Kano: Yan Sanda Sun Fadi Wadanda Suka Caccakawa Malamin Kur'ani Wuka har Lahira

Kano: Yan Sanda Sun Fadi Wadanda Suka Caccakawa Malamin Kur'ani Wuka har Lahira

  • Wasu bata-garin matasa sun kashe wani malamin addini a Kano bayan da suka yunkura kamar za su sace masa waya
  • Rundunar ‘yan sandan Kano ta tabbatar da cewa al’amarin ya faru a unguwar Gidan Sarki yayin wata haramtacciyar kilisa
  • Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce zuwa yanzu an kama wasu da ake zargi da hannu a cikin kisan

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Wasu bata garin matasa sun kashe mashahurin malamin addini kuma kwararre a fannin fasaha, Alaramma Jabir Lawan Abdullahi yayin wata haramtacciyar kilisa a Kano.

Rahotanni sun nuna cewa an sokawa malamin wuka sau da dama da wuka yayin kilisar da ta gudana a ranar Asabar a unguwar Gidan Sarki a cikin birnin Kano.

Alaramma
Gurbatattun matasa sun kashe Alaramma Jabir Hoto: Jabir Lawan Abdullahi
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta rahoto cewa rundunar 'yan sandan jihar Kano ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Litinin, inda ta bayyana cewa taron bai samu izini daga hukumomi ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka kashe alaramma a Kano

Arewa Updates ta ruwaito cewa rahotannin farko sun nuna cewa an kai wa malamin hari ne da nufin sace masa waya a lokacin da yake cikin adaidaita sahu a cunkoson ababen hawa.

Wannan bai zo da mamaki ba, ganin yadda masu kwacen waya da yan daba ke cin karensu babu babbaka, musamman a kwaryar birnin Kano.

Yan sanda
Yan sanda sun ce an kashe Alaramma Jabir yayin kilisa Hoto: Jabir Lawan Abdullahi
Asali: Facebook

An ruwaito cewa bayan matasan sun kusanto Alaramma Jabir, sai suka buga masa makami, sannan suka tsere.

Sai dai mai magana da yawun rundunar 'yan sanda ta jihar Kano, SP Haruna Abdullahi, ya karyata wannan jita-jita, yana mai cewa lamarin ba ya da alaka da satar waya.

Ya ce:

"Ba batun satar waya bane. Lamarin ya faru ne yayin wata kilisa.Yayin wannan kilisa ne wasu bata-gari suka kai masa hari suka soka masa wuka."

Kano: Yan sanda sun fara binciken kisan alaramma

SP Abdullahi ya tabbatar wa da jama’a cewa rundunar ‘yan sanda na ci gaba da gudanar da bincike don gano wadanda suka aikata wannan kisan gilla tare da daukar matakin shari'a.

Ya kara da cewa an kama wasu daga cikin wadanda ake zargi tare da dawakai hudu da ake amfani da su a wajen kilisar.

Ya ce:

"Ba ni da adadin wadanda aka kama, amma an kama wasu tare da dawakai hudu kuma suna hannun 'yan sanda."

Yan daba sun addabi mutanen Kano

A wani labarin, kun ji cewa mazauna Kano sun bayyana fargaba a kan yadda gungun yan daba suke kai masu farmaki tare da kwacen wayoyi, lamarin da ke kai ga kisan bayin Allah.

A ranar Lahadi, 11 ga watan Afrilu, 2025, an samu yan daba da suka mamaye Kofar Nasarawa da ke cikin birnin Kano, kuma sun kwace wayoyi tare da babur ba tare da fargabar kowa ba.

Wasu mazauna yankin sun bayyana mamakinsu ganin yadda ’yan daba ke aikata wannan laifi babu fagaba, duk da kasancewar ofishin ’yan sanda ba nisa da wajen ba da suka yi kwacen.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.