Latest
Duk da kashe kashe shugaban ‘yan ta’aadan jihar Zamafara da ake yi kashe kashe bai tsaya ba a jihar, an yi jana'izar gawarwakin da 'yan bindiga suka afkawa a ranar Lahadi a garin Bingi a karamar Hukumar Maru dake jihar Zamfara.
Mun kawo maku jerin mata masu kudin Duniya irin su Alice Walton. Liliane Bettencourt tana cikin manyan masu kudin Duniya kafin ta rasu. Bayan nan kuma akwai irin su Jacqueline Mars, Zhou Qunfei, da Sherry Brydson.
Hukumomin abinci dana bunkasa aikin gona tare da hadin guiwar hukumar bada agajin gaggawa na majalisar dinkin duniya sun yi hasashen cewa akwai barazanar yunwa akan jihohi sama da 16 a yankin arewacin Najeriya...
A cikin daren ranar Litinin ne gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir Ahmed El-Rufai, ya fita duba fitilun kan titi da ake sakawa a cikin garin jihar Kaudna da kan sa Mallam Nasiru El-Rufai, ya tsaya unguwar Ali Akilu Road dan duba su
Kungiyar kare hakkin dan Adam na Amnesty International, ta ce sojojin Najeriya sun yi kunnen uwar shegu akan gargadin da aka musu na cewa Boko haram za su kowa wa yankin Dapchi hari sao'i kalilan gabannin a sace 'yan matan Dapchi.
Wani matashin mai suna Faysal Abdullahi Omar, wanda har yanzu yana makaranatar Sakandare ya fadawa BBC cewa, yaki karban aikin ne saboda yana tsoron kada mayakan kungiyar al-Shabab su kashe shi dan suna aiki a yankin.
A cewar jaridar Bild na kasar Jamus, a yayin wata ganawar sirri da yayi da 'yan majalisar dokokin kasarsa, shugaban BND Ole Diehl, ya ce yana da tabbacin cewa makaman Koriya ta Arewa na iya cimma kasashen Turai a cikin kiftar ido.
Marafa yace dukkaninsu dauke da bindiga kirar AK 47, sun dira kauykan ne da misalin karfe 4:30 na ranar Lahadi, inda suka kwashi tsawon lokaci suna tafka ta’asa iri iri, tare da aikata ma jama’an kauyukan aika aika daban daban.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gargadi direbobin manyan motoci dasu guji ajiye motoci a kan manyan titi, sannan kuma su gina wuraren ajiye motocin domin kawo saukin zirga-zirga akan manyan titi, da kuma rage cinkoson motoci...
Masu zafi
Samu kari