman da Kwankwaso ke yi na sukar gwamnatin Bola Tinubu ba su da tushe, domin yana fama da radadin faduwa a zaben 2023 da ya gabata.

Hon. Ado Doguwa ya shawarci Kwankwaso da ya daina tada jijiyoyin wuya tun da wuri, ya mayar da hankali wajen shirin yin ritaya daga harkar siyasa bayan zaben 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.