Matasa Sun Fito Zanga Zangar Goyon bayan Tinubu a Benue

Matasa Sun Fito Zanga Zangar Goyon bayan Tinubu a Benue

  • Dubban matasa daga kungiyoyin goyon bayan Bola Tinubu da Gwamna Hyacinth Alia sun gudanar da zanga-zanga a Makurdi, babban birnin Benue
  • Zanga-zangar ta zo ne a ranar 12 ga Yuni, Ranar Dimokuraɗiyyar Najeriya, inda matasan suka taru a manyan tituna kafin taruwa a kofar gidan gwamnati
  • Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da ake gudanar da wata zanga-zangar adawa da gwamnatin Tinubu a birnin tarayya Abuja kan tsadar rayuwa da rashin tsaro

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Benue - Dubban matasa daga sassa daban-daban na jihar Benue sun mamaye titunan Makurdi domin nuna goyon bayansu ga Bola Tinubu da Gwamnan jihar, Hyacinth Alia.

Matasan da suka fito daga kungiyoyin goyon bayan Tinubu da Alia sun gudanar da zanga-zangar lumana tare da rera wakokin yabo da dauke da hotuna da takardun nuna goyon bayan Tinubu.

An yi zanga zangar goyon bayan Tinubu a Benue.
An yi zanga zangar goyon bayan Tinubu a Benue. Hoto Getty Images
Asali: Facebook

Punch ta wallafa cewa zanga-zangar ta samu halartar kungiyoyi masu zaman kansu da kuma wasu shugabannin matasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matasan sun kammala taruwa a dandalin da ke kusa da gidan gwamnatin jihar Benue, inda ake sa ran Gwamna Alia zai yi jawabi.

Matasa sun goyi bayan Bola Tinubu a Benue

Jagororin zanga-zangar sun bayyana cewa manufarsu ita ce nuna godiya da goyon baya ga ayyukan da Shugaba Tinubu da Gwamna Alia ke yi, musamman a fannin tsare-tsare.

Wani daga cikin matasan ya ce sun fito ne domin nuna cewa suna tare da Shugaba Tinubu da Gwamna Alia, kuma suna goyon bayansu su ci gaba da mulkinsu har zuwa 2031.

Ya kara da cewa matasa a jihar Benue suna ganin cigaba, musamman a fannin lafiya, noma, da ci gaban al’umma tun bayan da Gwamna Alia ya hau mulki a shekarar 2023.

An yi zanga zangar adawa da Tinubu a Abuja

Zanga-zangar goyon bayan ta Benue ta zo ne a daidai lokacin da ake gudanar da wata zanga-zangar adawa a Abuja.

A Abuja da wasu birane kamar Legas masu zanga-zanga na sukar gwamnatin Tinubu kan hauhawar farashin kayan masarufi da matsalolin tsaro.

A birnin tarayya, Vanguard ta wallafa cewa matasa da kungiyoyi sun fito da hotuna da alluna masu dauke da rubuce-rubuce na koke da bukatar gyara daga gwamnati.

Ana sa ran gwamna Aliya zai yi magana da masu zanga zanga a Benue
Ana sa ran gwamna Aliya zai yi magana da masu zanga zanga a Benue. Hoto: Benue State Government
Asali: Facebook

‘Yan sanda da jami’an tsaro da dama sun mamaye wuraren da ake kyautata zaton masu zanga-zanga za su taru, ciki har da manyan tituna da ke kusa da majalisar dokoki.

A yau ne ake sa ran shugaba Bola Tinubu zai yi jawabin ranar dimokuradiyya a majalisar tarayya a Abuja.

An sanar da wuraren zanga zanga a jihohi 20

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar Take It Back Movement ta ce za ta jagoranci zanga zanga a akalla jihohi 20.

Kungiyar ta shirya zanga zangar ne saboda yawan matsalolin tsaro da tattali da suka addabi Najeriya a karkashin mulkin Bola Tinubu.

Jagororin matasan sun bayyana cewa za su hadu a wurare a jihohin ciki har da Kano, Adamawa, Bauchi, Legas da birnin tarayya, Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng