White House: An Shiga Fargaba bayan Harbi a Kusa da Fadar Shugaba Trump
- Wani harbin bindiga da aka yi a kan wasu manyan tituna a birin Washington D.C ya sa an kulle Fadar White House cikin gaggawa a ranar Litinin
- ‘Yan jarida da ke wurin sun ruwaito cewa harbin ya faru ne mintuna kadan kafin Shugaba Donald Trump ya gudanar da taron manema labarai
- Wata 'yar jarida ta ce jami’an leken asirin Amurka sun harbi wani mutum da suka yi zargin yana dauke da bindiga a kusa da White House kafin taron
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Rundunar leken asirin Amurka ta harbi wani mutum mai dauke da makami da ke da alaka da wani harbi da aka yi kusa da fadar shugaba Donald Trump ta White House.
Rahotanni sun nuna cewa jami'an leken asirin sun gargadi jama’a da su guji zuwa yankin White House yayin da jami’an agajin gaggawa ke aiki a wurin.

Source: Getty Images
An yi harbi a kusa da fadar White House
A cikin wani sako da ta wallafa a shafin X, ofishin hulda da jama’a na hukumar leken asirin Amurka ya tabatar da harbin da aka yi a kusa da White House:
Ta ce:
“Jami’an leken asiri na wurin da aka yi harbi a Washington, DC. An harbi mutum daya; ba a san halin da yake ciki ba a yanzu.
"Don Allah ku guji yankin yayin da jami’an agaji ke gudanar da aikinsu.”
Wasu rahotanni sun nuna cewa na kulle fadar White House a lokacin da ake tsananta bincike bayan harbin da aka yi.
Karin bayani kan harbin Amurka
A wani taron manema labarai, jami'in leken asiri, Matt Quinn ya ce wani karamin yaro da ke wurin ya jikkata a yayin lamarin.
Gulf News ta rahoto ya ce:
“Wadannan jami’ai sun samu horo kan gano barazana, suna aiki kowace rana domin gano irin wannan... kuma sun ga alamar bindiga.”
Ya kara da cewa:
“Bayan sun tuntubi mutumin, ya yi kokarin guduwa na dan lokaci, sannan ya ciro bindiga ya fara harbi zuwa ga jami’anmu. Su ma sun mayar da martani da harbi.”

Source: Getty Images
Wanda ake zargi yana raye
Quinn ya tabbatar da cewa yaron da aka harba bai samu rauni mai barazana ga rayuwa ba kuma ana masa magani a asibiti.
Ya kuma bayyana cewa tawagar motocin mataimakin shugaban kasa JD Vance ta wuce yankin kadan kafin harbin, amma ya ce babu alaka tsakanin abubuwan biyu.
Da aka tambaye shi ko wanda ake zargi na iya nufar Shugaba Trump, Quinn ya ki yin bayani.
“Ba zan iya cewa ba—ba zan yi hasashe ba,”
In ji shi.
Iran ta farmaki jirgin Amurka
A wani labarin, mun kawo muku cewa rundunar sojin Iran ta sanar da cewa ta farmaki wani jirgin ruwan Amurka da ya zo zai wuce ta Hormuz.
Hakan na zuwa ne bayan Iran ta tsaurara matakan tsaro da sa-ido tun bayan da Donald Trump ya ce zai rika raka jirage su wuce ta wajen.
Biyo bayan harin, rundunar sojin Amurka ta fitar da sanarwa tana cewa babu wani jirginta da aka kai wa hari a mashigar Hormuz a ranar Litinin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


