Yadda Aka Kama Ma'aikaci a Fadar Aso Rock kan Zargin Yunkurin Juyin Mulki

Yadda Aka Kama Ma'aikaci a Fadar Aso Rock kan Zargin Yunkurin Juyin Mulki

  • Wani ma’aikacin fadar shugaban kasa a Najeriya ya yi karin haske game da yunkurin juyin mulki a kasar
  • Mutumin mai suna Zekari Umoru ya shaida wa kotu cewa abokan tuhumarsa sun ruɗe shi cikin zargin shirya juyin mulki
  • Umoru ya ce Ahmed Ibrahim ne ya haɗa shi da wani da ake kira Kanal Mohammed Ma’aji, wanda ya riƙa ba su kuɗaɗe masu yawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Wani ma’aikacin kamfanin Julius Berger da ke aiki a sashen kula da gyare-gyare na fadar shugaban ƙasa ya yi magana kan zargin juyin mulki.

Mutumin mai suna Zekari Umoru, ya ce an ruɗe shi cikin shirin juyin mulki inda ya ce ta yi nadama matuka.

Wani da ke aiki a Aso Rock ya fadi yadda aka yaudare shi kan juyin mulki
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Channels TV ta ce an nuna bidiyon bayaninsa a gaban Mai shari’a Joyce Abdulmalik da ke zamanta a babbar kotun tarayya da ke Abuja.

Kara karanta wannan

An yi wa Nafiu Bala barazanar raba shi da rayuwarsa kan ADC? Gaskiya ta fito

Juyin mulki: Ana tuhumar ma'aikaci a Aso Rock

Umoru, wanda shi ne mutum na huɗu cikin waɗanda ake tuhuma, ya bayyana cewa ya haɗu da wasu daga cikin waɗanda ake zargi ne ta hannun Ahmed Ibrahim.

Ya ce Ibrahim ya gabatar masa da wani Hassan Mohammed wanda daga baya ya gano shi ne Kanal Mohammed Ma’aji.

Ya ce an gaya masa cewa aikin lantarki za a ba shi a wani gini da ake ginawa, kuma ya ɗauki Ma’aji a matsayin ɗan kasuwa.

Umoru ya bayyana cewa ya karɓi kuɗaɗe daban-daban daga hannun Ma’aji tare da wasu lokuta da Ibrahim ke tare da shi.

Ana zargin malami da hannu a juyin mulki
Shugaba Bola Tinubu yana jawabi a Abuja. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Juyin mulki: Makudan kudi da aka ba Umoru

A cewarsa, sun haɗu da Ma’aji a wani wuri inda ya saya musu abin sha tare da ba su kuɗi tsakanin N100,000 zuwa N120,000.

Umoru ya ce a ranar 24 ga Satumban 2025, Ma’aji ya ba shi jakar 'Ghana-Must-Go' cike da kuɗi, ya bayyana cewa ya kai kuɗin bankin Zenith inda aka ƙirga su suka kai N8.8m.

Kara karanta wannan

Sharadin Trump ga Iran yayin da ya ke shirin afkawa kasar da yaki karo na 2

Ya ƙara da cewa washegari shi da Ibrahim sun sake haɗuwa da Ma’aji wanda ya ba su ƙarin N2m, cewar TheCable.

A cewarsa, daga baya ya fara jin tsoron yawan kuɗin da ake ba su, sannan ya nemi Ibrahim ya bayyana masa gaskiya.

Umoru ya ce Ibrahim ya gaya masa cewa Ma’aji bai gamsu da yadda ƙasa ke tafiya ba, kuma yana son a “gyara gwamnati.”

Malamin Musulunci ya musanta hannu a juyin mulki

A nasa ɓangaren, Sheikh Imam Kassim Goni ya musanta hannu a shirin juyin mulki inda ya ce duk kuɗin da Kanal Ma’aji yake turo masa na addu’a ne da ayyukan alheri kawai.

Sai dai masu bincike sun nuna wasu bayanai da suka ce sun saba da bayaninsa, ciki har da canja wurin miliyoyin naira tun shekarar 2023.

Sun ce akwai wasu maganganu da suka shafi samun hanya da kayan aiki da suka ƙara jawo zargi.

Ana ci gaba da shari'ar zargin juyin mulki

A wani labarin, an ji cewa majiyoyi sun ce an gabatar da bidiyon tambayoyin da jami'an tsaro suka yi wa wadanda ake tuhuma da hannu a kitsa juyin mulki, a zaman kotu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu za ta kashe Naira tiriliyan 1.1 a Kaduna, Uba Sani ya yi bayani

Mutanen suna daga wadanda ake zargi sun tabbatar da cewa sun samu labarin shirin kifar da gwamnatin Tinubu amma ba su ba da goyon baya ba.

Lauyoyin wadanda ake tuhuma sun kalubalanci bidiyon da bangaren gwamnati suka gabatar, inda suka ce da yiwuwar ba da som rai suka amsa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.