Hajji: A Karo na 2 cikin Sa'o'i 24, Dubun Ƙasurgumin Ɗan Bindiga Ta Cika a Filin Jirgin Sama

Hajji: A Karo na 2 cikin Sa'o'i 24, Dubun Ƙasurgumin Ɗan Bindiga Ta Cika a Filin Jirgin Sama

  • A karo na biyu cikin sa'o'i 24, jami'an hukumar DSS sun kama wani jagoran dabar ƴan bindiga, Sani Galadi yana kokarin tafiya aikin hajji
  • An ruwaito cewa a wannan karon, dakarun DSS sun kama kasurgumin ɗan garkuwar ne a filin jirgin sama da ke Sakkwato
  • Wata majiya daga cikin jami'an tsaro ta ce tuni aka fara gudanar da bincike bayan kama Sani Galadi kuma za a gurfanar da shi a kotu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Sokoto - Jami’an Hukumar Tsaro ta DSS sun cafke wani da ake zargi da babban jagoran dabar masu garkuwa da mutane ne, Sani Galadi, a Filin Jirgin Sama na Sultan Abubakar da ke Sokoto.

Jami'an DSS sun damƙe wanda ake zargin ne yau Litinin yayin da yake shirin tafiya ƙasa mai tsarki domin sauke farali a aikin hajjin bana.

Jami'an DSS.
Jami'an DSS sun sake kama wani ɗan bindiga a hanyar zuwa ƙasar Saudiyya Hoto: DSS
Asali: Facebook

Daily Trust ta ce Sani Galadi ya shiga hannu da misalin karfe 11:15 na safe a lokacin da ake tantance mahajjata gabanin kwashe su zuwa Saudiyya domin yin aikin hajji.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda DSS ta cafke ɗan bindigar a Sokoto

Rahoto ya nuna cewa jami’an sashin leken asiri sun bi diddigin Sani Galadi har suka kama shi a sashen hajj na filin jirgin sama da ke birnin Sakkwato.

Hakan na zuwa ne kasa da awanni 24 bayan an kama wani ƙasurgumin ɗan garkuwa da aka dade ana nema a sansanin mahajjata da ke Abuja, yana kokarin tafiya Saudiyya.

An ce wanda aka kama a Abuja yana cikin waɗanda jami'an tsaro ake nema ruwa a jallo kan sace-sacen mutane da ake zarginsa da hannu a Kogi da Abuja.

Dubun ɗan bindiga ta cika a Sakoto

Wata majiya mai karfi daga cikin jami’an tsaro ta tabbatar da kama ɗan bindigar a filin sauka da tashin jirage da ke Sakkwato.

A cewar majiyar, jami’an leken asiri na ci gaba da gudanar da ayyukan sirri domin kawar da miyagun laifuka daga kasar nan, rahoton Punch.

“Eh, an kama wani Sani Galadi yau a filin jirgi yayin da yake gab da tsallake matakan binciken kafin tashinsa zuwa Saudiyya,” in ji majiyar.

Ta ya wanda ake zargi ya samu fasfo?

Da aka tambayi yadda mutum kamar irin wannan ya samu fasfo da sauran takardun tafiya daga hukumomi daban-daban, jami’in ya ce:

“Wannan tambaya za ku iya tambayar hukumomin da suka ba shi wadancan takardun.”
"Abin da nake da tabbaci da shi shi ne, Sani Galadi yana hannun jami’an tsaro kuma yana amsa tambayoyi da suka dace. Za a gurfanar da shi a gaban kotu bayan kammala bincike.”

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, ba a samu jin ta bakin kakakin hukumar DSS ko jami'an kula da harkokun hajji ba.

NAHCON ta shirya wa alhazai abinci mai kyau

A wani labarin, kun ji cewa hukumar kula da jim daɗin alhazai watau NAHCON ta ce maniyyatan Najeriya za su samu abinci mai gina jiki a ƙasa mai tsarki.

NAHCON ta bayyana cewa ta dauki tsauraran matakan duba inganci da tsafta yayin zaben gidajen da za su rika dafawa mahajjatan abinci.

NAHCON ta kuma hana amfani da sinadarai masu illa ga jiki, inda ta buƙaci amfani da sinadarai na gargajiya da aka saba da su.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262