Minista a Gwamnatin Trump Ya Fadi Kasar da Ke da Ikon Bude Mashigar Hormuz

Minista a Gwamnatin Trump Ya Fadi Kasar da Ke da Ikon Bude Mashigar Hormuz

  • Ministan harkokin wajen Amurka, Marco Rubio ya bayyana tasirin da Amurka ke da shi musamman game da bude mashigar Hormuz
  • Rubio ya ce kasar ce kadai ke da ikon sake buɗe mashigin Hormuz idan rikici ya hana zirga-zirgar jiragen ruwa cikin yankin
  • Ministan ya bayyana cewa aikin “Project Freedom” zai bai wa Amurka damar kare hanyoyin kasuwancin mai tare da tabbatar da tsaron ruwa a Gabas ta Tsakiya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Ministan harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, ya yi karin haske kan ci gaba da yaki tsakanin Iran da Isra'ila a yankin Gabas ta Tsakiya.

Rubio ya bayyana cewa Amurka ce kaɗai ƙasar da ke da ikon sake buɗe mashigar Hormuz idan rikici ya dakatar da zirga-zirgar jiragen ruwa a yankin.

Kara karanta wannan

Tsugune ba ta ƙare ba, Amurka ta sake bijiro da maganar sulhu da ƙasar Iran

Amurka ta bayyana cewa ita kadai ke da ikon bude mashigar Hormuz
Jagoran addini a Iran, Mojtaba Khamenei da Shugaba Donald Trump na Amurka. Hoto: Imam Mojtaba Khamenei, Donald J Trump.
Source: Facebook

Rubio ya yi wannan bayani ne yayin da ake ƙara nuna damuwa kan yiwuwar rikicin Gabas ta Tsakiya ya shafi safarar mai da sauran harkokin kasuwanci ta ruwa, cewar Al Jazeera.

Shirin da Amurka ke yi kan mashigar ruwa

Rubio ya ce aikin da ake kira “Project Freedom” zai taimaka wajen kare hanyoyin sufuri na ruwa tare da tabbatar da tsaron jiragen kasuwanci masu zirga-zirga a yankin.

Mashigar Hormuz na daga cikin manyan hanyoyin jigilar danyen mai a duniya, inda ƙasashe da dama ke dogaro da shi wajen fitar da makamashi zuwa kasuwannin duniya, cewar rahoton Bloomberg.

Rubio ya jaddada cewa Amurka na da ƙwarewa da ƙarfin soji da zai ba ta damar jagorantar duk wani yunƙuri na tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankin.

Amurka ta fadi tasirin da ta ke da shi game da mashigar Hormuz
Amurka na ci gaba da ba Najeriya tallafi Hoto: @SecRubio.
Source: Twitter

Kalaman nasa sun zo ne a lokacin da ake ci gaba da samun tashin hankali tsakanin Iran da wasu ƙasashen duniya, lamarin da ke ƙara tayar da hankalin kasuwannin mai da tattalin arzikin duniya.

Kara karanta wannan

Amurka ta kai hari kan jiragen Iran, dakarun Trump sun kashe mutane

Amurka ta sha alwashi kan mashigar Hormuz

Yayin da Rubio ke magana kan mashigar ruwan, ya ce Amurka ba za ta taba bari a ci gaba da hana jiragen kasuwanci wucewa ta mashigar ba.

Ya ce:

“Suna ƙoƙarin mayar da wannan sabon abu na yau da kullum.
“Ba za mu taɓa bari su mayar da tayar da jiragen kasuwanci da sanya nakiyoyi a ruwa a matsayin abin da aka saba ba.
“Abin da muka fi so shi ne a sake buɗe waɗannan mashigai yadda ya kamata, kamar yadda suke a baya.”

Alwashin da Amurka ta sha kan Iran

A wnai labarin, mun ba ku labarin cewa ana ci gaba da gwabza fada a tsakanin kasashen Amurka, Isra'ila da Iran a yankin Gabas ta Tsakiya.

Ministan harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, ya fito ya yi magana kan yakin wanda aka shafe fiye da wata daya ana fafatawa da ya jawo asarar rayuka da dukiyoyi.

Marco Rubio ya bayyana cewa akwai abin da Amurka ba za ta bari Iran ta mallaka ba yayin da ya nuna cewa ana ci gaba da tattaunawa game da yakin da ake yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.