Mataimakiyar Kakakin Majalisar Dokoki Ta Kare Mutuncinta, Ta Yi Murabus daga Mukamin

Mataimakiyar Kakakin Majalisar Dokoki Ta Kare Mutuncinta, Ta Yi Murabus daga Mukamin

  • Hon. Maria Oligbi-Edeko ta yi murabus daga muƙaminta na mataimakiyar kakakin Majalisar Dokokin jihar Edo
  • Ƴar Majalisar ta tabbatar da ajiye muƙamin ne a wata wasika da ta miƙa wa Majalisar a zamanta na yau Litinin, 19 ga watan Mayu, 2025
  • Wannan mataki da ta ɗauka na da nasaba da yadda ƴan Majalisa suka fice daga PDP zuwa jam'iyyar APC mai mulki ciki har da kakaki

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Edo - Mataimakiyar Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Edo, Misis Maria Oligbi-Edeko, ta yi murabus daga mukaminta.

Ƴar Majalisa ta ajiye muƙaminta ne saboda kare mutuncin kanta a matsayinta na ƴar PDP bayan jam'iyyar APC ta zama mai rinjaye a Majalisar Dokokin.

Misis Maria Oligbi-Edeko.
Mataimakiyar kakakin Majalisar Dokokin Edo ta yi murabus daga muƙaminta Hoto: @MariaOligbiEdeko
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Hon. Oligbi-Edeko ta sanar da murabus dinta ne a zaman majalisar da aka gudanar a Benin City, babban birnin jihar, ranar Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin murabus din mataimakiyar kakaki

Murabus din Misis Maria Oligbi-Edeko, mai wakiltar mazaɓar Esan ta Arewa maso Gabas II na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan galibin mambobin majalisar sun koma APC.

Daga cikin waɗanda suka sauya sheka zuwa APC mai mulki har da kakakin Majalisar Dokokin jihar Edo, Hon. Blessing Agbebaku, rahoton Leadership.

A ƴan makonnin nan manyan ƴan siyasa da suka haɗa da gwamna, ƴan Majalisar Tarayya da na jiha sun bar jam'iyyunsu zuwa APC.

Hakan ya sa masana harkokin siyasa da ƴan adawa suka fara zargin gwamnatin Bola Tinubu da koƙarin maida Najeriya ƙasar da jam'iyya ɗaya ke mulki.

Tun farko dai an zaɓi Hon. Oligbi-Edeko a matsayin Mataimakiyar Kakakin majalisar dokonin Edo ta takwas a ranar 16 ga Yuni, 2023, kafin ta yi murabus.

Majalisa ta zaɓi sabon mataimakin kakaki

Bayan murabus din ta yau Litinin, majalisar ta zabi Hon. Osamwonyi Atu (APC Orhionmwon ta Gabas) a matsayin sabon mataimakin kakaki, bayan mambobi sun kada kuri’arsu tare da amincewa da shi.

A lokaci guda, Shugaban Majalisar, Hon. Jonathan Aigbokhan, ya gabatar da kudiri cewa a biya duk wasu hakkoki na ofishin mataimakin kakaki ga Oligbi-Edeko.

Misis Maria Oligbi-Edeko.
Dalilin da ya sa mataimakiyar kakakin Majalisar Edo ta yi murabus Hoto: Mrs. Maria Oligbi-Edeko
Asali: Twitter

Hon. Charity Airobarueghian, shugaban bangaren 'yan adawa, ta mara masa baya, kuma dukkan mambobi suka amince da kudirin ta hanyar kada kuri’ar murya.

A cikin wasikar da ta miƙawa majalisar, Oligbi-Edeko ta ce ta yi murabus ne ba don komai ba sai don tabbatar da adalci, daidaito, da kuma gaskiya ga dukkan mazabu.

Sai dai ta gode wa shugabanni da mambobin jam’iyyar PDP da suka ba ta dama har take wakilci mazabarta a majalisar dokokin Edo.

Kakakin Majalisar Edo ya kare komawarsa APC

A wani labarin, kun ji cewa Hon. Blessing Agbebaku ya ce ya fice daga PDP tare da shiga APC ne domin ci gaba da riƙe muƙamin shugaban majalisar dokokin jihar Edo.

Agbebaku ya bayyana cewa mutanen mazabarsa sun goyi bayan matakin da ya ɗauka na komawa jam'iyyar APC domin ci gabansu.

Tun farko, Blessing Agbebaku tare da wasu ƴan majalisa biyu, Hon. Sunday Fada Eigbiremonlen da Hon. Idaiye Yekini Oisayemoje, sun sauya sheƙa daga PDP zuwa APC a ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262