2027: 'Gwamnatin Tinubu Ta Fara Tsorata da Shirin Haɗakar Atiku, Peter Obi da El Rufai'

2027: 'Gwamnatin Tinubu Ta Fara Tsorata da Shirin Haɗakar Atiku, Peter Obi da El Rufai'

  • Hadimin Atiku Abubakar ya ce alamu sun nuna gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta tsorata da shirin haɗakar ƴan adawa a 2027
  • Paul Ibe, mai magana da yawun Atiku ya ce gwamnatin APC mai ci ta gaza, ta fi maida hankali kan neman tazarce maimakon sauke hakkin ƴan ƙasa
  • Ya ce lokaci ya yi da ƴan Najeriya za su haɗu wuri ɗaya, su tabbatar da burinsu na neman canji ya zama gaskiya a zaɓen 2027

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Paul Ibe, mai magana da yawun tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta firgita da shirin ƴan adawa.

Mista Ibe ya yi ikirarin cewa ga dukkan alamu gwamnatin Tinubu ta fara jin tsoron yuwuwar haɗakar jam’iyyun adawa da nufin kifar da ita a zaɓen 2027.

Paul Ibe tare da Atiku Abubakar.
Hadimin Atiku ya ce Gwamnatin Tinubu na tsoron ƙawancen jam’iyyun Adawa a 2027 Hoto: @Atiku
Asali: Twitter

Hadimin Atiku ya faɗi haka ne a wata hira da aka yi da shi a shirin Siyasa a Yau na Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alamar da ke nuna gwamnatin Tinubu ta tsorata

Ibe ya ce yadda ministan Abuja, Nyesom Wike, ke sukar ƙoƙarin ƙawancen jam’iyyun adawa a bainar jama’a, alama ce da ke nuna cewa gwamnatin na cikin fargaba.

A cewarsa:

“'Yan Najeriya sun maida hankali a kan neman canji. Ranar farin ciki na nan tafe amma sai mun yi aiki tuƙuru don cimma hakan, kuma wannan aiki zai fara ne da tabbatar da cewa an kawar da wannan gwamnati a 2027.”

Ya jaddada cewa haɗin kan jam’iyyun adawa shi ne kaɗai hanyar da ta rage don cimma wannan buri.

“Duk surutun da ake yi cewa wannan ƙawance ba zai yi aiki ba, ya nuna cewa sun tsorata ne. Idan ba tsoronsa suke yi ba, me yasa ya zama babban batu a bakunan su?”

Hadimin Atiku ya soki Gwamnatin Tinubu

Da aka tambaye shi yadda yake kallon gwamnatin Tinubu bayan kusan shekaru biyu, Ibe ya bayyana ta a matsayin “gwamnatin da ta gaza ta kowane fanni."

Ya ce gwamnatin Tinubu ta fi maida hankali kan yadda za ta sake lashe zaɓe a 2027 maimakon kokarin kyautata rayuwar waɗanda take mulka, rahoton Vanguard.

Shugaba Tinubu da Atiku Abubakar.
Paul Ibe ya bayyana gwamnatin Tinubu a matsayin wacce ta gaza Hoto: @OfficialABAT, Atiku Abubakar
Asali: Facebook
“Komai ya koma kan 2027. Gwamnatin nan ta mayar da hankali wajen kamfe, ba ruwanta da batun yi wa jama'a aiki.
"Ya kamata a ce su maida hankali wajen kyautata rayuwar 'yan kasa, su sauƙaƙa farashin abinci, su samar da tsaro, wanda shi ne babban nauyin da ke kan kowace gwamnati.”

- Inji Paul Ibe.

Dangane da alkawarin gwamnatin Tinubu cewa wahalhalun da ake ciki za su wuce, Ibe ya ce babu wata alamar sauyi ko sauƙi da ke bayyana shekaru biyu da kafa gwamnati.

'Atiku, Obi da El-Rufai za su iya kayar da Tinubu'

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon ɗan takarar gwamnan Adamawa, Umar Arɗo ya ce matuƙar ƴan adawa suka kafa sabuwar jam'iyya, za su iya kayar da Tinubu a 2027.

Dr. Arɗo ya bayyana cewa kafa sabuwar jam'iyya ita ce mafita idan har ƴan haɗakar suna son samun nasara a babban zaɓen 2027.

Ya yi watsi da ra’ayin haɗaka ta shiga wata jam'iyya, yana mai jaddada cewa kafa sabuwar jam’iyya ce za ta ba ƴan adawa damar karɓar mulki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262