2027: Matasa a Kano Sun Yi Tattakin Nuna Goyon baya ga Kawu Sumaila da Tinubu
- An gudanar da tattaki a Kano domin nuna goyon baya ga Shugaba Bola Tinubu da Kawu Sumaila bayan sauya shekar Sanatan zuwa APC
- Sun bayyana cewa akwai hikima mai tarin yawa da Sanata Kawu ya gaggauta barin NNPP, ganin cewa za ta iya shan kaye a zaben 2027
- Sun kuma yadda da yadda shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya kawo manyan ayyukan ci gaba ga Arewacin Najeriya, musamman Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – An gudanar da tattakin nuna goyon baya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Abdulrahman Kawu Sumaila wanda ya sauya sheka zuwa APC a jihar Kano.
Sanata Kawu Sumaila, wanda ke wakiltar Kano ta Kudu, ya sauya sheka tare da magoya bayansa daga jam’iyyar NNPP bayan an dade ana kai ruwa rana kan batun.

Asali: Facebook
The Nation ta ruwaito cewa sauya shekar ta haifar da martani daga jagoran NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, wanda ya zarge shi da cin amanar jam’iyya da mutanen da suka zabe shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An yi tattakin goyon bayan Kawu da Tinubu
Magoya bayan jam’iyyar APC sun cika titunan karamar hukumar Sumaila domin gudanar da tattakin nuna goyon baya ga Kawu Sumaila da Shugaba Tinubu.
Kungiyoyi daban-daban ne suka halarci taron, ciki har da Waraka Scholars da Waraka TikTok Influencers, inda suka rike manyan kwalaye dauke da rubuce-rubuce nuna goyon baya.
Magoya bayan sun sanya riguna da hular kwano da aka yi musu kwalliya da hotunan Kawu Sumaila da Shugaba Tinubu.
2027: An gudanar da addu’o’i don Tinubu da Kawu
Hadimin Sanatan kan harkokin dalibai, Dr. Umar Ali, ya bayyana cewa Kawu babban dan siyasa ne mai tasiri a matakin tushe a Kano ta Kudu.
Ya ce:
“Dalilin wannan taro shi ne mu tabbatar da goyon bayanmu ga duk wani mataki da Sanatanmu ya dauka domin mara wa Shugaba Bola Tinubu baya.”
Wani jigo a APC, Ahmad Aliyu, ya bayyana cewa shugaba Tinubu ya yi abubuwa masu yawa ga Arewacin Najeriya da Kano, musamman yadda ya amince da biliyoyin Naira don gyaran dam-dam a fadin jihar.

Asali: Facebook
Ya bayyana cewa sauya shekar da Kawu Sumaila ya yi zuwa APC mataki ne cike da hikima, ganin yadda NNPP ke cikin rikici kuma tana fuskantar barazanar faduwa a zaben 2027.
Ahmad Aliyu ya ce:
“Sanata Kawu yana daga cikin wadanda suka kafa jam’iyyar APC. Abin takaici, wasu abubuwa da suka faru a 2023 ne suka sa ya koma NNPP, kuma hakan ya taimaka wajen samun nasarar NNPP a Kano.”
Kawu Sumaila ya koma jam'iyyar APC
A wani labarin, kun ji cewa Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu a Majalisar Dattawa, Abdurrahman Kawu Sumaila, ya tabbatar da ficewarsa daga jam’iyyar NNPP.
Sanata Kawu Sumaila ya fice daga jam’iyyar NNPP ne saboda ya samu damar cika muradun mutanen da suka wakilce shi, na kawo masu manyan ayyukan gwamnatin tarayya.
Sanatan ya bayyana cewa manufarsa a siyasa ba ta canza ba, don har yanzu yana da kishin ganin jama’arsa sun ci gaba, tare a alkawarin hada gwiwa da gwamnatin Kano.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng