Tsoron kungiyar Al-Shabab ya sa wani matashi yaki karban aikin gwamnati a Somalia

Tsoron kungiyar Al-Shabab ya sa wani matashi yaki karban aikin gwamnati a Somalia

- Matashi mai shekaru 16 yaki karban aikin gwamnati a kasar Somalia saboda tsoron Al-Shabab

- Faysal Abdullahi Omar ya ce yana tsoron kada Alshabab su kashe shi idan ya karbi aikin gwamnati

Wani matashi mai shekaru 16 yaki karban mukamin mataimakin kwamishinan jihar Hirshabelle dake kudancin kasar Somalia saboda rashin tsaro da aka fama dashi a kasar.

Matashin mai suna Faysal Abdullahi Omar, wanda har yanzu yana makarantar Sakandare ya fadawa BBC cewa, yaki karban aikin ne saboda yana tsoron kada mayakan kungiyar al-Shabab su kashe shi dan suna da yawa a yankin.

Tsoron kungiyar Al-Shabab ya sa wani matashi yaki karban aikin gwamnati a Somalia
Tsoron kungiyar Al-Shabab ya sa wani matashi yaki karban aikin gwamnati a Somalia

Omar yace, shugabanin kabilar sa suka yanke hukunci a bashi mukamin ba tare da tuntuban sa ba.

KU KARANTA : Rikicin Benuwe : Rundunar ‘yasandan Najeriya ta mayar da martani akan tuhumar da Buhari yayiwa IGP Idris saboda rashin bin umarnin sa

Omar ya kara da cewa abun da ke gaban sa a yanzu shine kammala karatun sa na makarantar sakandare dan ya shiga jami’a.

A makonni biyu da suka gabat ne Legit.ng ta rawaito labarin yadda ‘yan ta’adan Al- Shabab suka kashe wani babban soja da Minista a brinin Magadishu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng