'Dan Jihar Jigawa Ya Zama Dan Afrika na Farko da ya Lashe Kyautar Fassara a Saudiyya

'Dan Jihar Jigawa Ya Zama Dan Afrika na Farko da ya Lashe Kyautar Fassara a Saudiyya

  • Malami a Sashen Larabci na Jami’ar Sule Lamido da ke Kafin Hausa, Dr Zaidu Jibril Muhammad, ya lashe kyautar fassara ta duniya a kasar Saudiyya
  • Shi ne dan Afrika na farko da ya lashe wannan gagarumar kyauta bisa fassarar littafin Larabci na Maqāmāt al-Ḥarīrī zuwa Hausa mai taken Dandalin Hikimomi
  • Hukumar da ke kula da kyautar ta yaba da zurfin ilimi da ke tattare da fassarar Dr Zaidu, tana mai bayyana lamarin a matsayin gagarumar gudumawa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Jigawa - Wani malami daga Jami’ar Sule Lamido Kafin Hausa (SLUK), Dr Zaidu Jibril Muhammad, ya kafa tarihi a duniya.

Dr Zaidu ya zama dan Afrika na farko da ya lashe kyautar fassara ta duniya ta Sarki Abdullah Bin Abdulaziz a kasar Saudiyya.

Dan Najeriya ya lashe gasar fassara a duniya
Dan Najeriya ya samu kyautar kan bajinta a fassara a duniya. Hoto: Sule Lamido University, Kafin Hausa
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan yadda aka karrama malamin ne a cikin wani sako da Jami’ar Sule Lamido, Kafin Hausa da ke Jigawa ta wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana ba da kyautar ne ga fitattun masana da suka yi bajinta wajen fassara daga Larabci zuwa wasu harsuna ko daga wasu harsuna zuwa Larabci.

An ba shi wannan yabo ne bisa fassarar littafin Maqāmāt al-Ḥarīrī zuwa harshen Hausa wanda ya sanya wa suna Dandalin Hikimomi.

An karrama dan Najeriya a kasar Saudiyya

Kwamitin gudanarwa na kyautar ya bayyana fassarar Dr Zaidu a matsayin mai cike da zurfin ilimi da tasiri a tsakanin al’ummomi.

An ce wannan aiki na Dr. Zaidu ya taka gagarumar rawa wajen inganta ilimin Afirka da kuma bunkasa fahimta tsakanin harsuna da al’adu.

Littafin da ya fassara ya samo asali ne daga adabin Larabci da aka wallafa tun ƙarni na 11, wanda ke ɗauke da labarai masu ɗauke da hikimomi, dabara, da rayuwar al’umma.

Tarihin rayuwa da karatun Dr Zaidu Jibril

Rahotanni sun nuna cewa Dr Zaidu ya fito ne daga kauyen Shungurum a ƙaramar hukumar Birnin Kudu ta Jihar Jigawa kuma an haife shi a ranar 15 ga Mayu, 1985.

Ya yi karatunsa a makarantu da dama ciki har da firamare ta Kwalli da ke Kano, cibiyar Abdullahi Mai Masallaci, Kwalejin Aminu Kano, Jami'ar Bayero da Jami’o’in Sudan.

Saudiyya ta karrama dan Najeriya
Kasar Saudiyya ta karrama dan Najeriya da ya yi fice a fassara. Hoto: Inside the Haramai
Asali: Twitter

Idan aka tattara nasarorin da ya cimma, za a gano cewa ya mallaki Difloma, Digiri na farko da na biyu, sannan da digirin digirgi a harshen Larabci.

Daga cikin littattafan da ya fassara akwai:

  • Dandalin Hikimomi
  • Dandalin Dabaru (Fassarar Maqāmāt al-Hamadhānī)
  • Bakandamai Bakwai (Fassarar Al-Mu‘allaqāt al-Sab‘a)

Kazalika, ya rubuta muƙalu fiye da 15 da aka wallafa a mujallu na gida da ƙasa da ƙasa.

A yanzu haka Dr Zaidu malami ne sashen Larabci na SLUK kuma mamba ne na Kungiyar Harshen Larabci ta Duniya.

Masarauta ta karrama Sheikh Isa Pantami

A wani rahoton, kun ji cewa masarautar Pantami ta karrama Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami kan gudumawar da yake bayarwa.

Legit ta gano cewa Hakimin Pantami ne ya fitar da sanarwar a wata takarda tare da lissafa bangarorin da ya bayar da gudumawa.

Karramawar na zuwa ne yayin da ake cigaba da rade radin cewa Sheikh Pantami na shirin fitowa takarar gwamnan Gombe a 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng