Gwamna Radda Ya Cika Burin Shekaru 30, Ya Kaddamar da Makaranta Ta Musamman a Katsina
- Gwamna Dikko Radda na jihar Katsina ya ƙaddamar da wata makarantar sakandare ta zamani, wanda hakan ya cika burinsa na shekaru 30
- Makarantar, wacce aka kaddamar a garin Radda, ita ce ta farko a cikin makarantu uku na musamman da gwamnan ke shirin ginawa a shiyyoyin jihar
- Shugaban ƙungiyar gwamnonin Najeriya, AbdulRahman AbdulRazaq, da kuma ministan ilimi, Tunji Alausa, ne suka jagoraci buɗe makarantar
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya cika burinsa na fiye da shekaru 30, yayin da ya kaddamar da makarantar sakandare ta zamani, kuma ta musamman a garin Radda.
Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya kuma gwamnan Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, da ministan ilimi, Ma’auuf Tunji Alausa ne suka jagoraci ƙaddamar da makarantar a rana Talata, 5 ga Mayun 2026.

Kara karanta wannan
An rantsar da mataimakin gwamnan Kano, Murtala Sule Garo, manyan jiga jigai sun halarta

Source: Facebook
Radda ya kaddamar da makaranta ta musamman
Rahoton jaridar Tribune ya nuna cewa, sabuwar makarantar ita ce ta farko daga cikin makarantu uku na zamani da ake shirin kafawa a kowane yanki na jihar Katsina.
Da yake jawabi a taron kaddamar da makarantar, Dikko Radda ya ce:
"A yau, ba ina tsaye gabanku a matsayin gwamna da ke jawabi ba. Ina tsaye a gabanku a matsayin mutumin da zai cika alkawarin da ya dauka.
"Wannan makarantar da muka kaddamar, ita ce ta farko a cikin guda uku da za mu gina. Wannan mafari ce kawai, akwai wasu na zuwa."
Gwamnan ya ce an samar da makarantar sakandare ta 'RMSS' domin ba yara a fadin jihar Katsina dama iri daya, ba tare da la'akari da gari, kabila, ko wani bambanci ba, wanda ke da nufin samar da kyakkyawar makoma ga yara.
Yadda aka samar da makarantar ta musamman
A cewarsa, sai da aka tankade aka rairaye sannan aka zakulo zakaruran yara 1,000 aka ba su gurbin karatu a wannan makaranta domin samun ilimi na musamman.

Kara karanta wannan
Matar da APC ta tsaida takara a Katsina ta fara fuskantar cikas daga malaman Musulunci
Dikko Radda ya ce an samar da azuzuwa na zamani, dakunan gwaje gwajen kimiyya, dakin karatu, kayayyakin motsa jiki da kuma gidajen malamai, duk don ganin an samar da ingantaccen ilimi.
Ya kara da cewa makarantar za ta mayar da hankali kan kunsa ilimin kimiyya da fasaha a kwakwalwar yara, ciki har da fasahar AI da sauran ilimummuka da ke tashe yanzu.
Baya ga ilimi, gwamnan ya ce makarantar za ta karfafi dalibai ta fuskar fasahohin zamani, wasanni, kasuwanci da kuma tabbatar da cewa sun rika yin tunani na ci gaban kansu da al'ummarsu.

Source: Facebook
Jawabin Gwamna AbdulRazaq da minista
A jawabinsa, Gwamna AbdulRazaq ya bayyana aikin a matsayin wata muhimmiyar dabara ta rage gibin da aka daɗe ana fama da shi wajen samun ingantaccen ilimi, in ji rahoton jaridar Independent.
Ya jaddada cewa bai kamata a hana kowane yaro damar cimma burinsa ba saboda ƙarancin kuɗi, tare da dora yakini cewa gwamnatin jihar Katsina za ta samar da dama iri ɗaya ga kowa.
Shi kuma Ministan ilimi, Dr. Ma’auuf Tunji Alaisa, ya yaba wa Gwamnatin jihar Katsina bisa wannan hangen nesa na zuba jari a ci gaban ɗan Adam.
Ya jaddada cewa cewa ire iren waɗannan makarantu suna kan tafarki iri daya da manufofin gwamnatin tarayya na ƙarfafa ilimin firamare da sakandare.
Ministan ya ƙara da cewa irin wannan tsari zai taimaka wajen gina shugabanni na-gari da kuma haɓaka ci gaban ƙasa ta hanyar ingantaccen ilimi.
Alkawarin wakilan yankin Radda ga gwamna
Kwamishinan ilimin bai daya na jihar Katsina, Alh Yusuf Sulaiman Jibiya, ya bayyana aikin a matsayin wata babbar nasara a cikin shirin gyaran ilimi na gwamnatin Dikko Radda.
Ya ce makarantar ta kafa sabon ma’auni ga ilimin gwamnati a jihar, inda aka haɗa ingantattun gine-gine, fasaha, da ƙwararrun malamai domin samar da ilimi mai inganci da zai iya gogayya a duniya.

Source: Facebook
Wakilan al’ummar yankin ciki hadda Hakimin Radda, Gwagwaren Katsina, Alh Muhammad Dikko Radda sun bayyana godiyarsu ga gwamnatin jihar bisa zaɓar yankin domin gina makarantar.
Sun kuma yi alƙawarin ba da cikakken goyon baya wajen kare makarantar da samar da yanayi mai kyau ga dalibai da malamai.
Kalli hotunan sabuwar makarantar da aka kaddamar a kasa, wanda Umar Muhammad Abdullahi ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Katsina: Malamai sun fara karbar N70, 000
A wani labari, mun ruwaito cewa, ma'aikatan gwamnati a jihar Katsina sun fara karɓan sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000.
Tun farko dai Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa ya yi alkawarin fara biyan sabon albashin a watan Disamba, 2024 bayan cimma matsaya da ƴan kwadago.
Malam Dikko Radda ya cika alkawarin da ya ɗauka na fara biyan sabon albashin, inda aka tabbatar da cewa malaman makaranta sun samu sama da N70,000.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

