Hajjin Bana: Jihohi 11 Sun Kashewa Alhazai N6.2bn a Saudiyya
- Alhazan Najeriya daga jihohi 11 sun samu tallafi daga wajen gwamnatocinsu yayin da suke gudanar da aikin Hajji a Saudiyya
- Ana lissafin cewa jihohin guda 11 sun ba da tallafin N6.2bn domin sauƙaƙawa Alhazan yayin da suke zaune a ƙasa mai tsarki
- Alhazan da suka fito daga jihar Sokoto sun samu kyautar kuɗin da suka kai N450,000 daga wajen Gwamna Ahmed Aliyu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Saudiyya - Wasu daga cikin jihohin Najeriya sun ba da tallafi ga Alhazansu da ke ƙasa mai tsarki yayin aikin Hajjin bana.
Rahotanni sun nuna cewa jihohi 11 sun ba Alhazansu tallafin N6.2bn yayin da suka gudanar da aikin Hajji a ƙasar Saudiyya.

Asali: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce kowanne daga cikin Alhazai 3,345 daga jihar Kano ya karɓi Riyal 50 na Saudiyya a matsayin tallafi domin taimaka musu yayin bukukuwan Sallah da sauƙaƙe musu zama a ƙasa mai tsarki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan bayanin ya fito ne a ranar Litinin daga wakilin Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin jihar Kano na Alhazai, Sarkin Karaye, Alhaji Muhammad Maharaz Karaye.
Sakataren kwamitin kuma daraktan hukumar jin daɗin Alhazai ta jihar Kano, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa, ya ce an gudanar da rabon tallafin ne cikin tsari.
Alhazai sun samu tallafi a Saudiyya
A ɓangare guda kuma, gwamnatin jihar Kebbi ba ta bayar da tallafi ba wajen biyan kuɗin Hajji ga maniyyata 3,800 daga jihar ba.
Sai dai a ƙasar Saudiyya, Gwamna Nasir Idris ya amince da bayar da Riyal 200 ga kowanne Alhaji daga jihar.
Gwamnatin jihar Legas ma ba ta ba da tallafin kuɗin Hajji a bana ba, inda kowanne daga cikin maniyyata 1,315 ya biya kusan N9m.
Amma Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya bai wa kowanne maniyyaci Riyal 180 (kimanin N74,870) wanda gaba ɗaya ya kai jimillar N98,454,050.
Gwamnatin jihar Jigawa, wadda ita ma ba ta ba da tallafin kuɗin Hajji a bana ba, rahotanni sun ce ta bai wa kowanne daga cikin maniyyata 930 Riyal 100 (kimanin N43,000) a matsayin 'Kyautar Arafat'.
A jihar Sokoto, kowanne daga cikin Alhazai 3,200 ya samu Riyal 1,000 (kimanin N450,000) a matsayin kyautar sallah daga Gwamna Ahmed Aliyu.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin da ya kai ziyara ga tawagar Alhazan jihar a Mina, Saudiyya, inda ya taya su murna bisa kammala aikin Hajji cikin nasara, rahoton Channels tv ya tabbatar.

Asali: Facebook
Jihar Borno ta biya kuɗin hadaya
A jihar Borno, mataimakin gwamnan jihar, Umar Usman Kadafur, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ce ta biya kuɗin hadaya ga dukkan Alhazan jihar.
An bayyana cewa jimillar maniyyata 2,174 daga jihar ne suka gudanar da aikin Hajji a bana.
Da aka tuntuɓi Malam Dauda Iliya, mai ba Gwamna Babagana Zulum shawara ta musamman kan harkokin yaɗa labarai, ya ce banda hadaya, bai san da wani rangwamen kuɗi ko tallafi da gwamnatin jihar ta bayar ba ga maniyyata.
Sahabi Abdulrahman ya shaidawa Legit Hausa cewa baya goyon bayan kyautar kuɗaɗen da aka ba Alhazai a Saudiyya.
"Wannan ai ƙarawa mai ƙarfi, ƙarfi ne kawai. Kuɗaɗen nan za su yi amfani sosai idan da wasu ayyukan aka zo aka yi wa al'umma."
"Akwai mabuƙata sosai waɗanda suka fi Alhazan buƙatar tallafi, su ya kamata a ce an taimaka."
- Sahabi Abdulrahmaɓ
Ranar da Alhazan Najeriya za su dawo gida
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta sanya ranar da Alhazan Najeriya za su dawo gida.
Hukumar NAHCON ta bayyana cewa za a fara jigilar dawo da Alhazai zuwa gida Najeriya daga ranar, 13 ga watan Yunin 2025.
Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Usman ya kuma taya Alhazai murnar kammala aikin Hajjin bana cikin nasara.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng