'Yan Bindiga Masu Garkuwa da Mutane Sun Sace Limamin Juma'a a Zamfara

'Yan Bindiga Masu Garkuwa da Mutane Sun Sace Limamin Juma'a a Zamfara

  • An fargabar ‘yan bindiga sun sace babban limamin masallacin Juma’a na Faru, Imam Sulaiman Idris da ke karamar hukumar Maradun a jihar Zamfara
  • Rahotanni sun nuna cewa an kama limamin ne da safiyar Laraba yayin da yake aiki a gonarsa, kuma har yanzu ba a san inda yake ba
  • Wani rahoto ya nuna cewa mazauna garin sun bayyana fargaba da fushi, suna kira ga hukumomin tsaro da su dauki mataki cikin gaggawa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Zamfara - Rahotanni daga jihar Zamfara na nuni da cewa ana fargabar ‘yan bindiga sun sace babban limamin masallacin Juma’a na Faru da ke karamar hukumar Maradun.

An ce an sace Sheikh Sulaiman Idris Faru da safiyar ranar Laraba yayin da limamin ke aikin gona a kusa da kauyen Faru, inda wasu gungun masu bindiga suka kuma yi awon gaba da shi.

An sace limami a Zamfara
Ana zargin 'yan bindiga sun sace limami a Zamfara. Hoto: @DanKatsina50
Asali: Twitter

Lamarin da wani mai amfani da dandalin X mai suna @DanKatsina50 ya fara bayyana wa jama’a, ya girgiza al’ummar yankin da ke fama da matsanancin rashin tsaro da yawan hare-hare.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An sace limamin Juma'a a gonarsa a Zamfara

Shaidun gani da ido sun ce Imam Sulaiman yana cikin gonarsa yana aikin noma lokacin da wasu mutane dauke da makamai suka iso da babura, suka sace shi ba tare da wata takaddama ba.

Kamar yadda rahotanni suka nuna, har zuwa yanzu babu wata kungiyar da ta dauki alhakin sace shi, haka kuma ba a tabbatar da ko an tuntubi iyalansa ko kuma an bukaci kudin fansa ba.

An bayyana cewa 'yan bindiga sun saba satar mutane domin neman kudin fansa a kauyukan jihar Zamfara da dama.

Al’umma na cikin fargaba kan sace limami

Daily Post ta wallafa cewa mazauna yankin Faru da ke Maradun sun bayyana fargaba da takaici kan yadda ‘yan bindiga ke kai farmaki a kan manyan mutane da malamai a cikin al’umma.

Wasu sun bayyana cewa irin wadannan hare-hare na nuna yadda tsaro ke kara tabarbarewa a yankin, kuma babu wata mafita face gwamnati da hukumomin tsaro su dauki matakin gaggawa.

Babu sanarwa daga gwamnati har yanzu

Gwamnatin jihar Zamfara ba ta fitar da wata sanarwa ba kan sace limamin, kuma hukumomin tsaro ba su bayyana matakin da suka dauka ba a hukumance.

Jihar Zamfara na daya daga cikin jihohin da suka fi fama da matsalar ‘yan bindiga a Arewa maso Yammacin Najeriya.

Ana jiran bayani daga jami'an tsaro kan sace limami a Zamfara.
Ana jiran bayani daga jami'an tsaro kan sace limami a Zamfara. Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Al’ummarta sun dade suna korafi kan hare-haren da ake kai musu a kauyuka, makarantu, masallatai da gonaki ba tare da tsayawa ba.

An kama wani dan China da ya shigo Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa dakarun sojin Najeriya sun kama wani dan kasar China da ya shigo Najeriya daga kasar Chadi.

Bayan jita jitar cewa mutumin na da alaka da 'yan ta'adda, an bayyana cewa ba shi da alaka da kungiyar Boko Haram ko wasu 'yan bindiga.

Sai dai duk da haka, hukumomi sun bayyana cewa mutumin ya shigo Najeriya ne domin hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng