Babbar Magana: An Soke Tattaunawar da Aka Shirya tsakanin Amurka da Iran
- Shugaban Amurka, Donald Trump ya dakatar da tafiyar wakilansa zuwa birnin Islamabad, lamarin da ya soke zaman tattaunawa da Iran
- Trump ya bayyana cewa ya dauki wannan matakin ne saboda yadda ake ta kwan-gaba kwan-baya kan shirya zagaye na biyu na zaman sulhu
- Bayanai sun nuna cewa Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya bar birnin Islamabad bayan ganawa da jami'an Pakistan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
United States - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanar da soke tafiyar wakilansa zuwa birnin Islamabad na Pakistan domin ganawa da jami’an Iran a zagaye na biyu na tattaunawar zaman lafiya.
Wannan mataki na nufin Shugaba Trump ya soke tattaunawar, wacce ake tunanin za ta gudana a yau Asabar da zarar wakilan Amurka sun isa Islamabad.

Source: Getty Images
Dalilin soke tafiyar wakilan Amurka

Kara karanta wannan
Asiri ya tonu: An kama mai taimaka wa yan bindiga su samu kudi a Sakkwato, ya fara bayani
Trump ya bayyana hakan ne a wani sako da ya fitar yau Asabar, 25 ga watan Afrilu, 2026 inda ya ce an bata lokaci sosai kan shirye-shiryen tafiyar, kamar yadda NBC News ta rahoto.
“An bata lokaci mai yawa, ana ta kwan gaba kwan baya, akwai kuma aiki da yawa,” in ji shi.
Ya kuma zargi shugabannin Iran da rikice-rikice da rashin fahimtar juna, yana mai cewa har yanzu ba a san su waye ke jagorantar kasar ta Musulunci ba.
“Akwai babban sabani da rikici a cikin shugabanninsu. Babu wanda ya san wanda ke da iko, har da su kansu.
“Mu muke da duk wata dama, su kuma ba su da komai, idan suna son tattaunawa, sai su kira mu,” in ji shi.
Shugabar Majalisar Iran ya bar Islamabad
Wannan na zuwa ne bayan Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya bar Islamabad bayan ganawa da jami’an Pakistan ciki har da Firaminista Muhammad Shehbaz Sharif.
A wani sako da ya wallafa a X, Araghchi ya ce ziyararsa a Pakistan ta yi amfani, amma har yanzu Iran na duba ko Amurka na da niyyar yin gaskiya wajen tattaunawar ko akasin haka.

Source: Getty Images
An soke tattaunawar Amurka da Iran
Ana sa ran wakilan Amurka karkashin jagorancin Steve Witkoff da Jared Kushner su isa Pakistan domin tattaunawar, amma matakin Trump ya kawo cikas ga shirin.
Matakin soke tattaunawar na nuna karin dagulewar al’amura tsakanin kasashen biyu, yayin da ake ci gaba da kokarin nemo mafita ta siyasa kan rikicin da ke tsakaninsu.
Shugaba Trump ya bayyana cewa Amurka a shirye take, kuma ta bar kofarta a bude, duk lokacin da Iran ta shirya ta tuntube su.
Iran ta mika sabon tayi ga Amurka
A wani rahoton, kun ji cewa Shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa kasar Musulunci ta Iran ta gabatar da tayi da nufin cika sharuddan da ya shimfida.
Duk da bai yi cikakken bayani kan tayin na Iran ba, Shugaba Trump ya ce Amurka za ta yi nazari kafin ta dauki mataki na gaba.
Wannan kalamai na Trump na zuwa bayan kasar Iran ta kafa sharadin cewa ba za ta koma zagaye na biyu na tattaunawa da Amurka ba har sai an bude tashoshin ruwanta.
Asali: Legit.ng
