Ranar Dimokuradiyya: Farfesa Jega Ya Bukaci Tura Sakamakon Zabe Ta Na'ura

Ranar Dimokuradiyya: Farfesa Jega Ya Bukaci Tura Sakamakon Zabe Ta Na'ura

  • Tsohon shugaban hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC), Attahiru Jega, ya bukaci a gyara dokar zaɓe ta Najeriya domin wajabta tura sakamakon zaɓe ta na’ura
  • Farfesa Jega ya kuma bukaci a rage yawan ‘yan majalisa tare da mayar da su ma’aikata na wucin gadi domin rage kashe kuɗin gwamnati
  • Ya bayyana haka ne yayin taron 12 ga Yuni da aka shirya a Legas, inda ya bukaci amfani da fasaha wajen inganta zaɓe a ƙasar nan

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Legas - Farfesa Attahiru Jega da ya jagoranci hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) daga 2010 zuwa 2015, ya bukaci kawo sauyi a harkar zabe.

Jega ya bukaci gwamnati da ‘yan majalisa su tabbatar da gyaran dokar da za ta wajabta tura sakamakon zaɓe ta na’ura a Najeriya.

Jega ya bukaci sauya tsarin zabe
Jega ya bukaci tura sakamakon zabe ta na'ura. Hoto: Imran Muhammad
Asali: Facebook

Rahoton Channels TV ya nuna cewa Jega ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin da ya halarci taron tunawa da Ranar Dimokuraɗiyya a jihar Legas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, wajabta amfani da fasahar zamani wajen tura sakamako zai haifar da ƙarin gaskiya da amincewa tsakanin ‘yan Najeriya da hukumomin gudanar da zaɓe.

Jega ya nemi aiki da fasaha a harkar zabe

Jega ya bayyana cewa akwai buƙatar ƙara amfani da fasaha domin gudanar da zaɓuɓɓuka cikin gaskiya da adalci.

Ya ce:

“Dole ne a inganta dokar zaɓe ta 2022 domin a sanya wajabcin amfani da fasaha wajen tura sakamakon zaɓe.”

Ya kara da cewa rashin amincewar ‘yan Najeriya da sababbin na’urorin da INEC ke amfani da su na da nasaba da rashin tsari mai gaskiya wajen gwada su kafin a fara amfani da su.

A cewarsa:

“Yana da matuƙar muhimmanci a samar da tsarin gwaji cikin gaskiya da haɗa kai da jama’a kafin a fara amfani da kayan aikin zaɓe,”

Ya kuma bukaci a kawar da duk wani ruɗani da ke cikin dokar zaɓe da ya shafi amfani da na’ura wajen aika sakamakon zaɓe daga rumfunan zaɓe zuwa cibiyar tattara sakamako.

Jega ya bukaci sauyi a aikin majalisa

Baya ga batun fasahar zaɓe, Jega ya shawarci gwamnati da ta yi la’akari da mayar da ‘yan majalisa a matakin tarayya da jihohi zuwa na wucin gadi domin rage kashe kudi.

A cewarsa:

“Ƙasar nan na bukatar rage yawan ‘yan majalisa da kuma mayar da su na wucin gadi domin rage yawan kuɗin da ake kashewa wajen gudanar da ayyukansu.”

Ya bayyana cewa tsarin da ake ciki yanzu ba mai dorewa ba ne, duba da yadda kuɗin da ake kashewa a majalisu ke ƙaruwa, ba tare da sauyi mai amfani ga jama’a ba.

Farfesa Jega ya bukaci sauya aikin majalisa
Farfesa Jega ya bukaci mayar da 'yan majalisa wucin gadi. Hoto: INEC Nigeria
Asali: Twitter

INEC ta koka kan rashin kudi

A wani rahoton kun ji cewa hukumar INEC ta koka kan rashin kudi game da dalilin gaza gudanar da zabukan cike gurbi.

Hakan na zuwa ne bayan samun gurabai bakwai a jihohi daban daban a majalisun tarayya da ya kamata a yi zabe domin cike su.

An samu guraben ne sakamakon mutuwar wasu 'yan majalisar wakilai da kuma samun mukamai da wasu suka yi a matakin jiha.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng