Ana Murnar Ranar Dimokuradiyya, Peter Obi Ya Sake Dura kan Gwamnatin Tinubu

Ana Murnar Ranar Dimokuradiyya, Peter Obi Ya Sake Dura kan Gwamnatin Tinubu

  • Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda al'amura suke tafiya a Najeriya
  • Peter Obi ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da maida hankali kan siyasa maimakon yi wa ƴan Najeriya aiki
  • Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasan ya kuma koka da cewa tsarin dimokuraɗiyya ya daina aiki yanzu a Najeriya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya yi wa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, raga-raga.

Peter Obi ya zargi gwamnatin Shugaba Tinubu da yin munafurci tare da maida hankali kan siyasa fiye da yin aiki don inganta rayuwar ƴan Najeriya.

Peter Obi ya caccaki Bola Tinubu
Peter Obi ya soki gwamnatin Bola Tinubu Hoto: @DOlusegun, @PeterObi
Asali: Facebook

Tashar Channels tv ta ce ya yi wannan furucin ne a wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja a ranar Alhamis, 12 ga watan Yunin 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Peter Obi ya ragargaji Tinubu

A cewarsa, abubuwan siyasa da ke faruwa a ƙasar cikin shekaru biyu da suka gabata suna nuna shirin da ke gudana gabanin babban zaɓe mai zuwa.

Peter Obi, wanda ya fara da girmama marigayi MKO Abiola, ya ce ƴan siyasa irin su Abiola sun sadaukar da rayukansu don tabbatar da dimokuraɗiyya, amma halin da ƙasar nan ke ciki a yau abin damuwa ne.

"Abin takaici ne sosai cewa a ƙarƙashin wannan gwamnati, ba za a iya cewa Najeriya na tafiya a tsarin dimokuraɗiyya ba, duk da cewa shugaban ƙasa na yanzu yana cikin waɗanda suka fafata don dawo da dimokuraɗiyya."
"Halin da ƙasar ke ciki abin takaici ne, tattalin arziƙi da tsaro sun taɓarɓare, kuma alamu da matakan da ake amfani da su don auna ci gaban ƙasa kamar kiwon lafiya, ilimi, da masana’antu sun rushe."
"A shekarar 2023, kimanin kashi 38.9% na ƴan Najeriya ne ke rayuwa ƙasa da layin talauci, amma yanzu ya ƙaru zuwa kashi 54%. Ƙasa da kashi 10% na cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko ne kawai ke aiki yadda ya kamata a faɗin ƙasa."

"Na ziyarci jihohi da dama cikin watanni shida da suka wuce, kuma na ba da tallafi a wasu daƙunan karɓar haihuwa, inda haihuwa ke zama wani yanayi na a mutu ko a yi rai tsakanin uwa da jariri."

- Peter Obi

Peter Obi ya koka kan tsadar rayuwa

Peter Obi ya jaddada cewa yunwa da matsalar rashin abinci sun kai matakin da ba a taɓa gani ba, inda mutane da dama ba za su iya sayen abinci ba, hakan ya jefa su sun maida yin roƙo a matsayin sana’a.

Peter Obi ya taso gwamnatin Tinubu a gaba
Peter Obi ya ragargaji gwamnatin Shugaba Tinubu Hoto: @DOlusegun, @PeterObi
Asali: Facebook
"Saboda wannan matsin da ake ciki, hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta fitar da rahoto da ke cewa sama da mutane miliyan 20 a Najeriya na fama da matsalolin lafiyar kwakwalwa."

- Peter Obi

Peter Obi ya ƙara da cewa, maimakon gwamnati ta nemo hanyoyin da za su rage wa mutane wahala, sai ta ci gaba da karɓar bashin kuɗi, wanda yanzu ya sa bashin da ke kan Najeriya ya kai Naira tiriliyan 188.

Peter Obi ya faɗi shirinsa kan 2027

A wani labarin kuma, kun ji cewa Peter Obi wanda ya yi takarar shugaban ƙasa a 2023, ya yi magana kan shirin da yake dangane da zaɓen 2027.

Peter Obi ya bayyana cewa magoya bayansa za su tsaya su tabbatar da cewa an ƙirga musu ƙuri'un da suka kaɗa a lokacin zaɓen.

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasan ya bayyana cewa za su nemo mutane masi nagarta waɗanda za su gudanar da wannan aikin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng