An Cafke Matar Babban Alkali a Sokoto, Ana Zargin Ta Ci Zarafin Karamar Yarinya

An Cafke Matar Babban Alkali a Sokoto, Ana Zargin Ta Ci Zarafin Karamar Yarinya

  • Rundunar ƴan sandan Sokoto ta tabbatar da kama Fauziya Rabo bisa zargin cin zarafin ma'aikaciyar gidanta, Bashariyya Usman
  • Rundunar ta fara gudanar da bincike kuma ta ce za ta yi wa kowane ɓangare adalci, bayan ta yi Allah-wadai da cin zarafin yara
  • Lauyan kare ɗan adam, Abba Hikima, ya lissafa zarge-zargen da ake yi wa Fauziyya da suka haɗa da jikkatata Bashariyya da cin zarafinta

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Sokoto - Rundunar ƴan sandan jihar Sokoto ta tabbatar da kama wata Fauziya Rabo bisa zargin cin zarafin ma'aikaciyar gidanta, Bashariyya Usman.

Rahoto ya nuna cewa Fauziyya Muhammad Rabo, wacce aka fi sani da Maman Rauda ta kasance matar wani babban alkali, mai suna Abubakar Zaki Tambuwal.

Rundunar 'yan sanda ta cafke Fauziyya Rabo da ake zargi da cin zarafin 'yar aikinta Bashariyya.
Babban Sufetan rundunar 'yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun. Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

An cafke matar alkali kan zargin cin zarafi

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Sokoto, DSP Ahmad Rufai ne ya tabbatar da kama Fauziyya Rabo a sanarwar da ya fitar ranar Laraba, inji rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin sanarwar, rundunar ƴan sandan ta bayyana cewa wani ƙorafi da aka shigar a hukumance ne ya sanya aka ɗauki matakin gaggawa, wanda ya kai ga kama Fauziyya.

Ko kafin a kama Maman Rauda, kafofin sada zumunta sun dauki zafi sosai bayan da aka samu bullar bidiyo da hotuna na irin cin zarafin da ake zargin ta yi wa 'yar aikinta, Bashariyya.

Bayan kamata da aka yi, rundunar 'yan sandan Sokoto ta tabbatar wa jama'a cewa ana gudanar da cikakken bincike kan lamarin, kuma za a yi wa kowanne bangari adalci.

'Yan sanda za su yi bincike na adalci

Sanarwar DSP Ahmad ta bayyana cewa:

"Rundunar ƴan sandan jihar Sokoto ta yi Allah-wadai da duk wani nau'i na cin zarafi ko tashin hankali a cikin gidaje.

"Za a gudanar da bincike mai cike da adalci bisa doron doka, kuma za a yi wa dukkanin ɓangarorin da abin ya shafa adalci, ba tare da nuna bambanci ko son kai ba."

Yayin da take kira ga jama'a da su guji yaɗa bayanan da ba a tabbatar da su ba, rundunar ta sake nanata jajircewar ta ga gaskiya kuma ta yi alƙawarin ci gaba da sanar da jama'a halin da ake ciki.

Sanarwar ta ƙara da cewa kwamishinan ƴan sandan Sokoto, Ahmed Musa, ya sake nanata jajircewar rundunar wajen kare haƙƙin ɗan adam da aiwatar da dokokin da ke kare mutunci da lafiyar dukkan mazauna jihar.

Abba Hikima, 'Dan Bello sun magantu

Lauyan da ke rajin kare hakkin dan Adam kuma wanda ke bibiyar wannan lamari, Abba Hikima, ya tabbatar da kama Fauziyya a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

A cikin sakon, Abba Hikima ya ce:

"Fauziyya Rabo Sokoto tana hannun ‘ƴan sanda yanzu saboda zargin jikkata mutum da gangan, cin zarafin yara, cin zarafi ta fuskar tunani, yaudara, aikata munanan al’adun gargajiya, da kuma sanya rayuwar Bashariya Usman cikin haɗari."

Shi ma dan jaridar nan na kasa da kasa mai rajin kare hakkin wanda aka zalunta, Bello Galadanci da aka fi sani da Dan Bello, ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa:

"‘Yan Sanda sun kama kuma sun rufe Fauziyya, matar da ake zargi ta azabtar da Bashariyya. Masha Allah, yanzu saura mu tabbatar gwannati ba ta saka hannu an yi rashin adalci an fito da ita ba"
Abba Hikima ya bayyana zarge-zargen da ake yi wa Fauziyya da suka hada da cin zarafi, da sauransu
Lauyan da ke kare hakkin dan Adam, Abba Hikima. Hoto: Abba Hikima
Asali: Facebook

Su wa suka shigar da korafi kan Fauziyya Rabo

A wata sanarwa da boyayyen dan sanda, kuma mai rajin kare hakkin dan Adam, Datti Assalafiy ya wallafa a shafinsa na Facebook, an fahimci cewa Abba Hikima ne ya shigar da korafi ga 'yan sanda kan zargin da ake yi wa Fauziyya.

A tare da sanarwar, Datti Assalafiy ya wlalafa hotunan takardar korafin, wacce ke dauke da sunan mahaifin Bashariyya, Malam Usman Aliyu, a matsayin wanda ya ba Abba Hikima izinin shigar da korafin.

A cikin takardar, lauyan ya bukaci rundunar 'yan sandan Sokoto da ta tuhumi Fauziyya Rabo kan karbo Bashariyya tare da ajiye ta a gidanta da zummar za ta rika yi mata aikatau.

Sai dai, a cewar takardar korafin, Fauziyya ta kasance tana azabtar da Bashariyya, ciki har da duka, hana ta abinci, kulle ta a daki, da sauransu.

Hakazalika, Abba Hikima ya shaidawa rundunar cewa suna da hujjoji na hoto da bidiyo da suka nuna irin munanan raunuka da Fauziyya ta ji wa Bashariyya, harda tabon wuta, duka da sauransu.

'Yar aiki ta kashe dan masu gida

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wata mai aiki 'yar shekara 11 a jihar Legas ta daba wa yaro dan shekara biyar da take kula da shi wuka har lahira.

An ce 'yar aikin, Ojiugo Ifechukwu Duru, ta hallaka yaron da gangan, jim kadan bayan mahaifiyar yaron ta tafi ta bar ta da shi da kannensa a gidan.

Makwbta sun yi gaggawar kiran matar jim kadan da fitar ta, tare da bukatar ta dawo gida, inda aka ce ta zo ta tarar da cewa mai aikinta ta kashe ɗanta na fari.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.