Bayan Shekaru 20, Dangote Ya Yi Murabus daga Shugabancin Kamfani, An Naɗa Sabo
- Attajiri a Nahiyar Afirka, Alhaji Aliko Dangote ya ajiye aiki a matsayin shugaban hukumar kamfanin sukari na Dangote bayan shekaru 20
- Kamfanin ya ce Dangote ya jagoranci manyan ayyuka a Adamawa, Taraba da Nasarawa don karfafa samar da sukari a gida da rage shigo da kaya
- Tsohon shugaban bankin Ecobank, Arnold Ekpe ya gaji Dangote a matsayin sabon shugaban, bayan cikakken tsarin tantancewa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Attajirin da ya yafi kowa kudi a Nahiyar Afirka, Alhaji Aliko Dangote ya yi murabus daga shugabancin kamfanin sukari na Dangote.
Attajirin ya ajiye a matsayin Shugaban Hukumar 'Dangote Sugar Refinery', lamarin da ya kawo karshen shugabancinsa na shekaru 20.

Asali: Getty Images
Dangote ya yi ritaya daga shugabanci a kamfaninsa
Sakataren kamfanin, Temitope Hassan shi ya tabbatar da haka a cikin wata da ya sanyawa hannu wanda jaridar Punch ta samu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta ce ritayar tasa za ta fara aiki daga ranar 16 ga Yuni, 2025 domin ba sabon shugaban damar fara aiki.
Dangote ya jagoranci kamfanin tun shekarar 2005, an danganta shi da kawo sauyi da tsarin kamfanin zuwa jagora a kasuwar sukari ta Najeriya.
Sanarwar ta ce:
“Dangane da ka’idojin nagartaccen shugabanci da shirin samar da magaji, 'Dangote Sugar Refinery' na sanar da ritayar Alhaji Aliko Dangote (GCON).

Asali: Getty Images
Yadda Dangote ke kokarin inganta tattalin arziki
Sanarwar ta ce karkashin jagorancinsa an aiwatar da manyan ayyukan bunkasa noma a Adamawa, Taraba da Nasarawa domin kara samar da sukari a gida.
A kwanakin baya, Attajirin ya yi alkawarin zuba hannun jari a jihar Taraba da ke Arewa maso Gabas domin inganta tattalin arziki.
Dangote da Tony Elumelu sun yi alkawarin zuba jari musamman a bangarorin noma da kuma makamashi, Daily Post ta ruwaito.
Attajiran sun bayyana hakan ne yayin taron Taravest da aka gudanar a Jalingo, inda suka yabawa kyakkyawan yanayin kasuwanci na jihar.
Taron ya samu halartar manyan mutane ciki har da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima da Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar III.
Dangote: An nada sabon shugaban kamfanin sukari
Hukumar ta bayyana cewa an nada Arnold Ekpe, Darakta mai zaman kansa, a matsayin sabon Shugaban Hukumar 'Dangote Sugar Refinery' daga 16 ga Yuni, 2025.
“Bayan tantancewa mai kyau da tsari, mun naɗa Mista Arnold Ekpe a matsayin sabon Shugaban Hukumar 'Dangote Sugar Refinery'.
“Muna maraba da Mista Ekpe a matsayin sabon shugaba, tare da godewa Alhaji Dangote bisa nagartaccen aiki da jajircewar da ya nuna."
- Cewar sanarwar
Ekpe gogaggen ma’aikacin banki ne kuma tsohon Shugaban Ecobank, mai kwarewa a harkokin jagoranci da aiki a manyan hukumomi.
Ana zargin an sacewa Dangote kayan N4bn
Kun ji cewa rundunar ‘yan sanda ta gurfanar da wani ɗan kasar India da wasu mutane 12 a gaban kotun tarayya da ke Ikoyi a jihar Lagos.
Ana zargin mutanen da haɗin baki da karkatar da dizal mai darajar sama da N4bn mallakar kamfanin Dangote.
Wadanda ake tuhuma sun musanta laifuffukan da ake zarginsu da su, yayin da kotu ta dage shari’ar zuwa watan Yuli mai zuwa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng