Miyagu Sun Farmaki Bayin Allah a Plateau, an Kashe Mutane

Miyagu Sun Farmaki Bayin Allah a Plateau, an Kashe Mutane

  • Wasu miyagun mahara ɗauke da makamai sun kai hari a garin Nkiendowro da ke ƙaramar hukumar Bassa a jihar Plateau
  • Maharan sun hallaka mutane ciki har da ɗan ƙaramin yaro mai watanni tara da haihuwa a yayin harin da suka kai a ranar Laraba
  • Rundunar ƴan sandan jihar Plateau ba ta riga ta fitar da wata sanarwa ba dangane da harin waɗanda miyagun maharan suka kai

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Plateau - Aƙalla mutum huɗu, ciki har da ƙaramin yaro mai watanni tara, sun rasa rayukansu a garin Nkiendowro da ke ƙaramar hukumar Bassa, a jihar Plateau.

Mace biyu da namiji ɗaya sun kasance cikin waɗanda aka kashe, yayin da wasu mutum biyu suka ji raunuka a harin da ya faru a ranar Laraba, 12 ga watan Yunin 2025.

An kai harin ta'addanci a Plateau
Miyagu sun kashe mutane 4 a Plateau Hoto: @CalebMutfwang
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce waɗanda lamarin ya rutsa da su, suna kan hanya ne lokacin da aka farmake su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Miyagu sun farmaki matafiya

Mutanen suna ɗauke ne da tumatir daga wani wuri zuwa Nkiendowro, inda suka shirya jigilar kayan zuwa kasuwar Farin-Gada da ke Jos.

Josiah Zongo, kwamandan tsaro a yankin Miango, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya bayyana cewa an kai gawarwakin mutane huɗun zuwa daƙin ajiye gawa, yayin da mutum biyu da suka samu rauni ke karɓar magani a wani asibiti da ba a bayyana sunansa ba.

Rundunar ƴan sandan jihar Plateau ba ta fitar da wata sanarwa kai tsaye a kan lamarin ba tukunna.

Mahara sun kai hari a Plateau

Hakazalika, an kai wani sabon hari a garin Murish da ke ƙaramar hukumar Mangu a cikin jihar a daren jiya.

Sai dai maharan sun gamu da cikas daga wajen mazauna garin, waɗanda suka fito suka kare kansu.

Wani matashi daga yankin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce maharan sun iso suna harbe-harbe kan mai uwa da wabi, amma an samu nasarar korar su kafin su fara ƙona dukiya ko kashe mutane.

Miyagu sun kashe mutane a Plateau
Miyagu sun kashe mutum 4 a Plateau Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Mutane sun tashi tsaye wajen kare kansu

Ya bayyana cewa suna cikin shiri a kowane lokaci domin kare kansu daga mamayar miyagu masu yunƙurin kawo musu hari.

A cewar Shohotden Mathias Ibrahim, daraktan al’adu na ƙungiyar ci gaban Mwaghavul kuma daraktan sansanin ƴan gudun hijira da ke Mangu, mutane suna cikin fargaba da tsoro.

Ya kuma buƙaci jama’a su ci gaba da gudanar da harkokinsu cikin nutsuwa da lumana, tare da kiran kowa da ya kwantar da hankali.

Mahara sun yi ɓarna a Plateau

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu mahara ɗauke da makamai sun kai wani mummunan harin ta'addanci a jihar Plateau.

Maharan sun ƙona gidaje 96 a ƙazamin harin wanda suka kai a ƙauyen Gyenbwas a yankin Langai da ke ƙaramar hukumar Mangu.

Mutanen yankin sun nuna yatsa ga mutanen ƙabilar Berom kan harin da aka kai musu wanda ya jawo musu asarar dukiya mai tarin yawa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng