"Ana Ta Asara," Rashin Wuta Ya Jawo Matsala a Jihohin Arewa maso Gabas
- Mazauna jihohin Arewa maso Gabas guda shida sun shiga tsaka mai wuya sakamakon katse masu wutar lantarki
- Tun da fari, kamafanin rarraba hasken wutar lantarki na TCN ya sanar da cewa zai yi aikin sanya sababbin turakun wuta
- Amma tsananin rashin ya fara ƙoƙarin durkusar da kananan sana'o'i, musamman wadanda suka dogara da samar da wuta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Adamawa – Jama’a da yan kasuwa a yankin Arewa maso Gabas na kokawa da asarar da suka tafka sakamakon matsanancin rashin wuta da yankin ke fama da shi.
Wannan rashin wuta ya samo asali ne daga aikin gina sababbin turakun lantarki na 330kV a sabon matattarar wutar lantarki ta Bauchi.

Asali: Getty Images
Kamfanin wuta na ƙasa (TCN) ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa ya sanar da kamfanonin rarraba wuta (DisCos) da ke aiki a jihohin shida na Arewa maso Gabas cewa za a samu yankewar wuta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce za a samu yankewar wuta a wasu wurare, yayin da wasu kuma za su fuskanci karancin wutar lantarki daga ranar 10 zuwa 14 ga Yuni, 2025.
Jama'a suna kuka da rashin wutar lantarki
Daily Trust ta ruwaito cewa wannan yankewar wutar ta shafi layin wutar Jos-Bauchi-Gombe na 132kV, kuma ya janyo damuwa a tsakanin mazauna yankin,.
Inda lamarin ya yi muni sun hada da Yola, babban birnin jihar Adamawa, inda mutane ke kokawa da yadda nama da suka yanka a Sallah ke lalacewa.

Asali: Original
Hajiya Aisha Babangida, wata mazauniyar Jimeta ce a Adamawa, ta ce:
“Ragon da muka yanka a Sallah ba a iya sanya shi a firji ba saboda rashin wutar da muke fama da shi.”
Rashin wuta ya jawo wa 'yan kasuwa asara
Adamu Abubakar, wani mai sayar da lemun kwalba a kasuwar Jimeta, ya ce sana’arsa ta fara tangal-tangal saboda yanayin zafi da kuma ruwan sanyi da ba ya samuwa. A cewarsa:
“Mutane ba sa saye kamar da saboda babu sanyi. Yanzu haka na fara shirin siyan kankara domin ci gaba da kasuwanci.”
Shi ma Muhammad Zaharaddeen, wani mai aski a jihar Bauchi, ya ce:
“Sana’armu da ke dogara da wutar lantarki ta kusa durkushewa. A yanzu ba ma samun kwastomomi kamar da saboda rashin wuta.”
Rashin wutar da ake fama da shi ya zo ne bayan bukukuwan Sallah, kuma yana ci gaba da shafar gidaje da sana’o’in jama’a a yankin.
An dauke wuta na kwanaki 4 a jihohi
A wani labarin, kun ji cewa huumar samar da wutar lantarki (TCN) ta sanar da cewa za a samu daukewar wutar lantarki na tsawon kwanaki biyar a jere a wasu jihohin Arewa maso Gabas.
A cewar wata sanarwa da kamfanin TCN ya fitar, ya kara da bayyana cewa za a dauke wutar ne domin kafa sababbin turakun wutar lantarki masu karfin 330kV.
TCN ya ce wannan aikin zai haifar da matsala a rarraba wuta a sassan Bauchi, Gombe, Ashaka, Savannah, Damaturu/Potiskum da Biu, sai kuma Yola da Jalingo.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng