An Samu Sauƙi da Sojoji Suka Hallaka Rikakken Ɗan Bindiga, Ɗan Ado Aliero Ya Tsere

An Samu Sauƙi da Sojoji Suka Hallaka Rikakken Ɗan Bindiga, Ɗan Ado Aliero Ya Tsere

  • Rundunar Sojojin OPFY sun hallaka shahararren shugaban 'yan ta'adda da abokansa a wani harin kwanton bauna da suka kai a Zamfara
  • Bincike ya nuna an kashe Abdul Jamilu da Salisu tare da Auta a harin da aka kai na kwanton bauna wanda ya yi ajalin yan bindiga da dama
  • Ɗan Ado Alieru, Sarki, ya tsere yayin da ake artabu, ana cece-kuce cewa 'yan ta'adda sun shiga damuwa kan yadda ake hallaka nasu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gusau, Zamfara - Rahotanni sun tabbatar da cewa dakarun sojojin 'Operation Forest Yakin' (OPFY) sun hallaka hatsabibin ɗan bindiga da wasu abokansa.

Rundunar ta samu gagarumar nasara kan yan bindiga a jihar Zamfara da ke Arewacin Najeriya, inda suka kashe fitaccen dan ta’adda, Auta da wasu abokansa.

Sojoji sun hallaka manyan yan bindiga
Sojoji sun suka hallaka rikakken ɗan bindiga da abokansa. Hoto: HQ Nigerian Army.
Asali: Twitter

Zamfara: Sojoji sun kawo karshen wasu yan bindiga

Bayanan sirri sun shaida wa Zagazola Makama cewa harin da aka kai a Ƙunchin Kalgo a karamar hukumar Tsafe da ke jihar Zamfara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tabbatar da cewa yayin harin, dakarun sojoji sun yi nasarar kashe hatsabiban yan bindiga, Abdul Jamilu, Salisu da Auta.

Sojojin sun fafata da 'yan ta'addan har suka yi nasara, amma har yanzu ba a san inda Babaye da wani abokinsa suke ba.

Rahotanni daga yankin sun ce watakila Babaye da abokin nasa ma sun mutu yayin artabun da ya gudana tsakanin sojoji da 'yan ta’adda.

Sojoji sun farmaki yan bindiga a Zamfara
Sojoji sun hallaka wasu yan bindiga a Zamfara. Hoto: HQ Nigerian Army, @ZagazOlamakama.
Asali: Twitter

Dan Ado Aliero ya tsere bayan artabu da sojoji

Hakan ya biyo bayan rahotanni cewa hatsabibin dan bindiga, Ado Aliero wanda aka fi sani da Sarki ya tsere ta gonaki yayin da ake harbe-harbe.

Shaidu sun ce hakan ya faru ne yayinda manoma ke aiki a gonakinsu, wanda ya ba shi damar tserewa daga hannun jami’an tsaro.

Bincike ya nuna cewa 'yan ta’adda a Ƙunchin Kalgo sun tara magoya bayansu don nemo Babaye da sauran da suka bace bayan harin.

Yadda sojoji ke dagawa yan bindiga hankali

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa akwai fargaba tsakanin 'yan ta’adda, ganin yadda dakarun gwamnati ke ci gaba da hallaka su a hare-haren baya-bayan nan.

Harin na baya ya faru ne a ranar 9 ga Yunin 2025 da muke ciki a wani shagon mai a Danjibga, inda aka kashe 'yan ta’adda kusan 10 yayin harin da aka kai.

Rahoto ya ce an binne ɗaya daga cikin su a makabartar Danjibga, ƙarƙashin jagorancin Alhaji Hamza MKO wanda Dogo Sule ya turo.

Bello Turji ya ƙaƙaba haraji ga manoma

A baya, kun ji cewa rikakken dan bindiga, Bello Turji na bukatar N50m daga mazauna Tsallaken Gulbi da ke karamar hukumar Shinkafi a jihar Zamfara.

Wadanda abin ya shafa sun hada da mutanen kauyen Fakai har zuwa Qaya da ke kusa da iyakar Najeriya da Jamhuriyar Nijar.

An tabbatar da cewa dan bindiga, Bello Turji ya bukaci kudin ne domin ya bar su su ci gaba da noma a wannan kakar ba tare da sun samu matsala ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.