NNPCL: Kamfanoni 2 daga kasar China Za Su Shiga Harkokin Gudanar da Matatun Najeriya

NNPCL: Kamfanoni 2 daga kasar China Za Su Shiga Harkokin Gudanar da Matatun Najeriya

  • Kamfanoni biyu daga kasar China za su shiga cikin masu tafiyar da harkokin matatun man gwamnatin Najeriya da ke Fatakwal da Warri
  • Hakan dai na zuwa ne bayan kamfanin mai na kasa (NNPCL) ya kulla yarjejeniya da kamfanonin domin gyara da fadada matatun guda biyu
  • Shugaban kamfanin NNPCL na Najeriya, Bayo Ojulari ne ya jagoranci rattaba hannu kan yarjejeniyar a birnin birnin Jiaxing na kasar China

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja – Kamfanin mai na kasa (NNPC Ltd), ya kulla yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) da wasu kamfanonin kasar China biyu domin sake farfado da matatun mai na Warri da Fatakwal.

Kamfanonin China da NNPCL ya kulla yarjejeniya da su sune Sanjiang Chemical Company Limited da Xingcheng (Fuzhou) Industrial Park Operation and Management Co. Ltd.

NNPCL.
Shugaban kamfanin NNPCL, Bashir Bayo Ojulari tare da wakilan kamfanonin China 2 lokacin sanya hannu kan yarjejeniyar gyara matatun Najeriya Hoto: @NNPClimited
Source: Twitter

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na kamfanin NNPCL, Andy Odey ya rattaba wa hannu kuma aka wallafa a shafin X.

Kara karanta wannan

Yaki na shirin dawowa: An zargi Iran ta harba makamai masu linzami UAE

Manufar yarjejeniyar da NNPCL ya kulla

Andy Odey ya bayyana cewa yarjejeniyar za ta bude hanya ga hadin gwiwar fasaha da zuba jari domin kammala gyaran matatun da kuma tabbatar da an yi ingantaccen aiki, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

An rattaba hannu kan yarjejeniyar ne a birnin Jiaxing na kasar China a ranar 30 ga Afrilu, 2026, inda shugaban NNPCL, Bashir Bayo Ojulari, ya sanya hannu tare da shugabannin kamfanonin China.

A karkashin shirin, kamfanonin China za su taimaka wajen kammala gyaran da ake yi a matatun biyu, tare da shiga harkar tafiyar da su domin tabbatar da dorewar aiki.

Haka kuma, za a yi kokarin fadada matatun da inganta su domin samar da man fetur mai tsafta, kara riba da bunkasa samar da kayayyaki.

Yarjejeniyar za ta kuma taimaka wajen samar da cibiyoyin masana’antu masu amfani da iskar gas a kusa da matatun.

Bayani daga kamfanin NNPC

Bayo Ojulari ya bayyana yarjejeniyar a matsayin babban mataki bayan watanni na tattaunawa, yana mai cewa bangarorin sun fahimci amfani da za su samu daga hadin gwiwar.

Kara karanta wannan

Atiku da shugabannin ADC sun fara shirin bin Kwankwaso zuwa NDC? Gaskiya ta fito

Ya kara da cewa yarjejeniyar na daga cikin kokarin nemo kwararrun abokan hulda domin gyara da fadada matatun mai na kasar nan

Duk da haka, ya bayyana cewa yarjejeniyar ba ta da cikakken karfi a yanzu, domin tana bukatar amincewar hukumomin Najeriya da karin tattaunawa.

Shugaban NNPCL.
Shugaban kamfanin mai na Najeriya, Bayo Ojulari yana magana a wurin taro a Abuja Hoto: @NNPClimited
Source: UGC

Yadda ake kokarin farfado da matatun

Idan ba ku manta ba, an amince da gyaran matatar Fatakwal tun 2021 tare da ware kudin da ya kai Dala biliyan 1.5, yayin da ake gyaran matatar Warri da kusan Dala miliyan 897.

Wadannan shirye-shirye na daga cikin kokarin rage dogaro da shigo da man fetur daga kasashen waje.

Matatar Fatakwal ta dawo ta fara aiki a karshen 2024 bayan shekaru, amma daga baya aka sake rufe ta saboda matsalolin aiki da na kudi.

NNPCL ya fara sayar da kayan matatun mai?

A wani labarin, kun ji cewa kamfanin mai na kasa, NNPCL ya yi bayani game da rahotannin da ke cewa an fara sayar da ƙarafa da sauran tarkacen matatun Najeriya.

NNPCL ya yi kira ga jama’a da su yi hattara da wasu bayanai da ke yawo, wadanda ke ikirarin cewa yana sayar da tarkacen matatun mai da wasu kayan aiki ga mutane.

Kamfanin ya kara da cewa bai amince da sayar da wani abu daga rumbu nan ajiya ko kayan aikin matatun kasar nan da ke jihohin Kaduna da Fatakwal ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262