Ranar Dimokuraɗiyya: An Tsaurara Tsaro, Ana Jiran Tinubu Ya Isa Majalisar Tarayya
- Shirye-shirye sun yi nisa a majalisar dokokin Najeriya yayin da ake jiran shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu
- An tura jami’an DSS, ’yan sanda da NSCDC domin tabbatar da tsaro yayin da shugaban kasa Tinubu ke shirin gabatar da jawabi
- Rahotanni sun ce tun da asubar fari aka keɓe hanyar shiga majalisar, kuma ba a barin kowa ya doshi hanyar sai wanda aka tantance
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Majalisar kasar nan ta cika da jami’ai da na’urorin tsaro na zamani a safiyar yau, Alhamis, 12 ga Yuni, 2025, yayin da ake shirin tarbar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Shugaban kasa Tinubu na shirin gabatar da jawabinsa ga zaman hadin gwiwa na Majalisar Dattawa da ta Wakilai da 12:00 na rana a wani bangare na bikin ranar dimokuraɗiyya.

Asali: Twitter
The Guardian ta wallafa cewa wannan na zuwa ne bayan gwamnatin ta sanar da janye jawabin da shugaban kasa ke gabatarwa da 7.00 na.s a kowace ranar dimokuraɗiyya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana jiran shugaba Bola Tinubu a majalisa
Daily Nigerian ta ruwaito cewa jami’an tsaro daga sassa daban-daban, har da DSS, ’Yan sanda da NSCDC, sun mamaye kofa da titunan da ke zagaye da majalisar tun kafin asuba.
Tun daga 7.30 na safe, aka fara tantance mutane da motocinsu cikin tsanaki, yayin da aka killace hanyoyin shiga majalisar.

Asali: Facebook
An gano cewa sai wadanda suka samu izini na musamman ne ake barin su shiga, daga ciki har da ma’aikata, ’yan jarida da jami’an tsaro da ke kan aiki.
Yadda aka soke jawabin Tinubu
Tun da farko, an tsara shugaban kasa zai yi jawabi ta talabijin da 7.00 na safe, amma daga bisani aka soke shi domin mayar da jawabin kai tsaye daga majalisar.
A wata sanarwa daga shugaban sashen yada labarai da hulda da jama’a na fadar shugaban kasa, an bayyana cewa:
"Saboda shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu GCFR zai halarci zaman hadin gwiwa na majalisar dokoki, an soke jawabin Talabijin da aka tsara a ranar 12 ga Yuni
"Shugaban kasa zai gabatar da jawabinsa daga majalisar dokoki, sauran shirye-shirye kuwa na nan kamar yadda aka sanar tun da fari.”
Bikin ranar Dimokuradiyya na shekarar 2025 ya zo da taken: “Ci gaba da amfana daga dimokuradiyyar Najeriya: Bukatar gyare-gyare mI dorewa.” Wannan shi ne karo na 26 da Najeriya ke gudanar da dimokuradiyya ba tare da katsewa ba tun bayan komawar mulki daga sojoji a shekarar 1999.
An roki Tinubu ya maido Fubara ofis
A wani labarin, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa daga yankin Kudu maso Yamma, Cif Bode George, ya miƙa ƙoƙon bara ga Bola Tinubu.
Ya ce kamata ya yi Shugaban kasar ya yi hakuri, ya yafewa gwamnan Ribas, ya mayar da Siminalayi Fubara kujerarsa ta gwamna bayan an dakatar da shi. Bode George ya bayyana hakan ne a cikin wata wasika da ya aikawa shugaban kasa a gabanin bikin ranar Dimokuraɗiyya ta bana, a ranar 12 ga Yuni, 2025.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng