'Yan Bindiga Sun Harbe Babban Malamin Addinin Musulunci, Ya Mutu nan Take a Pakistan
- 'Yan bindiga sun harbe Sheikh-ul-Hadith Maulana Muhammad Idrees har lahira a lardin Khyber Pakhtunkhwa na ƙasar Pakistan
- An kashe Maulana Idrees, wanda babban malamin addini ne kuma shugaban jam'iyyar Jamiat Ulema-e-Islam (F) a hanyar zuwa koyar da Hadisi
- Wannan kisan ya haifar da gagarumar zanga-zanga a yankin, inda daruruwan mutane suka fito kan tituna suna neman adalci kan kisan malamin
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Pakistan - Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da cewa an harbe wani fitaccen malamin Musulunci har lahira a wani hari da aka kai masa a lardin Khyber Pakhtunkhwa na ƙasar Pakistan a ranar Talata.
Wasu mahara ne suka yi wa motar Sheikh-ul-Hadith Maulana Muhammad Idrees kwanton-ɓauna a yankin Utmanzai na gundumar Charsadda, inda suka raunata jami'an tsaro biyu da ke tare da shi.

Kara karanta wannan
Matar da APC ta tsaida takara a Katsina ta fara fuskantar cikas daga malaman Musulunci

Source: Twitter
An harbe malamin Musulunci har lahira
Ana kallon Sheikh Idrees a matsayin ɗaya daga cikin manyan malaman addinin Musulunci a Pakistan, wanda ya yi fice kan gudunmawarsa ga ilimin addini, in ji rahoton BBC.
Babu wata ƙungiyar ta'addanci da ta ɗauki alhakin kai wannan harin har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
A cewar ƴan sanda, maharan sun buɗe wa malamin wuta ne yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa bayar da darasin Hadisi a Darul Uloom Utmanzai.
An rahoto cewa ya samu munanan raunuka kuma ya rasu yayin da ake kan hanyar kai shi wani asibitin gundumar.
Daga baya aka kai gawar tasa zuwa ƙauyensa na asali, Turangzai, a gundumar Charsadda, yayin da ɗimbin mabiya suka taru a asibitin bayan jin labarin mutuwarsa.
Zanga zanga ta barke kan kisan malami
Kisan ya haifar da zanga-zanga a yankin, inda daruruwan masu zanga-zangar suka yi tattaki zuwa cikin birnin Charsadda tare da neman a kama waɗanda ke da alhakin kisan cikin gaggawa.
Masu zanga-zangar sun kuma toshe muhimman hanyoyi tare da gudanar da zaman dirshan a dandalin Farooq-e-Azam Chowk.
Babban sufeton ƴan sandan lardin Khyber Pakhtunkhwa, Zulfiqar Hameed, ya nemi rahoto daga jami'in rundunar na shiyyar Mardan, inda ya umarci hukumomi da su tabbatar da an kama masu laifin cikin gaggawa.
A cikin wata sanarwa, Hameed ya bayyana ayyukan Idrees a matsayin "waɗanda ba za a manta da su ba" kuma ya ce za a hukunta waɗanda ke da hannu a wannan "mummunan aiki."

Source: Twitter
Ayyukan malamin a siyasar Pakistan
Maulana Muhammad Idrees ya kasance shugaban jam'iyyar Jamiat Ulema-e-Islam (F) na gundumar Charsadda kuma ana kallon sa a matsayin na hannun daman shugaban jam'iyyar na kasa, Maulana Fazlur Rehman.
Shugaban kasar Pakistan, Asif Ali Zardari ya nuna alhininsa kan kisan Idrees tare da miƙa ta'aziyya ga iyalan da aka yi wa rasuwar, in ji rahoton Hindustan Times.
"Irin waɗannan hare-haren ba za su iya raunata gwiwar al'umma ba," in ji shi, tare da jaddada cewa ƙudurin ƙasar na kawar da ta'addanci ya kasance "mai ƙarfi wanda babu gudu ba ja da baya".
Pakistan ta yi kaca kaca da Isra'ila
A wani labari, mun ruwaito cewa, ministan tsaron Pakistan, Khawaja Asif, ya bayyana Isra’ila a matsayin matsala ga bil’adama a wani saƙo da ya fitar wanda daga baya aka goge.
Khawaja Asif ya yi magana mai zafi game da Isra'ila, inda ya bayyana cewa yana fatan waɗanda suka kafa ta za su kasance cikin wadanda za a kona a lahira.
Pakistan dai ta fito fili tana kira da a kawo ƙarshen hare-haren Isra’ila a Lebanon, yayin da kuma take shirin karɓar baƙuncin tattaunawar diflomasiyya kan yaƙin Iran a Islamabad.
Asali: Legit.ng

