Latest
Bayan shafe shekaru 20 yana jagorancin kamfanin sukari, Attajiri a Nahiyar Afirka gaba daya, Alhaji Aliko Dangote ya ajiye muƙaminsa a matsayin shugaba.
Wasu mahara sun kai hari kan bayin Allah a jihar Plateau. Miyagun maharan sun hallaka mutum hudu ciki har da wani jariri mai watanni 9 a duniya a yayin harin.
Kamfanin sufurim jiragen sama na Air India ya tabbatar da cewa jirginsa da ya tashi daga birnin Ahmedabad zuwa London Gatwick ya gamu da mummunan hatsari.
A labarin nan, za a ji cewa jama'a , musamman masu ƙananan sana'o'i sun fara kuka bayan aikin da TCN ke yi ya jawo masu matsalar wutar lantarki na tsawon kwanaki.
Ana fargabar sace Imam Sulaiman Idris da ke zama limamin Juma'a a karamar hukumar Maradun. An sace limamin ne yana aiki a cikin gonarsa a zamfara.
Wasu daga cikin jihohin Najeriya sun ba da tallafi ga Alhazansu da ke kasa mai tsarki. An ba da tallafin ne domin saukakawa Alhazan yayin gudanar da aikin Hajji.
Mai magana da yawun tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Paul Ibe ya ce alama ta nuna cewa haɗakar da Atiku ke jagoranta ta fara tsorata gwamnatin Bola Tinubu.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa rundunar sojojin OPFY sun hallaka shahararren shugaban 'yan ta'adda da abokansa a wani harin kwanton bauna da suka kai a Zamfara.
Wani malami a jami'ar Sule Lamido da ke Kafin Hausa a jihar Jigawa, Dr Zaidu Jibril ya lashe kyautar fassara ta duniya ta Sarki Abdallah bin Abdulaziz a Saudiyya
Masu zafi
Samu kari