Ambaliyar Ruwa Ta Yi Mummunar Barna a Jihohin Najeriya 31, An Rasa Gonaki 180,000
- Rahoton SBM Intelligence ya nuna cewa sauyin yanayi da rashin tsaro sun addabi manoma Najeriya, musamman a jihohi 31 na kasar
- A cikin rahoton, SBM ya bayyana cewa ambaliyar ruwa ta lalata hekta 180,000 na gonaki a jihohi 31 kuma hakan ya shafi mutane miliyan 1.2
- Rahoto ya kuma bayyana cewa mutane miliyan 2.2 sun rasa muhallansu, yayin da aka samu hauhawar farashin abinci saboda ambaliya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - SBM Intelligence ta fitar da wani sabon rahoto da ke nuna cewa fannin noma a Najeriya ya gamu da koma baya sakamakon sauyin yanayi da ƙaruwar rashin tsaro.
Ambaliyar ruwa ta shafi jihohi sama da 30, inda ta haifar da lalacewar gonaki da aka noma na kimanin hekta 180,000 a faɗin ƙasar, a cewar rahoton.

Asali: Getty Images
Ambaliyar ruwa ta shafi jihohi 31 a Najeriya
Rahoton, wanda aka buga a watan Yunin 2025, ya bayyana cewa jihohi 31 daga cikin 36 na Najeriya ne suka gamu da ambaliya daga Yulin 2024, kamar yadda Punch ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakazalika, rahoton ya nuna cewa mummunar ambaliyar ruwa da ta afkuwa a jihohin ta shafi akalla mutane miliyan 1.2, wadanda suka rasa muhalli, gonaki da kadarori.
SBM Intelligence ya rahoto cewa:
"Tun daga watan Yulin 2024, jihohi 31 daga cikin jihohi 36 na Najeriya sun fuskanci ambaliyar ruwa, wanda ya shafi kusan mutane miliyan 1.2.
"Wannan yawaitar ambaliyar ruwa da ake samu ta lalata gonaki da aka noma na kimanin hekta 180,000 a faɗin ƙasar".
Dalilin hauhawar farashin abinci a 2024
Ambaliyar ta haifar da barna mai yawa ga kayayyakin aikin gona, wanda ya ƙara tsananta matsalar rashin abinci a faɗin ƙasar, kamar yadda rahoton ya nuna.
Yankin Middle Belt, wanda aka sani da yawan samar da amfanin gona, ya gamu da lalacewar amfanin gona a cikin shekara daya, sakamakon ambaliya.
A sakamakon karancin abinci da aka samu saboda ambaliyar, jihohi sun fuskanci hauhawar farashin abinci, wanda ya kai kashi 35.41 cikin ɗari a watan Janairun 2024.
Mutane miliyan 2.2 sun rasa muhalli a Arewa
Baya ga ambaliyar ruwa, zaizayar ƙasa a yankunan Arewa ta ƙara jawo karancin amfanin gona. Rahoton ya nuna cewa hekta 350,000 na gonaki ake rasawa a kowace shekara saboda zaizayar ƙasa.
Waɗannan abubuwan, tare da rashin tsaro daga rikicin manoma da makiyaya da kuma ayyukan ɓarayin daji, sun kawo cikas ga ayyukan noma kuma sun tilasta wa manoma da yawa barin gonakinsu.
Fiye da mutane miliyan 2.2 ne aka ce suka rasa matsugunansu sakamakon rashin tsaro, musamman a yankunan Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Yamma.

Asali: Facebook
Mutum miliyan 100 ba su da wadataccen abinci
Wannan ya dakatar da samar da kayan gona mai yawa a waɗannan yankunan, wanda ya ƙara jawon rashin wadataccen abinci a faɗin ƙasar.
Rahoton ya nuna cewa 'yan Najeriya miliyan 100 ba su samu wadataccen abinci ba a watanni uku na farkon 2024, inda miliyan 18.6 ke fuskantar matsanancin yunwa.
An fitar da rahoton ne bayan ambaliyar ruwa da ta afku a Neja a watan Mayun 2025, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 200 tare da raba mutane sama da 3,000 da muhallansu.
Jihohi 8 da za a iya samun ambaliya a Yuni
A wani labarin, mun ruwaito cewa, NiMet ta yi gargaɗin yiwuwar ambaliyar ruwa a wasu jihohi a watan Yuni 2025, yayin da ƙasar ke shiga tsakiyar damina.
Wuraren da aka fi fargabar ambaliya sun haɗa da Kano, Kaduna, Neja, Nasarawa, Kwara, Sokoto, Filato da Abuja, inda ruwan sama zai sauka da ƙarfi.
NiMet ta buƙaci manoma su yi shiri sosai, kuma ta yi kira da a dakile ambaliya ta hanyar share magudanan ruwa da bin sabbin hanyoyin noma masu dacewa da yanayi.
Asali: Legit.ng