ADC: Gaskiyar Abin da Ya Kori Obi da Kwankwaso zuwa NDC

ADC: Gaskiyar Abin da Ya Kori Obi da Kwankwaso zuwa NDC

  • Jam'iyyar ADC ta yi zargin cewa dama tun can Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da Peter Obi ba su damu da hada kai da sauran 'yan hadakar ba
  • A karshen makon da ya gabata ne manyan 'yan siyasan biyu suka yanke shawarar 'ballewa daga hadakar adawa ta ADC zuwa jam'iyyar NDC
  • Sakataren yada labaran ADC na kasa, Bolaji Abdullahi ya shaida cewa alamu sun tabbatar da dama tun can Obi da Kwankwaso ba su shirya zama ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar ADC, Malam Bolaji Abdullahi, ya bayyana cewa ficewar Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso daga jam’iyyar ba wani abu ne na bazata ba.

Ya ce manyan yan siyasar sun shirya ficewa daga ADC domin su cika burin da suka kudira ba wai lamari ne wanda ya zo 'bakatatan ba.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PRP ta yi magana kan sauya shekar Kwankwaso da Obi zuwa NDC

ADC ta ce Obi da Kwankwaso sun shirya ficewa daga ADC tun farko
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso tare da Peter Obi a wajen wani taro Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Twitter

Jaridar The Cable ta wallafa cewa Bolaji Abdullahi ya ce Obi na neman jam’iyyar da za ta tabbatar masa da tikitin takarar shugaban ƙasa kai tsaye, wanda hakan ne ya sa ya koma NDC.

ADC ta soki sauya shekar Obi, Kwankwaso

Ita kuwa Leadership ta ruwaito Sakataren yada labaran ADC ya ƙara da cewa, tun watanni kafin ficewar tasu, an riga an fara tattaunawa tsakanin su da jagoran NDC, Seriake Dickson.

Ya bayyana cewa hakan ya tabbatar da cewa dama sun tsara barin ADC domin yawon neman takara ba tare da sun fuskanci matsala ba, kuma ba za su jure neman takara a jam'iyyar ba.

Bolaji Abdullahi ya ce ADC za ta mayar da hankali kan manufarta
Sakataren yada labaran ADC, Bolaji Abdullahi Hoto: Bolaji Abdullahi
Source: Twitter

A cewarsa, siyasar haɗaka kamar ta ADC na buƙatar juriya, tattaunawa da kuma haɗa kan mutane daban-daban, ba wai a ba mutum tikiti kai tsaye ba.

Sai dai Bolaji Abdullahi ya ce duk da rashin jin daɗin ficewar tasu, hakan ya ba jam’iyyar damar mai da hankali kan manufofinta ba tare da matsin lamba ba.

Kara karanta wannan

Martanin jam'iyyar ADC bayan ta rasa Kwankwaso da Peter Obi zuwa NDC

An kare sauya shekar Peter Obi

Sanata Victor Umeh daya daga cikin yan ADC da ya fice daga jam'iyyar ya kare matakin Obi, yana mai cewa matsalolin shari’a da rikice-rikicen cikin gida ne suka lalata tsarin haɗakar jam’iyyar tun farko.

Sanata Umeh ya ce ba daidai ba ne a zargi Obi da yawan sauya jam’iyya, domin kusan dukkannin ‘yan siyasar Najeriya sun taɓa yin hakan a wani lokaci.

Ya kuma soki shugabancin ADC, yana cewa sun kasa kafa ingantaccen tsari na fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa, lamarin da ya sa ‘yan takara da dama suka shiga ba tare da tantancewa ba.

NDC za ta mika tikitin takara Kudu

A baya, kun samu labarin cewa jam’iyyar adawa ta NDC ta ware tikitin takarar shugaban ƙasa na zaben 2027 ga yankin Kudancin Najeriya kwanaki kadan bayan ta karbi jiga-jigan ADC.

Jam'iyyar karkashin Sirieke Dickson ta yanke wannan hukunci ne jim kadan bayan Peter Obi da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso sun sauya sheka zuwa cikinta bayan sun rabu da hadakar adawa.

Yanzu haka dai, jam'iyyar NDC ta fara shirye-shiryen yadda za ta gudanar da zaben fitar da gwani yayin da ta bayyana cewa ba za ta fara da batun masalaha ba, sai dai a fafata tsakanin yan takara.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng